PAGE 71-72

140 17 4
                                    

💞💞💞 LAILAH💞💞💞

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU 💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚

INA MUKU BARKA DA SALLAH EN UWANAN MISULMAI,ALLAH YA MAIMAITA MANA.AMEEEEEEEN.

                  WHATPAD LINK

https://www.wattpad.com/user/AishaMaaruf1?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

PAGE 71-72

_____________________________Washe gari tun karfe 5:00 Sa'ad ya tashi,bayi ya shiga yayi Alwala bayan ya fito ya nufi inda Amaryar shi take kwance,Dan yaye bargon yayi,ruwan dake hannun shi ya yayyafa Mata,Yana Dan hura Mata iska ahankali,blinking idon ta tafarayi,"yace sweetheart ki tashi lokacin sallah yayi",bude idan ta tayi a hankali ta kalle shi,hada Ido sukayi da hubbinta,kashe Mata Ido yayi yace bby wake up zantafi masallaci karma makara,gyda mishi Kai tayi tana murmushi, murmushi Shima yayi sannan ya fice a dakin,tashi tayi ta shige bayi tayi wanka,brush da Alwala,bayan ta fito ta saka wani dogon riga kalan Marron,hijabi tasa sannan ta tayar da sallah,raka'atanil fijir tayi,(Yana da kyau duk wani musulmi yayi wannan sallah,Shima kariya me ga nawa,Allah yasa my dace ya kare mu daga sharrin mutun da Aljan,yasa mu dace duniya da lahira).bayan ta idar tayi sallan Asuba,Bayan ta idar ta Fara karatun Al-Qur'ani da Azkar,ba ita ta kammala ba sai karfe 7,dai-dai ta mike zata ajiye Qura'anin hannun ta da Azkar mijin ta ya shigo bakin shi dauke da sallama,amsa mishi Aysha tayi tana gaishe shi,"amsa Mata yayi da murmushi a fuskan shi,sannan yace kin tashi lafiya bby" dukar da kanta tayi tana murmushi ta amsa mishi da lafiya Lau a kunyace,"karasowa dakin yayi ya rike haban ta sannan ya dago kanta sama tana kallan fuskan ta"
Itako Yana dago kanta ta sauke idan ta kasa,peck yayi Mata a goshi sannan yace Allah yayi Mata Albarka,amsawa tayi da Ameeen a hankali.ansan Qur'anin hannunta yayi ya ajiyeshi a inda ake ajiyewa,itako ta linke darduma ta ajiye,gyara dakin ta farayi Shima ya matso Yana tayata, sukayi suna Hira ya lura haryanzu Bata sake da Shiba Amman ba damuwa with time komi sai Zama labari.bayan sun kammala parlor Suka nufa,dayake parlor ba ayi komai ciki ba already a gyare yake,tularen wuta kawai ta kunna,sannan ta nufi kitchen duk Yana biye da ita, breakfast suka hada a tare sunayi suna Hira gwanin ban sha'awa,basufi minti 30 ba suka Gama,Sa'ad ne ya kwashi duka coolers din da flask ya Kai dining,itako ta share kitchen ta wanke kwanonin da aka Bata,bayan ta kammala ta nufi dining table, serving dinsu tayi inda zata zuba a wani plate yayi saurin hanata,hada musu tayi a plate daya,sannan ta hada mutsu tea,Zama tayi suka Fara cin abincin,diba yayi yakai bakinta,dago shanyayyun idanuwan ta tayi ta kalle shi kafin ta bude Dan karamin bakin ta ta amshi abincin ta tauneshi da natsuwa,haka dai suka cigaba da cin abincin,Yana feeding dinta itama tana feeding dinshi.

