31

148 11 1
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

      

*SHAFI NA 31*

Koda Hauwa ta ƙarasa gidan su lkiram ta sama tsakar gida tana bawa yarinyar ta nono, da sallama tashigo bayan ta amasa ta samu waje ta zauna kana ta dubi lkiram tace,

" Amma dai satinnan zaki koma gidan mijinki ko?".

" Eh daman tun jiya yace na koma Mama tace sai wani sati".

"Ai babu damuwa, Allah ya kaimu lafiya.wai kuna jin  mutsin Ahamd kuwa? gaba ɗaya kwana biyu na rasa inda ya ke shiga ko leƙomu ba ya yi wallahi".

" Daman ina son na gaya miki jiya ya zo wajan Mama wai ya samu matar aure kuma fa Aunty babbace dan yasin zata kai sa'arki in ma bata fiki ba, kuma yace babu wanda zai hana shi auren ta, jiya har wajan Mama tazo gaishe ta".

Gaban Hauwa ne ya faɗi, lokaci ɗaya ta tuna da ƙawarta da ta haɗa da Ahamad kar dai ace ita, cikin rawar murya Hauwa tace,

" Ikiram ya take matar, tana da haske?".

" Eh tana dashi da ganinta tasha mai da yawa, dan yasin wannan ba farinta bane dagani tana shafa man fari".

Zuface ta karyuwa Hauwa, lokaci ɗaya ta ɗauko waya ta fara kiran Ahamad.

Koda takira Ahamad yana tare da Hajiyar shi, suna tsara yadda aure zai kasance, wayarshi ce ta fara rura, ɗauka ya yi musamman da yaga sunan Hauwa ya bayya na kan wayar, tana jin ya ɗauka cikin rawar murya tace,

" Ahamd kana ina? duk inada kake kazo gida ina nemanka yanzu dan Allah".

Tafaɗi haka cikin rawar murya.

Lafiya dai ko?".

" Eh lafiya ƙalau kazo dai".

" Gani zuwa".
Haka yace da ita sannan ya katsi wayar.
            Addu'a take azuciyar ta, Allah yasa ba ita bace.

Mumy koda taje wajan ƙawarta tajima zaune kafin ta dubeta da kyau tace,

" Hajiya wallahi ina cikin damuwa, musamman na rashin sanin inda Hansa'u take, gashi yau Kabir akan ban haihu ba har gori ya yi min, wallahi har ga Allah abinda ya yi min ya taɓamin zuciya"....nan dai ta kwashe komai ta gaya wa Hajiya abinda Kabir ke mata.

Ƙara dubin Mumy tayi da kyau kana tace,

" Ai kowa zuba miki ido ya yi irin yadda kika ɗau son duniya kika ɗaurawa Kabir, gani nake ko Bashar baki yi wa irin son da kikayi wa wannan mijin naki ba, shiyasa unguwar nan kaf haushin shi ake ji saboda nuna izza da taƙama da yake shi mijin Hajiya ne, kuma dan baki da hankali har ki bar mijinki da ƴarki gida ɗaya, yanzu duniya da ta lalace ko ubanta ne kana tsoron kabar masa ƴarka bare wani miji, ai kinyi arziki ɓacewa tayi ba lalata ta ya yi ba, dan wallahi muna jin labarinshi.

Hawaye Mumy ta shafe kana tace,

" Ni nasan  auren Kabir kaddarace a wajena, kuma Allah ya riga da ya kaddari sai na aureshi, shiyasa Allah ya rabani da mijina, da ba dan mutuwa ba, yanzu haka muna tare, dama tun farko nasu ko fahinceni, Allah ya riga da yasamin son shi a zuciya na, kuma ba komai ya kawo haka ba kulawa da nuna min ƙauna shiya kuwa har na kamu da son shi, amma tunda ya yi aure har yanzu da matar ta haihu wallahi bai sake kulani ba, ke ko ya kulani kamar dole, wani lokaci sai nace wai ko magani akayi muna dan a rabamu?".

" Wallah ba magani ki daina zargi, haka ƴarannan suke ka auresu tun basu da, da zaran sun samu kaine farko wanda zasu fara gudu, ke tsaya kiji ko ƙanwata haka akayi tazo ta aure kamar sa'ar mijinki wallahi ba muso tace sai shi haka akayi aure ta ɗau komai nata ta bashi, ke bari kiji daga ƙarshe yaje ya yi aure ko haihuwa matarsa batayi ba ya saketa kuma wallahi yanzu haka ko gidan da suki ciki ita taginashi da cewar itace tazata koma ciki, ni dai shawar zan baki ki koma ga Allah kiciga da roƙonsa ya bayanar miki da ƴarki, duniyar nan baki da kamarta".

