44

174 15 3
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*

         *Tsarawa da Rubutawa*
       *(UMMU JA'AFAR)*


*SHAFI NA 44*

Bayan ƴan kai amarya sun watse sannan Abdul ya shigo gida, kai tsaye ɓangarin iyayen shi ya nufa, zaune ya same su suna fira, dan haka shima ya samu waje ya zauna haɗi da gaishe da su.

Bayan sun karɓa ne suka ɗaura da yi masa nasiha a kan ya riƙi a manar da aka bashi, kuma ya yi ƙo ƙari ya  sauke nauyin da ke kansa in har ya na son ci gaba cikin rayiwar shi, sosai suka yi masa wa'azi kana suka ce ya tashi zuwa ga iyalin shi sai da safe idan Allah ya kaimu.

Ba musu ya tashi kai tsaye wajan da ya yi parking ɗin motar shi ya nufa, tsara bar da ya sayo mata ya ɗauko da sauran kayan sanyi.

Kai tsaye part ɗinshi ya nufa, tun bai ƙarasa ba ƙamshin turare ke dukan hancinsa, a jiyar zuciya ya sauke kana ya sa kai ya shiga parlour gidan, bai same ta can ba dan haka ka tsaye bedroom ɗinta ya shiga, zaune ya sameta kamar wata amaryar kunya ta rufe fuskarta da mayafi sai famar wasa da ya tson hannunta take.

Ƙamshin turarin shi ne ya sanar da ita zuwan shi, lokaci ɗaya tsoro da fargaba suka ɗar so a zuciyar ta, ƙara sun kuyar da kanta ƙasa tayi ta ci gaba da wasa da ya tson hannunta har taji shi ya zauna kusa da ita, haɗi da yi mata sallama.

Amsawa marya ta yi ƙasa-ƙasa.

Murmushi ya yi haɗi da jawo ta jikinshi ya na faɗar,

" Amarya kin sha ƙam shi".

Bata ce da shi koma ba, kuma bata yi wani murmushi ko nuna jin daɗin kasancewa da shi ba, saboda idan ta tuna abin da ya taɓa faruwa tsaka nin ta da shi sai ta tausaya wa kanta.

Sun jima a haka daga baya ya ce ta tashi ta je tayi alwala ta zo su gabatar da sallar nafila.

Ba musu ta tashi taje ta ɗauro alwala ta zo suka gabatar da sallah.

Bayan sun kammala ne suka yi addu'a samun zaman lafiya da zuri'a mai albarka.

Bayan sun gama ne ya je ya ɗauko tsara bar da ya zo mata da ita ya zauna ya fara bata da kanshi, da ƙar dai ya samu ta ci kaɗan sannan ya tashi ya gyara waje da kanshi kana ya ce ta je ta sauya kaya zuwa na bacci ta kwanta, sai da ta bari ya fice daga ɗakin sannan ta tashi ta ɗauko wata riga mai kauri ta sa kana tayi addu'ar bacci ta kwanta.

Taji ma kwance sannan ya shigo ɗaki, basmala ya yi lokacin da zai rufi ɗaki sannan ya kashe musu wutar ɗaki sannan ya hau kan gado haɗi da jawo ta jikin shi.

   Asuba ta gari.

Koda ta tashi jikin ta ba ƙara min ciyo ya ke mata ba, saboda daren jiya ta jigata a hannun Abdul har sai da ta kai gayi masa kuka sannan ya kyaleta.

Bayan ta kammala sallah a suba yana dawo daga masallaci ya ɗauke ta kamar wata ƴar tsana sai kan gado ya ce su rama baccin da basu yi jiya ba.

Sun jima suna bacci dan har Mumy tasa aka kawo musu breakfast ɗinsu ba su sani ba, sai da suka tashi suka gan shi, bayan sunyi wanka sun ci sannan suka zo part ɗin Mumy suka gaisheta, nasiha ta ƙarayi musu mai ratsa jiki kana tayi musu sallama suka koma ɓangarinsu.

Ranar Abdul ba inda ya fita sai washi gari ya fita koshi saboda zai fara yi musu shirin tafiya ne, saboda wani sati za su bar ƙasar.

Duk wani shiriye-shiye ya kamala musu na tafiya, mahaifinshi ne yace ya kaita wajan ƴan uwa da ƴan uwanshi suyi ban kwana.

Haka kuwa ta kasance, kai tsaye gidan  Kaƙar shi ya fara kai ta, wato mahaifiyar Daddy , bayan ta gama yi musu duk wata nasihar da zata yi musu suka wuce gidan Yayan Daddy, wato Alhaji Nura.

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now