Zaune Lailah take a kujera Mai zaman mutun biyu ta mimmike abinta,jikin ta sanye da bomshort Jeans color,sai wani singlet Mai hannun shimi da tasa kalan fari,gashin kanta ko ya Sha parking ya Sha gyara sossai,sai kamshi Mai Dadi k tashi daga jikin ta,gaban ta ko cup ne Mai cike  da 5alive a ciki,sai charting take tana korawa da shi,tana cikin charting a WhatsApp ko Mai ya tabota oho!,sai kawai ta sauka ta koma Instagram,tana login first thing da idan ta ya Fara cin Karo da shine hotunan su Sa'ad da videos dake ta yawo a medai,tana cin Karo da hoton wani iron tari ya tsarke ta,tari ta farayi ba kakkautawa,idan ta ko harda hawaye,ta for minti 10 kafin tarin ya Dan lafa Mata,hawaye Mai zafi ne ya zubo daga idan ta,tunanin zuci ta Fara kodai bashi bane,kaiiiiii........ Shine Dan kamannin shi bazai taba bace min ba,daukan wayan ta karayi,tanasan ta tabbatar da abunda idan ta ya gani,tanacikin kallan wani video bikin taga Hydar Yana bada labarin Ango,wani irin sarawa taji kanta yayi mata,hannu tasa ta tallafi kan tana hawaye,tabbas tasan wannan fuskan,Kuma ba kowa bane face Abokin Sa'ad saboda akwai abin da Hydar ya Fadi Wanda Sa'ad ya Gaya Mata haka,haka ta cigaba da kallan videos din har tazo ta daina ganin wayan,baya tayi zata fadi,sai ga kawarta zainab ta shigo,saurin karasowa Zainab tayi tana Kiran sunan ta da ihu,jijjiga ta take tana Kiran sunan ta,shiru kake ji ko alaman motsi batayi ba,tashi Zainab tayi da gudu ta nufi inda fridge yake,budewa tayi ta dau Goran ruwa Mai Dan sanyi,ko kulle fridge din Bata Gama Yi ba ta nufi inda Lailah take,ruwan ta bude kwai ta kwarara Mata ajiki,hawaye kawai zainab take tana Kiran Lailah tana kuka,tana zuba Mata ruwan ko taja ajiyan zuciya Mai karfin gaske,dagota Zainab tayi tasa hannu biyu ta rungume ta tana kuka tana shafa bayan ta,baya kaman minti 5 ta cire ta daga jikin ta tana duba lfiyanta,Kara rungume ta Zainab tayi tana kuka,itama Lailah kuka take,haka Suka dinga kokawa har na tsawon minti 15,Zainab me tayi jarumtar lalashin su,Bayan kukan ya lafa,ta mikar da ita suka nufi dakin ta,zaunar da ita tayi a gefen gado, bathroom ta shiga ta hada mata ruwan wanka Mai zafi,fita tayi ta dau towel ta Mika Mata sannan ta riketa har ban dakin,Bayan kaman minti 20 Lailah ta fito hannun ta rike da kanta,Mai Zainab ta Mika Mata Amman ta kasa shafawa,Zainab me ta shafa Mata man Kuma tasaka Mata dogon riga Mai Dan kauri Dan ta lura tanajin sanyi,Bayan ta Gama ta kwanta a kan gado taja bargo,Zainab me ta tanbaye ta Mai ya same ta,hawaye ne ya zubo daga idan Lailah,shiru tayi ta kasa magana,chan bayan kukan ya Dan lafa mata,shine ta zayyane Mata abin da yasa ta cikin wannan halin,ta karasa da itakam Bata yarda ba kodai ba shi bane,I in shine zata ji q wurin course mate dinta kokuma a wurin Zainab,Amman taji shiru kaiiiiiii......duk tabi ta rikece ta koma kaman wata tababbiya,shiru kawai Zainab tayi tana hawaye,karasowa tayi ta rungume Lailah tana hawaye,sun shade minti 5 a haka kafin Zainab ta nufi Baki ta gayamata abin da ta gani gaskiya ne Kuma wacce ma ya Aura makaranta daya suke,wani irin zabura Lailah tayi ta mike,chan Kuma ta koma ta kwanta jagwab ba alamun nunfashin a tare da ita,fashewa Zainab tayi da kuka tana Kiran Lailah,Dan Allah karki mutu ki barni Dan Allah ki tashi,jijjiga ta kawai take Amman shiru,alamun bude kofa taji,juyawa tayi da sauri,Ido hudu sukayi da Abba,a sitting ta fita daga kan gadan ta nufi Abba tana kuka tana nuna Mai inda Lailah ke kwance,Nan take Shima ya rikice ya karaso inda Lailah k kwance,jijigata yayi Amman Bata mosa ba,daukan ta yayi da tsauri ya nufi waje da ita,hijab Zainab ta dauka da takalmi ta bi bayan shi da ita,horn yayi da karfi Mai gadi ya bude mai,da gudu ya bar gida,bin binyan shi da kallo Mai gadi yayi Dan da gani kasan ba lafiya.

💞💞💞LAILAH💞💞💞(COMPLETE) Where stories live. Discover now