💞💞💞LAILAH💞💞💞
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU 💞💞💞
ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚📚📚
PAGE 61-62
___________________________Sunje wurare dayawa basu suka dawo ba sai 9 na dare,agajiye duk suka dawo da Kaya niki niki,bajewa duk sukayi a parlor suna gaishe da mummy,bayan sun gaisa daki duk suka nufa,Lailah ko dakin mummy ta shiga da kayan ta a hannu,batan tayi wanka ta shafa man mummy ta shirya,bayan ta gama tasa hijabi sannan ta tada sallah,bayan ta idar ta linke hijabin da darduma,dakin su twins ta nufa ta tarar duk sunyi wanka,Husna cr kawai k sallah,Zama tayi Suka cigaba da hira kafin Husna ta idar,bayan ta idar tayi Addu'a ta linke darduman da hujabi,wurin su ta zo,zata zauna Lailah tace karma ki zauna parlor muka nufa,mikewa duk sukayi suka nufi parlor,samun mummy suka yi da Yaya suna hira,Shima yayi wanka ba kayan jikin shi bane,Hira suka Fara yi,Lailah ne ta ta tashi tace mummy muje muci abinci,tashi duk sukayi suka nufi dining,Lailah ne tayi serving din su gaba daya, bayan an Gama cin abinci Suka nufi parlor aka cigaba da hira basu Suka nufi wurin kwanciya ba sai karfe 12.
Da mama taji shiru har karfe tara basu dawo ba sai ta Kira mummy,bayan sun gaisa tayi tanbayan Yara duka kafin tayi tanbayan su Lailah akn ko zasu dawo,dan dariya mummy tayi tace ayi Mana afuwa maman Yara bazasu samu Daman dawowa yau ba gaskiya sai dai gobe insha Allah,da toh bakomi mama ta amsa sannan tace dama ta Kira be Dan tasani,Hira Suka Dan taba kafin Suka ajiye wayan.
Suna komawa daki Raihan ta tura ma yayan ta hotunan,tana dubawa ko ta gan shi online,chart Suka Fara yi,chan yace mata ya dill din mu was it successful and fantastic,dariya Raihan tayi tace Kai Yaya soyayya dadi, murmushi kawai yayi yace bazaki gane ba,hotuna da video da ta dauka ta tura mishi,wurin 65 zaro Ido yayi yace waiiiiii! sisi kinyi kokari gaskiya ya kamata a Kara Miki gyra,dariya tayi tace Allah ko Yaya,kasan muna hi da Kai duk abin da kake so muna kokarin yi ma, murmushi yayi,tura mata kudi yayi 150k,tana chart taji wayan ta yayi karan alert,har taso ta share sai kuma tace bari ta dai duba,dubawa tayi ta saman waya taga ansa credited,tashi tayi da tsauri ta zauna akan gado da kyau,ta bude, message din Dan ta tabbatar,iko tana budewa idan ta ya Fara sauka akan sunan Wanda ya turo mata,gani tayi sunan yayan tane, amount ta duba taga 150k ihu tayi ta daka tsalle akan gado tana rawa,Dylan su dake daki sai da Suka tsorata harda Husna data Fara barci,Mari Ramlat ta sakin mata a baya sannan tace Amman k banza ce wannan irin ihun fahhhhh! Haba bakisan dare yayi ba,dariya Raihan tayi sannan tace wlh bazaki gane ba,Lailah ko kallon ta kawai take Bata ce komi ba,nuna mats abin da yasa ta ihu tayi,zaro Ido Ramlat tayi sannan ta matso kusa da Raihan tace sis waya tura miki wannan makudan kudin ta fada tana rike haba alamun mamaki,dariya Raihan tayi tace kinsan waye ne,girgiza Kai Ramlat tayi akan Bata sani ba,kinsan kiji,girgiza mats Kai tayi,Yaya ne ya tura min,wani yaya,yaya Abba Mana,Mai kikayi da ya baki,Ina ruwan ki k dai bana nuna Miki ba,dai-dai nan mama ta shigo tace wayayi ihu,Mai yafaru,Raihan ne tayi tsaurin cewa kenkeso ne ya haumin jiki,Allah ya kyauta,mama tace sannan ta wuce dakin ta,chart Raihan ta koma tayi ma Abba godiya sossai,kwanciya duk sukayi,Asuba ta gari.
