PAGE 67-68

117 20 1
                                    

💞💞💞LAILAH💞💞💞

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU 💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚

HAPPY RAMADAN MUBARAK TO ALL MUSLIM UMMAH. ALLAH YA SA MUNA CIKIN ENTATTUN BAYI,ALLAH YA SADA MU DA ALKAIRIN DAKE CIKIN WANNAN WATAN MAI ALBARKA.AMEEEEEEEN 🤲🤲🤲.


WANNAN PAGE DIN SADAUKARWA NE GA MASOYA LITTAFIN NAN LAILAH♥️♥️♥️


PAGE 67-68

________________________Bayan ya raka a Nolan shi ya dawo ya kulle kofa sannan ya kashe wutan parlor har na kitchen.Dakin da take ya nufa Yana shiga ya iske Bata dakin,alamun tsaukan ruwan da ya jiyo daga bayi ne yasa shi fahimtan tana ciki,kullo kofan yayi sannan ya nufi nashi dakin,bayan musalin minti 30 ya dawo in da ya samu wutan dakin a kashe,kunna wutan yayi ya gan ta kwance akan gado ta rufe kanta da bargo har kanta Bata Bari a waje ba, kashe wutan yayi sannan ya taka sannu a hankali ya nufi in da take,hannu yasa ya tada ta,banza tamai kaman tana barci,Kara taba ta yayi Amman shiru,hannu yasa zai yaye bargon jikin ta,tsaurin rike bargon tayi ta amsa da ummmmmm......... Murmushi yayi sannan yace ki tashi kiyi Alwala turo Baki tayi kafin tace nayi sallah,ehhhh!nasani k dai taso,kunkuni ta fara yi kasa kasa Bata bari yaji ba,sai da ta shafe minti 10 kafin ta mike da bargo a jikin ta shiko Yana tsaye komi baice Mata ba,dama ta ajiye hijabin ta a kan bed side din ta hannu kawai tasa zata dauka sai ya riga ta dauka,iko tana lalabawa taji Babu tayi tsaurin bude fuskan ta,taga da gaske Babu,a zuciyar ta tace toh waya dauka ko ban ajiye bane,a'a na ajiye kafin na kwanta bayan na idar da shafa'i da wuri,ko dai shi ya dauka, dagowa tayi a hankali ta kalle shi I ko taga hijabin a hannun shi,haba!, Haba meh kinyi mamaki ne,rike Baki tayi tace wai Dan ita Bata masan maganan ya fito ba,toh ki tashi ki je kiyi Alwala,da toh ta amsa Mai sannan tace toh Miko min hijabi na,tana Miko Mai hannun ta,harda yaso Kar ya Bata ko Mai ya tuna oho sai kawai ya Mika mata,amsa tayi ta warware sannan ta saka kafin ta cire bargon jikin ta,ta shi tayi ta shige bayi tana murguda Baki, murmushi kawai Abba yake Dan duk abin da take Bai bashi haushi Asali ma Kara kyau take mishi da sa shi nishadi.bayan ta fito daga bandaki ta nufi inda ya shinfida darduma ta tsaya,juyawa yayi ya tayar da sallah,bayan sun idar ya Kama kanta tayi Mata Addu'oi sossai sannan ya Fara Mata tambayoyi,kumbure kumbure take tana bashi amsa sai wani hura hanci take,shiko Yana same da ita Amman yayi Mata banza,ta shi yayi ya dauko Kazan dake saman fridge din dake dakin ta ya ajiye a gaban ta,kallan ta yayi sannan yace je ki dauko Mana plate,dagowa tayi ta kalle shi,har zatayi mutsu ko Mai ta tuna oho,mikewa tayi ta fita a dakin,bayan ta fita daga dakin tsauka kasa tayi ta Fara bire duk kofan da ta gani Dan gaskiya Bata San wanne ne kitchen ba,ta bude kofa uku a cikin kofofi 6 data gani a down stairs,tsayawa tayi tasa hannu a kwankwaso,tana kallon duka kofofin,ji kawai tayi an taba ta ta baya,razana tayi zatayi ihu yayi tsaurin rikota ya rungume ta,rike shi tayi sossai Dan ta tsorata,tsabida Bata ji zuwan shi ba,bayan kaman minti 5 ya cire ta daga jikin shi,hannun ta ya Kama ya jata zuwa kitchen din,shiga sukayi a tare Suka dau abin bukata sannan Suka koma daki,ajiye try da plate din sukayi,Abba ne yayi serving din su Dan tasan Lailah bazata yi ba,bayan yasa ya ce ta ci,kin ci tayi,shiru yayi Yana kallon ta,sai da ya mai-mai ta Mata tsau uku kafin tasa hannu ta Fara Dan tsakura,ko Rabin mama Bata ciba ta cire hannu,kallan ta Abba yayi yace