💞💞💞LAILAH💞💞💞
STORY AND WRITTEN BY
AISHA MA'ARUF(GIMBIYA AYSHU)
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚
Page 9-10
___________________Lailah nada lectures kuma na safe,bayan ta gama tayi wa Mama sallama ta wuce,bayan minti 20 suka isa,ba bata lokaci ta shiga cikin hall,karfe sha biyu suka gama lecture,cafteria suka nufa ita da wata yar ajin su,sha biyu da minti arba'in da biyar suka bar cafteria zuwa masallaci dan suyi sallah,bayan sun fito suka nufi hall.daya da rabi daid-dai malamin ya shigo ya rubuta musu test sannan yace minti ashirin kawai ya basu,bayan an gama yasa class rep ya hada mishi papers din,bayan kowa ya gama harhadawa ya bashi,lecture ya fara,uku da rabi dai-dai ya fita bayan ya kwashi test script da handout din shi,bayan ya fita a ka fara watsewa dan an gama lecture na ranan.
Bayan Lailah ta fito ta tadda driver dan dama ta gayamai lokacin da zai zo, back seat ta bude ta shiga,direct gida suka nufa,yana gama gyara parking ta fice abin ta tare da mai a huta gajiya,zaune ta tadda Mama hannun ta rike da Al-Qur'ani tana karantawa,gaida ta Lailah tayi,Mama ta amsa dai-dai tana kulle Al-quranin dake hannun ta tace"ya test din,da Alhamdulillah Lailah ta amsa ta manna wa Mama peck a goshi,toh ga abincin ki a cooler,ki je ki watsa ruwa sai ki zo kici abinci,"am full first luv, bari anjima",da toh Mama ta amsa,"daki Lailah ta nufa,bayan ta gama cire kayan ta ta shiga bathroom,wanka tayi tare da alwala dan lokacin la'asar ya kusa",bayan ta fito ta shafa lotion ta dan shafa powder kadan,tasa lip gloss,Kiran sallah da ta ji ne ya sata mikewa ta nufi drawer ta dau kayan da za ta sa,bayan ta gama shiri ta shifida darduma tasa hijab dinta ta tayar da sallah bayan ta idar ta danyi addu'an da ake bayan an idar da sallah,sai tadan kwanta dan ta huta,barci yayi awon gaba da ita,ba ita ta tashi ba sai 6:00pm,tana tashi tayi addu'ar tashi daga barci ta miki ta linke darduman ta cire hijab din ta ta shiga bayi,brush tayi ta fito parlor,ta samu babu kowa,kitchen ta shiga ta dauko abincin ta ta ci,bayan ta gama ta shiga kitchen dan daura abincin dare,ruwa tasa a tukunyya ta daura a gas,ta debo wake ta gyra dai-dai ruwan ya tafasa,ta wanke ta zuba,tasa kanwa kadan ta kulle,kayan miya ta gyra, kafun bakwai ta gama girki,shinkafa da wake jelof ta dafa,da cos low,sai water mellon and cocumber juice,jera coolers din tayi kan dining taje tayi sallah,bayan isha'i suka ci abinci,lokacin kwanciya nayi su kabi lafiyan gado.
Washe gari Saturday,tun karfe goma duk suka gama shiri zasu gidan yayan Daddy su sada zumunci,mota duk suka shiga,da kanshi Daddy yayi driving,a cikin 1 hour suka isa,danna door bell Lailah tayi,Mum ta amsa daga ciki ta bude kofan tace a'a manyan baki zuwa ba sanarwa,ta fada tana rungumar Lailah,"surprise mu ka muku,cewar Mama",naga alama kam,ina sauran mutanan gidan cewar Abba bayan sun gaisa da Mum,su twins na sama,Abba da Muhammad kuma sun fita,kwala ma twins kira Mum tayi,ba bata lokaci suka sauko,bayan sun sauko su kaga i Daddy da family shi ne,da gudu suka nufi Mama suka rungume ta,kun ki girma har yanzu,dariya su kayi hadi da cewa we miss u Mama,"ba wani miss,ku da ba ku zuwa inda nake",noooooo! Mama ba haka bane,school ne wlh,amman za muzo insha Allah,da Allah yasa Mama ta amsa,suka amsa da Ameen,barin Mama su kayi suka rungume Lailah da Husna,a tare suka gaishe da Daddy,ya amsa da twins dina ya kuke,ya school,lfy lau Daddy,ya aiki,da Alhamdulillah Daddy ya amsa yace"yaya fa,wlh ya fita,bai ma jima da fita ba,bari ma na kira shi,da toh Daddy ya amsa,sama Mum ta haura dan ta dau wayar ta,kiran Dad tayi,bayan ya daga tace ga Alhaji karami da iyalan shi,ahhhhh! shine ba sanarwa,ga ninan dawowa yanzu insha Allah,da toh Allah ya tsare Mum ta amsa,bayan kaman minti ashirin Dad ya iso,gaisawa su ka yi,Dad yace zuwa babu notice,i da na san da zuwan ka da ban fita ba,gaida shi Mama tayi kafin su Lailah,amsawa yayi tare da tanbayan su ya karatu,da Alhamdulillah duk suka amsa tare da tanbayan shi ya Aiki,da Alhmd Dad ya amsa yana mai sa musu albarka,hira su ka fara,kitchen Husna da twins suka shiga dan taya Mama da Mum girki,abinci kala uku da local drinks suka hada,bayan sun gama girkin aka zuba a cooler masu daukan ido,daukan cooler twins su kayi suka nufi dining area suka jera,bayan sun gama kwashewa su Mama suka fita parlor suka ga babu kowa,"ko sun fita ne,cewar Mama",da wiya fita suka yi dan banji karar kofa ba,bari dai na duba sashen Alhaji,ki shiga daki na ina zuwa,da toh Mama ta amsa ta amsa,part din Dad ta nufa,tun kafin tayi knocking taji dariyan su sai kawai ta juya ta koma dakin ta,a zaune ta tadda Mama gefen gado da waya a hannun ta alaman yanzu ta gama waya,shine baki shiga wanka ba cewar Mum,da a'a babu komi Mama ta amsa,haba hajiya haka za muyi da ke,nanma fahh....... kaman gida ne,ba haka ba ne,ban zo da wasu kayan bane,indai kaya ne matsalan ki toh karki damu,ina da wani sabo zan baki kisa,tohh ya na iya dake,wanka ta shiga bayan ta fito Mum ta nuna mata lotion din da zata shafa da turarurruka tace ga kayan nan saman gado nima bari na shiga na fito,to a fito lfy.
YOU ARE READING
💞💞💞LAILAH💞💞💞(COMPLETE)
RomanceWallahi ko zaka mutu bazan taba auren kaba yaya Abba na tsaneka na tsani duk mai sonka, "ni sa'ad nakeso kuma shi zan aura" ta karasa fada tana fashewa da wani irin matsanancin kuka mai taba zuciya. Daddy daya shigo parlorn ya Daka mata tsawa "wlh...