💞💞💞LAILAH💞💞💞
STORY AND WRITTEN BY
AISHA MA'ARUF
GIMBIYA AYSHU💞💞💞ELEGANT ONLINE WRITER'S📚
PAGE 23-24
_____________________Ni dai sake ni,mai haka?.
"Friend wlh you are in love",ya fada tare da fashewa da dariyar dake kular da abokin zance.
Wani mugun kallo ya aika mai da shi yana kada kai ya ce"kana hauka,ni fall in love,mtswwwww!,you must be stupid for saying that,Let go pls",ya fada tare da mikewa tsaye.
Bin shi da ido Hydar ya yi baki bude,shi da ya zata abokin shi ya fada soyayya ashe bai masan mai yake ba,tabdi akwai aiki ja.
"Am going,what are u think of?".
"Nooo nothing let go".
"Amman friend maganan gaskiya kana san yarinyar nan,kuma irin sosai dinnan,kawai ka bayyana mata a wuce wurin".
Tunda ya fara magana Sa'ad ya hade girar sama da kasa,wani mugun kallo yake bin shi da shi,bayan ya gama maganar ya fice daga parlor.
Bin shi a baya Hydar ya yi suka nufi parlor ummi ba tare da ya kuma ce mishi komi ba,babu kowa a parlor sai karan tv daya karade parlor,wuri Sa'ad ya naima ya zauna fuskar shi a hade,dakin Ummi Hydar ya nufa ya shiga bayan ya yi sallama kuma an ba shi izinin shiga,zama ya yi kusa da ita ya ce"Ummi Sa'ad zai wuce".
"Okh ina zuwa,yanzun zan sauko".
"Toh shikenan Ummi",ya fada tare da mikewa ya fice daga dakin.
Bayan ta gama azkar ta sauko hannun ta rike da laida,zama ta yi a daya daga cikin kujerun ta ce"son har za ka tafi?".
Murmushi Sa'ad ya yi ya ce"ehh! Ummi".
Toh ka gaishe min da Mummy ka,ta fada tare da mika mishi laidan hannun ta ya kai mata,godiya Sa'ad ya yi mata sosai ya juya zai tafi ta ce"zo nan,amshi wannan kasa mai ba yawa",girgiza Kai Sa'ad ya yi ya ce"nagode Ummi".
Hararar shi Ummi ta yi ta ce"ina wasa da kai ne?,maza amsa kafin ranka ya baci".
"Hannu biyu Sa'ad yasa ya amsa yana murmushi ya yi mata godiya sannan suka fice daga parlor".
Murmushi Hydar ya yi ya ce"NI DA DALIBATA",ko kaki ko kaso kana san yarinyar nan,sabida haka tun wuri ka yi gaggawar sanar mata kafin wani yama kafa,ya fada tare da juyawa da sauri yana dariya ya bar wurin yana daga mai hannu ya ce"Allah ya kiyaye hanya"NI DA DALIBATA".
Kwafa Sa'ad ya yi ya ja kofar motar shi,sai da yayi warming din shi sannan ya ja ya fice daga gidan,a hanyyar shi ta komawa gida ya tsaya a wani masallaci dake bakin hanya ya yi sallah kafin ya wuce gida,horn ya yi mai gadi ya bude mai ya shiga,parking ya yi a parking space ya fito da wayoyin shi da Ledan da Ummi ta bashi ya kulle motar,direct parlor Mummy ya nufa ya shiga da sallama,a parlor ya same ta tana kallo,zama ya yi kusa da ita ya ce"washhh! na gaji Mummy,ina wuni ya gida?".
"Lafiya lau son,fatan an dawo lafiya,ya ka baro su?".
"Lafiya kalau Alhamdullah,ta ce ma na gaishe ki kuma ta bani wannan na baki",ya fada tare da mika mata laidan dake hannun shi yana fadin har kyautar 10k ta bani wai nasa mai.
Allah sarki Allah ya anfana ya bar zumunci,Hajiya Khadijat ba dai kirki ba,bata gajiya da dawainiya,maza je ka watsa ruwa ka huta,naga kaman ka gaji.
Wlh kuwa Mummy,sai da safe Allah ya tashe mu Ameen,bai zarce ko ina ba sai part din shi,bai tsaya parlor ba ya wuce bedroom,ajiye wayar shi da car key ya yi ya fara cire kayan jikin shi ya saura daga shi sai short,bayi ya shiga,bayan minti goma ya fito daure da towel,da sauri ya karasa gun wayar shi dake ta famar ruri,dagawa ya yi ya saka a kunne ba tare daya ce komi ba,dariya Hydar ya yi ya ce"NI DA DALIBA TA,ka isa lafiya?".
Wani dogon tsaki Sa'ad yaja ya ce"wlh zan maka rashin mutunci".