ya Kika cire hannu,"na koshi"kallan ta yayi yace Mai Kika ci,"girgiza mishi Kai tayi alamun Babu komi,tashi yayi ya dawo kusa da ita,Yana Zama kusa da ita gaban ta ya Fara bugun 9-9 hannu yasa ya rike ta ya kwantar da kanta kan kadadan shi sannan ya Fara Bata Naman a baki,kamshi tularan shi da ta Shaka ne yayi Mata Dadi har ta Fara amsan Kazan Bata sani ba,haka ya dinga Bata har taci sossai,5Alive ya Bata tasha sannan ya Bata ruwa bayan ta Sha ya dau tissue ya share Mata bakin ta,jinginar da ita yayi da jikin shi sannan ya Fara ci shima,Bai wani ci dayawa ba ya kulle kazan,cire kanta yayi a jikin shoulder din shi sannan ya tashi ya saka tsauran Kazan a fridge,kafin ya Kai kwanon da aka Bata kitchen ya dauriye su sannan ya dawo dakin,ko days dawo samun ta yayi a gado ta lullube da bargo,shiga yayi ya kashe wutan dakin dama already yayi Shirin barcin shi.takawa ya farayi a hankali har ya karaso bakin gadon,"Lailah ko tun daya bude kofan kirjin ta ya Fara luguden tara tara har zuwa zaman shi a gefen gado,ko motsi batayi ba Dan Kar ya gane batayi barci ba".Bayan ya Gama abin da zai yi ya kwanta akan gado sannan ya ja bargo,bayan kaman minti 30 barci ya kasa daukan shi haka dai yayi ta tunani daga baya dai ya Dan matsa kusa da ita kadan gap din dake tsakanin su bai da yawa,tunanin yanda zai to yake chan dai yayi jarumtar juyo ta sannan ya rungume,"dama Lailah barci bawai nauyi yayi ba,Dan a tsorace take".tana jin ya juya ta ta bude Baki zata sandara ihu yayi tsaurin yaushe mata Baki da nashi,tuni wutar nepan ta ya dauke,mukus tayi jikin ta sai kyarma yake,sai da ya shafe minti 15 Yana Abu daya kafin ya tsake ta,tapin bayan ta yake Yana Mata gagana a kunne,Ni dai banji Mai akace ba,gani kawai nayi ta natsu,haka dai ya dinga Mata har barci ya dauke su,washe gari Abba ne ya Fara tashi bayan ya Yi Alwala ya dawo ya tashe ta sannan ya fita masallaci,ko daya dawo masallaci samun ta yayi kwance a kan  darduma hakan me ya tabbatar mishi da tayi sallah Dan Bai tsaya har ta tashi ba tsabida ya kusa makara a masallaci,Yana zuwa ya zunkuce sai kan gado,tana jin an dauke ta ta firgita,kwantar da ita yayi a jikin shi sannan yace k nine, kina da shegen tsoro dayawa,komai Bata ce mishi ba,kwantar da ita yayi akan gado,Aiko tana kwantawa ta gyara kwanciya ta ja bargo ta rufe jikin ta sannan ta cigaba da barcin ta,ba ita ta tashi ba sai karfe 9 da minti 20,ko da ta tashi bayi ta shiga tayi wanka da brush,fitowa tayi daga ita sai towel dai dai Rabin cinya,ko Rabin ma Bai ida kaiwa ba,dude kofan tayi ta nufi gurin dressing mirror ta Fara shafa Mai,tazo zata shafa a jiki sai tasa hannu zata kwance towel sai jikin ta ya Bata kaman akwai Wanda ke kallon ta,Aiko tana juyawa taga Abba a tsaye kusa da kofa,haba tana ganin shi tayi tsaurin durkusawa,shiko murmushi yayi sannan ya Fara takawa a hankali har ya karaso inda take,ya na zuwa yasa hannu zai daga ta,dunkule jikin ta tayi Taki tsaki,yunkurin dagata Kuma yayi Aiko ta saki kuka tana rokon shi daya kyale ta,Yana ganin tana kuka ya tsaki Baki Yana kallon ta,sannan yace Mai na Miki,girgiza mishi kai tayi,kallan ta yake sannan yace na fita kike nufi,daga mishi Kai tayi da tsauri, murmushi yayi ya shafi gemun shi tare da tsosa kan shi ya fita a dakin,raka shi tayi da harara bayan ya fita tace Dan rainin wayyo mutun zai shigan ma daki ba sallama tsaki ta ja sannan ta mike ta Isa shafa manta kafin ta Nemo Kaya.

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya inda a yanzu sun kwashe wata 2 Amman haryan zu ba abin da ya shiga tsakanin su,sai dai akwai Dan fahimta akan da.