A jiyar zuciya Mumy ta sauke kana tace,

" Insha Allahu koni nayi hankali daga yau, kuma zan roƙo Allah da ya sassautamin son Kabir a zuciya ta, kuma ina ji ajikina komai daren jimawa zan haɗu da Hansa'u".

Sun jima suna fira daga bisani Mumy tayi mata sallama ta koma gida, yau har wani abu take ji kamar an sauke mata, dan rabon da tafito tayi fira da abokanta har ta manta.

Tunda Kabir ya fita gidan Mumy bai sake dawowa ba sai bayan kwana biyu, itama  bata sa damur rashin sa a gareta ba, ita yanzu burinta ta kasan ce tare da ƴarta.

Ko sallama babu haka ya shigo gidan, kallo ɗaya tayi masa ta kauda kai, zama ya yi kan kujera haɗi da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya dubeta da kyau kana yace,

" Kawo min abinci nace yaunwa nake ji!".

Murmushi tayi tayi kamar bata jishi ba, saboda yau gani take ya rainata, tun yaushe rabon da ya kawo mata kwayar gero, bare har yabata kuɗin cefene, kullum ita ke dafawa suci har shi, to yanzu ta daina tunda baya gani bare ya gode.

Dubanshi tayi tace,

" Ban dafa".

Saboda me!".

''Saboda banda kuɗi".

Tsaki ya yi kana yace,

" Nifa nagaji idan har auren ne kika gaji dashi ba dole zama dake sai na sawaƙa miki, amma dan rashin kunya na dawo gida ba ko sannu da zuwa bare kizo ki bani haƙurin abinda kika aikata min, dan na nuna kar ki lalatamin ƴa shine zaki zomin da haka".

Haka ya riƙa yi mata masifa har ya gaji ya kyaleta dan bata ce dashi komai ba, da yaga ta ɗau zafi itama ranar ko firar dare bai fita ba, yana ganin tayi shirin kwanciya shima ya zo ya kwanata haɗi da jawota jikinshi har da sauke wata ajiyar zuciya.

        ********
Koda Hansa'u ta isa parta ɗinta ciki da kunyar da kuma haushin kanta, to miyasa zatayi kuka da wanda bai damu da ita ba, kuma ko ya damu da ita ai ita bata damu dashi ba, dan ita bata ɗauke shi a matsayi miji ba, tsaki tayi kana ta cire kayan jikinta ta kwanta bacci.

Tana cikin bacci ne  ta tashi a firgece sanadiyar mafarki Mumy ta datayi tana kuka tana cewa ƴata kizo gareni wallahi ina muradinki, banda kowa aduniyar nan sama dake...dai-dai na ta farka, tashi tayi ta watsa ruwa haɗi da ɗaura alwala tayi sallah sannan taje wajan Mumy.

Koda ita isa inda Mumy tana waya, zama tayi har ta kammala sannan Mumy ta dubeta kana tace,

''Ƴar ta yaushe ne bikin makarantar ku, dan so nake kafin ya dawo kin shiga wata makaranta, kinga babu yadda zai hana kici gaba, dan nasan ra'ayishi baya son mace ta haura sama da secondary school , amma inda ya dawo yaga kin cigaba ba yadda zai yi dole ya haƙura".

" Tau  Mumy wani sati ne biki".

" Tau ya yi Allah ya kaimu".

Da amin ta amsa sannan Mumy tace,

" Nasan zuwa 8pm zasu sauka dan haka ina so ki zan mutum ta farko da zaki farayi masa barka da sauka kinji ƴata".

Murmushi Hansa'u tayi haɗi da cewa tau kana ta tashi ta koma ɗakinta, dan itakam wallahi bazata iya kiranshi ba, wata ƙiƙa ma ya zageta.

Tunda ya shiga jirgi sai murmushi ya ke, can kuma ya yi tsaki, a haka har ya sauka.

Bayan ya huta ya kira iyayenshi ya sanar dasu ya sauka, sosai suka ji daɗin haka, bayan sun yi sallama ya cigaba da harkar gabansa batare da ya kira Hansa'u ya gaya mata ba, dan shi zuwa yanzu ya manta da wai ya yi aure.

Itama a wajanta haka take kasancewa, dan ko cikin ƙawayenta bata gaya musu da ita aka ɗaura mishi aure ba, harka gabanta take, fita ko sai anbata so fita, yanzu shirye-shiryen biki makaranta suke bakama hannu yaro, yau ne suka je gidan kunshi bayan angama sukaje a wanke musu kai, ana gamawa ita da ƙawayenta suka dawo gidan Mumy, bayan sunci sunsha ne sannan tasa direba ya mayar dasu gida, saboda gobe ne bikin nasu.


*COMMENT AND SHARE*

*SUMMY M NA'IGE✍️*

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now