Washe gari tun karfe 5:00 duk suka ta shi,Kuma ba su koma ba,batan sun Yi sallah aikin gida suka kamayi,karfe 9:00 dai-dai suka Gama komi da komi,wanka duk sukayi,mummy ne ta kawo musu Kaya sabbi Kal a laida,atanfa ne Mai kyau Mai tsada,amsa Lailah tayi tayi mata godia sossai,bayan sunyi wanka Suka shirya cikin kayan da mummy ta Bata,sukayi kwalliya sossai,dai-dai sun gama makeup suna hoto mummy ta shigo da laida a hannun ta tace,daughter gashi,da tsauri Lailah ta karaso ta amshi laidan tayi ma mum godiya sossai, bayan mum ta fita ta bude laida ta ga takalmi ne da gyle sai jaka,masu mugun kyau,Raihan ne tace Lailah mu gani,nuna mats jakan tayi,da wow Raihan ta Masa tace kaiiiiiii! Jakan Nan ya hadu wlh Kai mummy ta it's zabe wlh, Murmushi Lailah tayi,Lailah ne tace kuyi tsauri mu tafi fahhhh! Dauka gyalen su da jakunkunan su sukayi,fita sukayi daga dakin suna saukowa step suna hira,Lailah na sanyya kafan ta a parlor ta jiyo sallaman Abba,sai da gaban ta yabada wani Karan da ita kadai ta iya jin shi,shigo Yana shiga idan shi yafada kansu saboda Karan takalmin su,kallan su tafara Yi daya baya daya,Kai da ganin kallan Nan kasan akwai alamun tanbaya,bai ce musu komi ba ya bari suka karaso,gaishe shi duk sukayi a tare,saman Lailah tace mummy zamu wuce,wani kallo Abba yayi mata,iko tana ganin kallon sai da cikin ta ya bada kuuuuuullllllllll! Wanda har Karan sai da yasa Raihan dake kusa da ita ta juyo ta kalle ta,dariya ta kwashe dashi har da rike ciki duk kallo ya dawo kan ta,Dan su Kam basu San Mai yasa ta dariya ba,mama ne tace lafiyan ki kuwa,naga kaman kwanan Nan Baki da lafiya,zan da yayanku yayi maganin ki in Baki shiga taitayin ki ba,gimsewa tayi,Ina zakuje,shiru duk sukayi,Lailah ne tayi karfin halin cewa wai fita zamuyi,zuwa Ina,unguwa,unguwan baida suna be zunguro Dan karamin bakin ta tayi, murmushi yayi ya soda kanshi,I ko Babu inda za kuje in dai Baku Gaya min ba,Dan murmushi Lailah tayi tace haba Yaya na,kayi hakuri ka bari muje pls kaji,bazamy Dade ba plssssssssssssss,kanne Ido daya yayi Yana kallan ta,sai da yayi minti 5,kafin yace kuje Amman karfa ku dade,har sun Kai kofan parlor, sai Abba yace kujira Ni zan Kai ki,salati Lailah tayi Dan ya Bata mata budget,sallama yayi ma mummy dama da makullin a jikin shi,fita duk sukayi a parlor,mota duk suka shiga Suka wuce,suna cikin mota yace Ina zakuje,shiru duk sukayi na minti 2 daga baya Lailah tace Dizeny,komi bai ce ba ya dauku hanyyan zuwa wurin,Yana kaiwa ya ajiye su,Yana zaune a motan ya ga wani na auna ma abin kwaunar shi kallo,hada Rai yayi sossai,fita yayi a motan sannan ya fita,Yana shiga cikin wurin ya tadda wani Yana mats magana,tsayawa yayi Yana kallan shi,zuciyar shi sai tafarfasa yake,dago kan da zatayi ta hango shi a bakin kofa, Addu'a tafara a zuciyar ta Dan ita Kam ta bani,taga kwanan nan yanaji da matsifa,ita Kam ta shiga su,takowa ya farayi a hankali fuskan shi a hade kaman hadari,Yana kaiwa wurin yace kai,juyowa guy din yayi ya kalle shi sannan yace lfy,zaka tanbaya Ni lfy kana magana da matana,zaro Ido guy din yayi yace Amman sun ce min ba matan aure bane,toh Ni nace maka matatace tashi ka bani wuri,tashi guy din yayi Dan ba Mai hayaniya bane,Zama yayi akan kujeran da ya tashi Yana kunbura Yana sauka kaman farashi ya tashi a kasuwa,ana cikin haka wayan Lailah yayi ringing,sai da cikin ta ya bada kullllllll! Dan ita Kam a rayuwan ta batasan fada,daukan wayan tayi tasa shi silent wanna ta tura mishi message akan zata kirashi,haka dai Suka cigaba da Zama a wurin duk a takure take,kayan kwalama Suka Sha sannan Suka siya wani akayi packaging din shi a laida Suka tafi da shi,daga Nan bai zarce dasu ko Ina ba sai gida.da sallama Suka shiga Babu kowa a parlor haurawa sama Lailah tayi ta cire kayan jikin ta ta daura