A bangaren Sa'ad ko Allhah yasa soyayya Lailah ya dan yi tsauki a zuciyar shi dan har give Yana tuna ta,gidan su ko an matsa Mai ya kawo Mata inda shi bai da ma wacce zai gabatar a matsayin wacce zai Aura.

Yau Wednesday inda Sa'ad k da lecture karfe 2 na rana,tun karfe 1:30 yake makaranta inda 2 dai-dai ya shiga aji Aiko Yana shiga en class din ba sufi su 40 ba out of 110 student,Aiko Yana Gama lecture ya ce a tanka paper za'ayi test,da tanka paper da koman su duk a cikin minti biyar a kayi,in ka rubuta oho in ma bakayi ba oho,iko sai da yabi duka desk din ya kwashe papers din Bayan ya sa duk sun daga hannu sama, Mika ma Aisha yayi sannan yace ta bishi da papers din,amsa tayi ba Dan ranta yaso ba ta bishi zuwa office,yana ta fiya tana binshi a baya da yake Bata da tsauri har ya Kai Bata Kai ba,sai Bayan minti 3 kafun ta karaso,sallama tayi a bakin kofan a kalla yayi tsau biyar kafin ya Bata izinin shiga,bayan ta shiga ta Kara gaishe shi sannanta ajiye mishi papers din zata koma,kiran ta yayi yace tazo ta zauna,bayan ta zauna ya yace kwanakin baya kin gabatar da soyayar ki a gate Ni haka ne ki ba haka bane,daga mishi Kai tayi alamun haka ne duk kunyya ya kamata,toh yanzu in bazaki damu ba zan so ki ban dama na nemi izini a gidan ku,dagowa tayi ta kalle shi da tsauri,suna hada Ido kobta tsaukar da Bata kasa,hawaye be ya taru a idan ta Amman Bata Bari ya fito ba,"kina jina kuwa",girgiza mishi Kai tayi alaman ehhhh!.Toh ki ban Address Yana miko Mata paper,amsa tayi kanta a kasa ta rubuta sannan ta Mika mishi,amsa yayi ya duba sannan ya kalle ta yace zan iya zuwa yau,Abban ki na gida,shiru tayi Bata ce komai ba,"tanbayan ki fa nake ya fada ranshi a Dan hade Amman Bai Bari ya sani ba"daga mishi Kai tayi Alamun ehhhhh! Sannan ta tashi zata fita a dakin,Kiran ta yayi,tsayawa tayi a inda take taba jiran ya Fadi abin da zai ce,Baki bani number ba,Kuma bansan abin ya dau lokaci inasan Nan da 1 month ayi komai in ba damuwa,tsaurin juyowa tayi ta kalle shi Dan Jin abin da yace,suna hada Ido ta tsaukar da Bata Dan bazata iya jure kallan idan shi ba,tafiya take kaman kwai ya fashe Mata a ciki,daukan biro tayi ta rubuta number sannan ta ajiye ta juya tana Allah Allah Kar ya kirata,aiko ta cu sa'a Bai kirata ba har ta fita,tana kulle office din ta jingina da kofan tana tsauke ajiyar zuciya,hawaye ne k tsauka daga idan ta sai Jan majina take,ta shafe minti 3 a tsaye kafin tasa kasan nayafin ta ta share hawayen ta ta gyara fuskan ta sannan ta bar wurin.



Bayan Aisha ta Kai gida sai zukkumi da tunani take,Allah yasa dadyn ta ya yarda Dan yace Bai Mata Sure har sai ta kammala karatun ta,tun da ta dawo ta kasa cin abinci,mummy tayi tanbayar duniyan Nan Amman amsan dayane Babu komi,haha dai mummy ta zuba Mata Ido.

Karfe 9 dai-dai yayi ma Sa'ad a kofan gidan su Aisha,horn yayi Mai gadi ya leko yana dubawa ganin Bai San shi ba yasa ya karaso Suka gaisa,bayani Sa'ad yayi Mai sannan maigadi ya Mai sannu da zuwa,komawa yayi ya bude mishi gate cilla hancin motan shi yayi a cikin gidan,tsaurin karasowa Mai gadi yayi yace Bari nayi mishi magana,dama Aisha na tsaye a wurin window dakin ta Wanda ake it's ganin abinda k faruwa a tsakar gidan,tana ganin shi gaban ta ya bada dummmmm! Cikin ta kohhhh! Ya amsa da kulllllllllll!....................

LUV U MY FANZ♥️♥️♥️

COMMENT AND SHARE

BY GIMBIYA AYSHU 💞💞💞

💞💞💞LAILAH💞💞💞(COMPLETE) Where stories live. Discover now