Ni dai ba wannan yasa na kira ka ba,fatan ka isa lafiya?,kai tsaye Ya ce"lafiya lau kaman an mai dole".
"Toh shikenan a huta gajiya Angon Khadija",ya fada tare da fashewa da dariya ya katse kiran.
Kwafa Sa'ad ya yi ya ce"zan yi maganin ka yaro,da ni kake zance".
Zama ya yi gefen gado yana sauke ajiyar zuciya,knocking din daya jiyo ne yasa shi mikewa ya nufi bakin kofar,barka da dare Alhaji karami,Mummy ta ce a kawo maka.
Amsar basket din ya yi ya ce"nagode sosai mu kwana lafiya,ya fada tare da kulle kofar ya wuce dining table da basket din ya ajiye ya shiga kitchen,plate da cup da spoon ya dauriye ya fito,shinkafa ne da stew sai pepper soup,pepper soup din kawai yasa a plate kadan,bayan ya gama ci ya kwashi plate din ya kai kitchen ya wanke,bayan ya gama shiryawa cikin kayan barci ya dau basket din ya miyar part din mummy,bayan ya dawo ya kulle kofar parlor shi sannan ya kashe kayan wutan parlor kafin ya nufi bedroom,laptop din shi ya dauka ya jingina da gado yana operating sai tunanin khadija ya fado mai,tuna abinda Hydra ya fada dazun ya yi,wai yana San ta,"how could that be possible,that can never be possible,ni ba San ta nake ba",wani bangare na zuciyar shi ta ce"toh in ba San ta kake ba mai kake,ita Kadai fah kake tunowa fahhh!,kuma kaga yarinyar na da hankali,kawai ka yarda kana San ta,ka bayyana mata a wuce wurin".
Allah ya kiyaye ni kam ba Santa nake ba,taya ma za'ayi nace ina san wata mace,tabdi da sake,cigaba da operating laptop din dake gaban shi ya yi amman tunanin yaki barin shi,hakan yasa ya kulle ya kashe wutan dakin ya bar dim light,kwantawa ya yi yaja blanket ya kwanta yana ta tunanin daya fara zame mai jiki har barci ya dauke shi........
A bangaren Lailah kuwa tana shiga gate din gidan su ta hango driver,ya ce" yanzu zanje daukoki sai gaki,dayar motar ba gyaran yanzu bane"
"Ehhh! wlh an rage min hanyya ne".
"Toh shikenan Hajiya karama a huta gajiya".
Murmushi ta yi ta ce"nagode malam kabir".
"Ba komi Hajiya ni keda godiya".
A parlor ta iske Mama tana kallon Sunna Tv,dagowa Mama ta yi ta ce"waya kawo ki?,naga kabir bai tafi ba tukunna","eh Mama na bi abin hawa ne sabida tun dazu muka tashi kuma driver ya ce"mota ya yi faci,yanzu ma wata yazo daukawa ya dauko ni sai muka hadu a tsakar gida".
Shine bai gaya min ba,kudin dake ajiye a gefen ta ta cire dubu daya a ciki ta ce"gashi ki bashi".
Amsa ta yi hannun ta na rawa,bayan ta dawo ta wuce daki a daburce,jikin ta duk rawa yake,kayan jikin ta ta cire ta fada bayi ta yi wanka sannan ta daura da alwala,bayan ta fito ta saka dogon riga ba tare da ta shafa mai ba,hijabi ta saka ta yi sallah,bayan ta idar ta yi Addu'a ta shirya ta wuce parlor ta ci abinci,Husna ce ta ce"Anty Lailah mun gama exams yau harma an bamu hutu,murmushi Lailah ta yi ta ce"nima yau muka gama tamu".
Yauwa shikenan,kinga sai muje gidan su Anty twins,kallon ta kawai Lailah ta yi ba tare da ta ce komi ba,Mama na jin su amman bata tanka su ba,bayan an yi sallar Isha'i suka ci abinci,bayan sun Kammala Daddy ya ce"tunda sun gama exam a tare za suje ma yayana hutu na kwana biyu,dadi ne ya kama Husna har ta kasa boyewa,Lailah ko ido ta kurawa Tv ba tare da ta ce komi ba,goma na yi duk aka watse.........................................
COMMENT
AND
SHARE
BY GIMBIYA AYSHU💞💞💞.
YOU ARE READING
💞💞💞LAILAH💞💞💞(COMPLETE)
RomanceWallahi ko zaka mutu bazan taba auren kaba yaya Abba na tsaneka na tsani duk mai sonka, "ni sa'ad nakeso kuma shi zan aura" ta karasa fada tana fashewa da wani irin matsanancin kuka mai taba zuciya. Daddy daya shigo parlorn ya Daka mata tsawa "wlh...