26

174 6 0
                                    

*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*


*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

               *Z.W.F.🏝️*

*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*



*SHAFI NA 26*

Haka aka akmmala ɗauren aure kowa ya watse ciki da farin ciki musamman Daddy shida aka so yayi kunya Allah ya fitar dashi wannan kunyar ta abokai da ƴan uwa, dan ko Yayan Daddy sosai yayi mamaki ina aka samu ma Abdulrazak mata, wani marar hankali ne zai bawa ɗan daba ƴarsa, bashi da amsar wannan tambayar ko ɗaya dan haka ya zuba na mujiya.

Gida ya dawo shida abokanshi duk sai ya nemi ɓacin rai ya rasa sai farin ciki yake shida abokansa, haka suka riƙa tsokanarshi da angon Hansa'u.

Abokinshi ɗaya ya maida hankali wajansa yace,

" Yusuf daman yarinyar nan Hansa'u ne sunan ta?".

Harara Yusuf ya galla masa kana yace,

" Kai baka san sunanta ba, to ni ya zan san sunan ta".

" Naga kune kuka buga lb shiyasa na tambaye ka, amma ni a sani na kamar Fatima ne sunan ta".

Har Yusuf ya buɗa baki yayi magana sai ga Mumy tashigo ɗaki sai zuba kamshi take, kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin farin ciki.

Gaishe ta suka farayi ciki da kulawa, itama ta karɓa musu kamar yadda suka gaishe ta, zama tayi kan ɗayan kujera  kana ta dubeshi shida abokansa kuma ɗiya ga ƴan uwanta tace,

" Naga sai murna kuke baku zo  tambaya ya akayi wannan juyin mulki ba, nan da ta gaya musu halin da ake ciki, sosai suka ji zafi haka da akayi wa Abdul, dan su zaman da sukayi dashi ko sigar basuga yasha ba har yanzu, amma mutane da dama suna faɗin yana shan kayan maye.

Baice da Mumy komai ba har sai da tafice sannan ya ɗago da kai ranshi a ɓace yace,

" Ni wallahi da ma sun sani afasa wannan aure, har sai anyi min haka, a haɗani da wata ƴar mitstsyar yarinyar da ko rainunta ba'a gama ba ni sai a haɗani da aiki, wallahi ko kallonsu bazanyi da ita ba gwara ma tun wuru su san abinyi".

Haƙuri abokansa suka riƙa bashi amma ya ɗau zafi, daga ƙarshe makulin mota ya ɗauka yafice gidan bai tsaye ko ina ba sai wani sabon gidan karuwa da aka buɗe.

Ranshi a ɓace, kowa ya buɗa baki yace yana shin kayan maye, ko yana kula mata, har yanzu zai iya rantsuwa da Allah bai taɓa shan komai na maye ba, kuma bai taɓa an fani da kowace irin mace ba, amma yau tabbas zai fara, gwara yayi sai ace yayi da bayayi amma ace yana yi.

Ana gama ɗauren aure Daddy yakira masu sayar da kayan ɗaki aka zo akayi jere, sosai Daddy ya gyaramata ɗaki, ita ko Mumy na can tasa amarya gaba saboda wani zazzaɓi ya tasu mata lokacin da aka ɗaura wannan aure dan har ga Allah bata taɓa jin son Yaya Abdul a ranta ba, amma ya zatayi tunda gashi tazama matarshi.

Haka aka kammala biki lafiya kowa ya koma gidansa.

Kwalbar giya ce gabansa an zuba masa cikin cup sai kallon cup ɗin yake yana tunanin wani abu a ranshi, yana cikin haka sai ga wata matashiyar buɗurwa sanye da wasu kananun kaya waɗanda suka bayyanar da siffar jikinta, hannuta ta ɗaura saman lallausar sumar kanshi.

A hankali ya juyu dan yaga ko wacece.

    ***********

Da kyar Hauwa ta iya shiga gidan saboda warin da yake, ko yanzu fita tayi tasamu almajirai ta biyasu suka gyara ɗakin Babanta kana aka sauya mishi tufafi sanna ta samu ta zauna.

MIJIN BABATA NEWhere stories live. Discover now