towel ta shige bayi bayan ta fito tasa kayan Ramlat, tayi sallah,taja idarwa ta Kira Rabin heart,suka Sha love din su,yace sweetheart inasan mu hadu gobe,shiru Lailah tayi Dan batasan irin karyan da zatayi a bari ta fito ba,yace ta dai kinyi shiru, murmushi tayi sannan tace a'a ba komi Allah kaimu, washe gari karfe 10:00 na safe su Lailah Suka koma gida tare da kayan sallah Mai yawa daga wurin mummy,kids Suka dawo komi basu Yi ba Banda barcin gajiyan yawon da Suka Sha kwana biyu,karfe 12:00 Lailah ta tashi barci ta shige bayi tayi wankabayan ta fito ta shafa Mai yasa wani Dan plain riga ta wuce dakin Husna Danae da ita tayi akan zasu fita,daganan daki mama ta nufa ta nemi izini,shiru mama tayi na second 2 wanna tace shikenan Amman karki Dade,da tom ta amsa tana murnan an barta,daki ta koma tayi Shirin kece raini,karfe 1:00 Suka Gama shiri Amman sai da tayi sallah kafin duk suka bar gida,suna fita gate ta Kiara shi Dan jin inda zasu hadu,"ki zo bakin titin laying ku Ina wurin" da tom ta amsa sannan ta katse kiran,iko suna kaiwa sai gashi,Husna ne tace Kai Anty motan waye ne,dungure mats Kai Lailah tayi tace yimin shiru Ni dai,komi Husna Bata Kara cewa ba Banda kalle kalle daga baya dai ta amshi wayan Lailah dataga sun Fara hira,sa'ad be yace Naga Kuna kama galan sis din mu ce,da ehhhh ta amsa mai,gaishe da Husna yayi ya mats tanbayan karatu da gida,zaga gari sukayi sossai,ya kaisu super market ya musu siyayya sossai,Husna sai zare Ido take Dan taga kayan sunyi yawa,Lailah ko rokin shi take ya bari,Dan yace su dibi abin da sukeso suka ki,shine ya Kira wata attendant,ya mats magana kasa kasa,gani kawai sukayi tana kallan dukan su biyu,suko basu San Mai ke faruwa ba,itako tana gama scanning ta Kira wata ta Gaya mata abin da zata Gaya mata sannan ta Fara diban Kaya baji ba gani,sai da suka cika baban laida na super market a kalla 15,karfe 4:30 tayi musu a bakin gate,bude musu kofa yayi suka fita sannan ya but bayan su,kayan ya fito musu da shi Lailah ko ta na fita taja hannun Husna suka nufi gate tana daga mishu hannu,hada Rai yayi yace wlh Kika wuce zai na biki da shi har parking ku wlh,chak ta tsayata juyo ta dawo in da yake,Dan tasan tsap zai it's wlh,dauka kayan suka farayi ita da Husna suka aji ye shi kusa da wani Karan flowers sake kusa da parlor,Nan suka note duka laidan,komawa tayi tamai sallama kafin suka day daya aciki Suka shiga parlor da bakin su day k da sallama,sun sami mama a parlor suka gaishe ta,suka nuna mats kayan akan su Suka siya,Amman duk a sure su ke,saki duk Suka nufa Suka wasa ruwa tare da yin sallah,da misalin karfe 11 dare ita da Husna suka fita kwaso kayan sai Wanda suke kaman barayi,a karshen ne da ta he kulle kofa be mama ta fito,tace Mai kike Yi a wajen,iko Lailah najin muryan mama cikin ta ya bada wani Kara kullllllll! Iko da mama na kusa sai ta ji Karan,samun kanta tayi da jarumtar cewa naje gyra windon daki nane,komi mama Bata ce ba ta juya daki,tana ganin mama ta shige ta tsauke ajiyar zuciya Mai karfi tare da Addu'a harda fidda huci Mai zafi daga bakin ta,kofan ta kulle sannan ta nufi dakin ta in da Husna k jiran ta,tana shiga ta datse kofan da makulli,ta matso wurin kayan,Zama yayi kan gado tana ba ma Husna labarin yanda sukayi da mama,dariya Husna tayi tace nasan kin rude Anty,aaaaaa!ba dole ba irin wannab bala'in da aka hadani da shi,raba kayan sukayi,Lailah tasa nata a drawer while Husna ta nufi dakin ta da Bata ta a dana shi,Asuba ta garu yaran mama.
YOU ARE READING
💞💞💞LAILAH💞💞💞(COMPLETE)
RomanceWallahi ko zaka mutu bazan taba auren kaba yaya Abba na tsaneka na tsani duk mai sonka, "ni sa'ad nakeso kuma shi zan aura" ta karasa fada tana fashewa da wani irin matsanancin kuka mai taba zuciya. Daddy daya shigo parlorn ya Daka mata tsawa "wlh...