PART 25-26

129 23 0
                                    

💞💞💞LAILAH💞💞💞

STORY AND WRITTEN BY

AISHA MA'ARUF
GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

*Gimbiya Ayshu's Data service*

*Ku siya data a garabasa*

*MTN*

750 -230
1GB -280
1.5GB - 380
3GB - 720
6GB - 2200
10GB - 3700

*AIRTEL*

750 -230
1GB -280
1.5GB - 380
3GB - 720
6GB - 2200
10GB - 3700.

*GLO*

750 -230
1GB -280
1.5GB - 380
3GB - 720
6GB - 2200
10GB - 3700.

*9MOBILE*

750 -230
1GB -280
1.5GB - 380
3GB - 720
6GB - 2200
10GB - 3700.

Account number:8036434941

Account name: Maryam Maaruf Muhammad

Bank name:Opay

*Contact me on this number:08076119294*

PAGE 25-26

____________________Washe gari juma'a tun karfe goma suka gama shiri Daddy ya kaisu gidan yayan shi kafin ya wuce aiki,Mummy na jin kewan yaranta amman ba yanda ta iya,dole su sada zumunci.

Bayan Daddy ya ajiye su ya wuce ba tare da ya shiga ciki ba,parlor suka shiga da murnan su,da gudu suka nufi Mum dake zaune a daya daga cikin kujerun parlor suka rungume ta,Mum na dariya ta ce"suwa nake gani haka?".

Husna na dariya ta ce"mune Mum,munzo miki hutu ne".

"Nako ji dadi,amman kunbar Maman ku ita kadai da kadaici".

I kwana two kwai za muyi Mum cewar Lailah,"i ba komi,a hakan ma nagode,ku kai kayan ku dakin su twins sai kuzo ku yi break".

Toh Mum amman mun yi break kafin muzo.

"Toh shikenan".

Bayan sun dawo suka yada zango a parlor,zama suka yi suka sa Mum a tsakiya suna hira,dama Mum ba tada masala she's so simple shi yasa suke mugun sonta da son zuwa wurin ta,suna cikin hira suka jiyo sallaman twins,suna shiga Lailah suka fara hangowa,da gudu suka yi kansu,ko takan Mum basu biba,sai da suka gama murnan su kafin suka gaida Mum ta ce"sai yanzu kuka ganni",dariya duk suka yi harda su Lailah.

"Ba haka bane Mum wlh muna murnan zuwan su Any Lailah ne".

"Toh shikenan kuje ku watsa ruwa asr ya kusa".

Daya saura minti 10 Mum da su Lailah suka nufi upstairs dan yin sallah.

Zaune suke a parlor bayan sallar la'asar suna hira Yaya Abba ya shigo da sallama,Lailah na ganin shi ta dauke kai.

Wuri ya naima ya zauna ya ce"Mum ya gidi?",ya fada yana Satan kallon Lailah,hada baki su Husna suka yi suka gaishe shi Lailah ta yi karshe,dagowa yayi ya kalleta kafin ya amsa.

Tana ganin sun hada ido ta dauke kai,a zuciyar tako cewa tayi maye ya dawo,yanzu zai ishe ni da kallo,mtswwwww.

"Bari nayi fresh up Mum".

"Okh son saika fito".

Part din shi ya wuce,bayan fitar shi Lailah ta sake suka cigaba da hira.

Bedroom din shi ya nufa,wani irin farin ciki kawai yake ji,ajiye laptop bag din shi yayi ya cire kayan jikin shi ya saura daga shi sai boxers da singlet,bathroom ya shiga,bayan kaman minti sha biyar ya fito daure da towel daure a waist din shi da wani a hannun Shi yana goge gashin kan shi,bayan ya gama ya shafa lotion,wani T-shirt ya dauko sky blue an rubuta life is wonderful da wando jeans neavy blue da short da singlet,shiryawa ya yi shap-shap,ya yi kyau sossai,dressing mirror ya nufa ya fesa turare sosai,tsayawa ya yi a jikin madubi yana kallon kan shi yana murmushi,agogo yasa kafin ya nufi hanyyan kofar,main parlor gidan ya nufa ya shiga da sallama.

Lailah na jin sallamar shi ta ce"na shiga uku nikam",zama yayi a one sitter dake facing Lailah.

Lailah dan sawa yayan ku abinci.

Tashi ta yi ta nufi kitchen ranta bai so ba.

Binta ya yi da kallo a fakaice,bazaka taba sanin ita yake karewa kallo ba,bayan ta kawo abincin ta aje a kan center table,har ta juya zata tafi ya ce"zuba min".

Juyowa ta yi ta fara serving din shi sannan tasa mai drink da ruwa a cup ta koma mazauninta,5:15 ta tashi ta ce"Mum bari nayi mana girki".

Okh duk ku tashi ku bita,6:39pm suka kammala komi har wanke-wanke,fito da coolers din suka yi aka jera a dining,daki duk suka nufa dan su watsa ruwa,bayan duk sun yi sallah suka sauko parlor,suna nan zaune har takwas amman Daddy bai shigo ba,Lailah ce ta ce"Mum ina Daddy yake?".


"Yaje Abuja yau da safe".

"Yaushe zai dawo?".

"Maybe tommorow bayan sallar isha'i insha Allahu".

Dining suka nufa,Abba ya zauna a kujeran dake facing dinta,suna cikin cin abinci muhammad ya ce"gaskiya abincin nan ya yi dadi,daga jin dandanon shi nasan ba su oo suka yi shi ba",ya fada tare da kallan su Raihan ta kasan ido,duka Raihan ta kawo mai ya doje,dariya duk suka fashe da shi,twins ko sai hararan shi suke,oga Abba ko sai Satan kallon mutuniyar yake,duk wani motsin ta a kan idan shi ne,hakan yasa ta kasa sakewa taci abinci sosai.

Bayan sun gama suka kwashi komi zuwa kitchen,Ramlat da Husna suka yi wanke-wanke sauran suka yi parlor,daukar wayar ta Lailah ta yi tana latsawa,ji take kamar ta fasa kara tsabar takaici,ita a duniya ta tsani yawan kallo,sai wuraran sha daya na dare duk suka watse,Abba bai so ba amman babu yanda ya iya.

A bangaren Sa'ad kuwa Washe gari karfe biyar dai-dai ya tashi a barci,bathroom ya shiga ya yi wanka da alwala sharp-sharp dan ya kusa makara,bakin jallabiya yasa da farin hula sannan ya fesa ya wuce masallaci...........................................




Ku yi hakuri da wannan,bazan ringa posting kullun ba sai randa ya samu saboda makaranta.

COMMENT

AND

SHARE

FISABILILAH

BY GIMBIYA AYSHU💞💞💞.

💞💞💞LAILAH💞💞💞(COMPLETE) Where stories live. Discover now