💞💞💞LAILAH💞💞💞
STORY AND WRITTEN BY
AISHA MA'ARUF
GIMBIYA AUSHU💞💞💞ELEGANT ONLINE WRITER'S📚
PAGE 21-22
_________________Direct daki ya shiga bai tsaya parlor ba ya shiga bedroom,jakan shi ya ajiye ya zauna saman gado ya rike kan shi,shi dai changes din da yake ji this days na damun shi,bai san mai yasa yake jin changes in yaga yarinyar ko kuma suna tare ba,tashi ya yi ya cire kayan jikin shi ya shiga wanka,bayan minti goma ya fito daure da towel,gashin kirjin shi da ruwa ya jika su sun kwanta luf-luf gwanin ban sha'awa,share ruwan kan shi ya yi ya busar sannan ya shafa mai,ya yi kyau sosai Kaman balarabe,kujera ya ja ya zauna sannan ya fara shafa lotion din shi a lallausar fatar shi mai kama dana mace,bayan ya gama ya nufi drawer yana takawa daddaya Kaman bai so,wani hadaddan jeans ya ciro kalan blue,farin boxers da singlet sannan ya dauko farin T-shirt an rubuta Handsome a jikin shi,ajewa ya yi saman gado ya nufi dressing mirror ya fesa turare sossai,sai kamshi ke tashi Kaman anyi barin turare a dakin,shiryawa ya yi cikin kayan daya ciro,zo kuga yanda ya fito a kayan nan,a raina na ce"amman Mummy ta iya haihuwa,he look's handsome,ya hadu 100%",turare ya Kara fesawa sannan ya dau wayan shi da car key,parlor ya nufa ya shiga da sallama.
Mummy dake ta jiran dawowar shi ne ta ce"haba son,daga cewa za kaje ka dawo shi ne sai yanzu,wannan wankar fahh! sai ina,ko dai ko dai",ta karasa maganar ta tana dage mai gira.
Hade rai ya yi ya ce"kai mummy! wurin Hydar fa zani".
"Fada gaskiya dai",ta fada tana rike dariyar dake kokarin kufce mata.
"Haba mummy kema dai kin san halina,ni dai na tafi sai na dawo",ya fada yana hade rai.
"Toh a dawo lfy Allah ya tsare,idan kaje kace Ina gaishe ta,ta fada tare da fashewa da dariya ganin yanda yake ta cika yana batsewa".
Turo baki kawai ya yi tare da kankance ido daya ya ce"Ameen mummy na love you,ni dai Mummy wurin Hydar zani,banda budurwa fahhh".ya fada tare da ficewa.
"Mummy na dariya ta ce"love u too my son".
Bai zarce ko ina ba sai gidan su Hydar,yana isa yayi horn a bakin gate,lekowa mai gadi ya yi yaga shi ne,da sauri ya bude kofar ganin babban abokin dan gidan ne,parking ya yi ya kira Hydar din a waya,bayan ya daga ya ce"hello man ina kake?".
"Ina gida".
"Okh gani a compound"."Wani compound",ya fada fuskar shi dauke da mamaki.
Hade rai Sa'ad ya yi ya ce" ban san raini,ka fito kar ka bata min lokaci",ya fada tare da katse wayar.
Hydar na fitowa ya hango motar sa'ad,da sauri ya nufe shi ya ce "shege man,ashe dai da gaske ka ke,shi yasa naga gari da hadari,ashe duk dan kai ne,ya fada yana dariya.
Kokarin rufe murfin motar shi yake,da sauri Hydar ya rike kofar ya ce"daga wasa,dan Allah ka bari,kai na bisa wiya,a yi hakuri shalelen Mummy,yan zun dai mu shiga ciki ya fada yana jan hannun shi.
"Toh tsaya ni kam kar ka tuge min hannu na shiga uku".
"Dariya Hydar ya yi har da rike ciki",daukan wayoyin shi ya yi ya fito ya kulle motar.
Jerawa suka yi,suna tafiya Hydar ya ce"man mai ke damun ka ne?",ya fada tare da kure shi da ido.
Cikin dakiya Sa'ad ya ce"mai ka gani".
"A,a ba komi".
"No is not true,gaya min".
"Na ce ba komi",dai-dai nan suka isa kofar parlor,Hydar ne ya fara shiga da sallama sannan Sa'ad yabi bayan shi,Hajiya dake zaune a parlor ta ce"wa nake gani haka",ta fada hannun ta rike da habar ta.
YOU ARE READING
💞💞💞LAILAH💞💞💞(COMPLETE)
RomanceWallahi ko zaka mutu bazan taba auren kaba yaya Abba na tsaneka na tsani duk mai sonka, "ni sa'ad nakeso kuma shi zan aura" ta karasa fada tana fashewa da wani irin matsanancin kuka mai taba zuciya. Daddy daya shigo parlorn ya Daka mata tsawa "wlh...