28

174 14 1
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*



*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*

      
*_INAYIWA ƳAN UWA DA ABOKAI BARKA DA SALLAH, ALLAH YA ƘARƁI IBADON MU, YA NUNA MUNA WATA CIKIN ƘOSHIN LAFIYA._*

*SHAFI NA 28*

Gab da zai shiga mota suka ƙaraso, tsawa suka daka masa akan kada ya shiga motar, tsayuwa ya yi ya ɗago da kansa yana musu kallon rashin sani, dan shi bai taɓa gani su ba bare a ce yasan su.

Baki ya buɗe dan ya yi magana bai ankaraba yaji sun kai masa bugu a fuska, cikin zafin nama ya tare, amma duk da haka sai da ya shafe fuskarshi, Abdul naganin haka shema ya gyara hannayen rigar sa, dan shima ba baya ba wajan iya faɗa.

Ɗaya bayan ɗaya yake faɗa dasu har yasa mu yaci galaba a kansu saboda dukkansu ƴan shaye-shaye ne, shiko baya shan komai sai dai idan ka ganshi zaka ce yana shan kayan maye, shiyasa yafisu ƙarfin damtse.

Guduwa sukayi da suka ga so yake ya illatasu, shiko yana ganin haka ya shiga mota ya bata wuta, bai tsaya ko ina ba sai gida.

Parking ɗin motarshi yayi kana ya fito, kai tsaye part ɗinshi ya nufa, ko kallon ɗakinta bai yi ba ya ƙarasa nashi ɗakin, toilet yashiga ya sakarwa kanshi ruwa zuciyar na zafi, yana fitowa ya buɗa firij ya ɗauko ruwan gora ya sha, daga bisani yabi lafiyar gado sai tunani yake wai shi za'ayi wa auren dole.

Gari na waye wa, Hansa'u ta fito daga part ɗinta ta koma part ɗin Momy, can tayi wanka ta sauya kaya, har zata shiga kicing sai ga Momy tafito, da sauri ta buɗe ido tace,

" Yaushe kika shigo nan?".

Murmushi tayi haɗi da sun kuyar da kai tace,

" Yanzu nazo Mumy nayi wanka, shine naga baki tashi ba nace bari na ɗaura muku abin karyawa".

" A'a dan Allah rufamuna asiri har yanzu da mutane a gidannan kawai kiyi sauri ki koma part ɗinki kar wani ya ganki".

Tace,

"Tau mumy".

Ko mawa tayi, palo ta zauna ta kunna tv ta fara kallo, amma a zahirin gaskiya ba kallo take ba tunanin Mumy ta take, dan duk jin daɗin da zata samu burinta ace tana tare da mahaifiyar ta.

Tana cikin haka taji ƙamshin turare, da sauri ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, tsaye ta ganshi sanye da wata danƙareriyar shadda tayi masa masifar kyau haskin sa  ya ƙara fitowa, kai sai kace wani jinin turawa.

Kallo ɗaya ya yi mata ya kauda kai haɗi da yin wani tsaki.

A hankali ta durƙusa ƙasa tace,

" Yaya ina kwana".

Wani baƙin ciki ne ya rufe masa zuciya dan haka ya bar palon batare da ya kalle wajan da take ba bare tasa ran zai karɓa.

Haka da ya yi mata ba kaɗan taji zafi ba, lokaci kaɗan idonta suka fara zubar da kwalla.

  Bayan kwana biyu da biki, duk wani ɗan uwa da yazo daga nesa ya koma gida, gida yarage daga Mumy sai Daddy sai Hansa'u sai Abdul.

Yau gaba ɗaya Daddy ya tarasu falo bayan sunyi beark sannan ya yi musu nasiha akan suyi haƙuri da junan, su zauna lafiya yana so subawa maraɗa kunya baya su aji.

Bayan Daddy ya gama musu nasiha ne sai Abdulrazak ya dube Daddy yace,

" Daddy dama ina so na gaya muku jiya wajan aikinmu sun turani Germany in yi wani karatu wanda zai ƙara taimakar ma'akatar".

" Masha Allah , abu ya yi kyau, sai kutafi kai da Hansa'u in yaso itama sai ta ƙarasa karatun ta a can".

Cewar Daddy kenan.

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now