PAGE 29-30

128 19 1
                                    

💞💞💞LAILAH💞💞💞

STORY AND WRITTEN BY

AISHA MA'ARUF
GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

       SHARE  FISABILILAH

*Gimbiya Ayshu's  Data service*

*Ku siya data a garabasa*

*MTN*                   

500MB-180
1GB -280
2GB - 550
3GB - 750
5GB - 1250
10GB -2500

*AIRTEL*
300MB - 170
500MB - 200
1GB - 300
2GB - 550
5GB - 1350
10GB - 2600

*GLO*

200MB - 120
500MB - 180
1GB - 300
2GB - 550
3GB - 850
5GB - 1350
10GB - 2600

*9MOBILE*

500 - 180
1GB -280
2GB - 550
5GB - 1300
10GB - 2500

Account number:8036434941

Account name: Maryam Maaruf Muhammad

Bank name:Opay

*Contact me on this number:08076119294*

PAGE 29-30

____________________washe gari Sunday bayan sun yi sallar asuba suka nufi kitchen,bayan sun gama suka koma barci,ko da wasa Mum bata tashe su ba,ta bari su tashi da kan su,tasan duk gajiyar jiya ne,ba su suka farka ba sai sha biyu da rabi na rana,wanka duk suka yi,idan daya ta fito sai daya ta shiga,bayan sun yi sallah suka sauko downstairs a tare suna tafe suna hira gwanin sha'awa.

Da misalin karfe biyar na yamma suka kammala shirin komawa gida,daga Mum har yaran ta basu so tafiyar su ba amman babu yanda ta iya,wani katan laida Mum ta mikawa Lailah wanda yake shake da kaya,amsar laidar ta yi tana godiya sosai,rakasu su Mum suka yi har bakin motar yaya Abba dake fake a harabar gidan,har hawaye su ka yi da zasu rabu da juna,murmushin karfin hali kawai Mum take amman ji take kamar ta yi hawaye,Allah ya sani tana mugun son yaran kanin mijin ta sosai.

Ramlat na Sharar hawaye ta ce"Allah sarki Mum kamar kar su tafi wallahi,zan yi missing din su".

Amsawa Raihan ta yi tana sharan hawaye ta ce"za muje gidan su idan mun yi hutu koh Ramlat?",ta fada tana share hawayen idan ta.

Dariya Mum ta yi ta ce"ku kuka sani,idan kunga dama ku tafi yanzu,karewar abin kenan",dariya yan biyu suka yi tare da bin bayan maman su.

Cikin minti ashirin suka isa,suna isa Husna ta fita da gudu ta nufi cikin gida,kokarin bude kofar Lailah ta yi amman ta ji shi a rufe,ji ta yi gaban ta ya fadi amman ta dake bata bari ya gane ba,wasa da yatsar hannun ta take gaban ta na faduwa,Allah Allah take ya sallame ta sabida a mugun takure take,ji take kamar nunfashin ta na tsarkewa.

Ganin bai ce mata komi ba har tsawon minti uku  ne yasa ta fadin"zan fita yaya".

"Shiru ya yi ba tare daya amsa mata ba",dagowa tayi taga yana kallon ta,turo baki ta yi ta saukar da kanta kasa tana wasa da zoben hannun ta.

"LAILAH",ya kira sunan ta da wata kasalalliyar murya,jan nunfashi ya yi ya ce"mai yasa kike min haka ne Lailah,ko kina da wanda kike so ne?",ya fada tare da tsare ta da ido.

Wani irin faduwa gaban ta ya yi jin abinda ya ce,shiru ta yi ba tare data ce mishi komi ba har tsawon minti biyu.

Murmushi ya yi ya ce am serious dear,idan akwai ki gayamin,"FARINCIKIN KI SHINE NAWA".

Dagowa ta yi ta kalle shi idon ta cike da hawaye.

"Talk to me pls I will help you out insha Allah".

"Share hawayenta ta yi ba tare da ta ce komi ba",shiru ne ya ratsa har na tsawon minti biyar.

💞💞💞LAILAH💞💞💞(COMPLETE) Where stories live. Discover now