23

190 14 1
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

      

*SHAFI NA 23*

Nayi kuka kamar rai na yafita, ba wanda bai ba mahaifina haƙuri ba amma yaƙi, dan haka nima na yanki shawara gwara nabi duniya tunda har Mahaifina ya iya cewa ya barwa duniya ni, haka kuwa ta kasance ina fita gidan mu naje gidan Kakata, wato uwar mahaifiyata na kai mata yaran da sunan munzo muyi mata yini, daya ke batasan wainar da ake tuyawa ba, bayan hankalinta ya ɗauko nafice daga gidanta na bar mata yara tare da guntuwar ta karda nayi tafi tashar muta cikin azama.

Koda lkiram ta fara kuka aka nemeni sama da ƙasa aka rasa, dan haka Kakata ta tazo da kanta har gidanmu ɗauke da yaran, koda taje Babana baya nan ta cewa lnnata ga yara nan na barmata kuma tarasa inda nashiga, haka taƙare masifarta sannan lnnata ta gaya mata halin da ake ciki mahaifina ya koreni, kuka ƴar tsoho ta sanya tana faɗin,

" Dana san haka ne ni zan ɗau kaddara ta zauna gidana".

Suna cikin haka Babana ya dawo, yana ganin yaran ya fara faɗa, wallahi sai da lnnata ta bar gidanshi amma shi bazai iya zama dani da yara ba, Kakata ce tayi saurin cewa baza ta bar gidanka ba, amma kasani kayi kuskure na korar ƴan mace, yau ko namiji ka kora ya abin ya kasance bare mace, kuma yarinya yanzu haka ba'a san inda take ba, amma tunda kace ko yaran bazasu zauna ba, ni zan ɗauke su har tsawon raina, ko kuma idan shi mahaifinsu ya dawo ko ita ta dawo na basu yaransu.

Tana faɗar haka ta fice ɗauke da yaran, koda ta koma gida tana zauna cikin ɗaki sai idonta suka faɗa kan wannan ta karda, cikin azama ta ɗauka , da yake bata iya karantawa ba sai ta tashi tashiga maƙota tasamu wani ɗan saurayi ya karanta mata kamar haka.

Hajiya Kaka ni natafi kuma sai Allah ya sake haɗamu, ga yarana nan nabaki amanarsu, dan Allah Kaka ko sun girma kada kitaɓa gaya musu nice na haifesu ko ki nuna musu suna da mahaifiya kice musu tun wajan haihuwar lkiram na mutu, ina muku fatan alhairi Kaka.

Yana gama karantawa Kaka ta sanya kuka tana faɗin na shiga uku na lalace, yanzu ƴar nan haka zakiyi ma zuri'ata, bayan Kaka ta gama kukanta ta tashi ta koma gida tabawa yaran abinci har sukayi bacci.

To haka Kaka ta cigaba da rainun Ahamd da lkiram har zuwa wani lokaci, ina can bariki amma duk abinda nake yaran na manne a zuciya ta, dana samu kuɗi  masu yawa na dawo gida, ban sauka ko ina ba sai gidan Kaka, kuɗi na bata sosai nace asayawa yaran babur abada haya kullum ariƙayi musu hidamar  yau da kullum, bayan nasa su makaranta, sannan nasaye wannan gidan da muke ciki nace ko na mutu na Ahamd ne dan nasan bashida gadon kuwa sai ni.

A lokacin ba yadda Kaka ba tayi karna tafi ba amma sai da na koma.

To tundaga lokacin na kan ɗan zo naga halin da suke da karatunsu na koma, watarana koda nazo Kaka babu lafiya rai a hannu Allah, kuma ga yara ba mai kula dasu dan haka dole na zauna ina jinyar Kaka daga baya kuma Allah yayi wa Kaka rasuwa, sosai mutuwar Kaka ta tsaya min a rai, dan haka na yanke shawar zan koma gidan dana saya nacigaba zama ni da yarana .

Haka kuwa ta kasance na koma na ciga dazama ina sana'a ina samun kuɗin kashewa da hidimar yara, ana cikin haka nasamu mijin aure mukayi aure nidashi nacigaba da bawa yarana kulawa, daga baya muka rabu, wuyar danasha wajanshi ne yasa ban sake aure ba sai yanzu nayi aure.

Wannan kena.

Mumy na gama shiryawa kai tsaye gidan mijin nata ta nufa, da sallama tashiga, basu karɓa ba har sai da tayi sau uku sannan ya fito haɗi da faɗin,

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now