Page 3-4

239 26 1
                                    

💞💞💞LAILAH💞💞💞

STORY AND WRITTEN BY

AISHA MA'ARUF (GIMBIYA AYSHU)

ELEGANT ONLINE WRITERS

page 3-4

___________Washe gari taka sance Monday Ana hada hadan zuwa school husna tana ss2 while lailah ma na shirin makaranta dan tana da lectures ranan kuma na safa ne,sauri take dan kar tayi latti malamin da suke dashi bai daukan raini inya rigaka shiga lecture hall to ba zaka shiga ba kuma ba'a surutu ajin shi,Lailah na gamawa taje dakin mama ta anso kudi tayi mata sallama taje wurin driver ya kaita school acikin 20min suka isa saboda gudun da driver yayi,yana ajeta ya juya,ita kuma tayi tsauri ta shige lecture hall tana shiga da 2min sai ga lecturer din su ya shigo Dr sa'ad muhammad Aliyu kenan dan matashi mai jida kudi,aji,kyau,nasaba,miskilibne na karshe,na bugawa a jarida ba'a gane gaban shi balle bayan shi,Mommy ce kawai ke iyawa dashi itama sai tayi da gaske wani sa'in.

Yawancin student din makarantar na mutuwar son shi,wasu na gayamai,ko kallo basu ishe shiba,wasu ko sun bar ma zuciya kaman su ooo,ban dai kira suna bahh... Wasu miskilan cin shi ne ke burgesu,wasu dan kyawun shi suke san shi.

Sallama yayi kafun ya shiga suka amsa mai hadi da gaisuwa ya amsa sannan ya fara lecture,tsit kake ji,ba'a tanbaya har sai ya gamakuma daya riga ka shiga hall toh ka hakura kawai dan inka shiga ko kika shuga toh ranan zaka/zaki sha wulakanci na kin karawa.

Yana gama lecture ya fara tanbaya as usual, yace k,"juyawa Lailah tayi tana naiman inda k take",daka mata tsawa yayi yace" dake nake",tuni jikinta ya fara kyarma,tashi tayi ya jeho mata tanbaya,shiru tayi tana tunanin amsan da zata bashi,taji yace bada k nake bahhh!,"jiki na kyarma tace nice sir,amsa tanbayar ta fara yi da kwarewa,in kaji yanda take zuba turanci zaka rantse ba yar Nigeria bace,tana gama amsawa aka tafa mata ta zauna tana ajiyar zuciya",(a zuciyarta tace Allah nagode ma daka bani ikon amsawa),tanbayan wasu student yayi kafin lokacin fitan shi yayi,lokacin fitan shi nayi ya fita wani lecturer ya shiga,basu suka gama lectures ba sai 6pm,tana fita daga lecture hall ta hango driver har yazo taje ta shiga yaja mota sai gida,su na kaiwa gida ta bude kofan ta fita, tana shiga parlor taga ba kowa sai ta leka kitchen taga Mama ita kadai dan Husna na islamiya bata dawo ba,gaida Mama tayi,bayan Mama ta amsa tace mata ya gajiyan makaranta,da Alhmd Lailah ta amsa tana murmushi tace bari naje na dan watsa ruwa kafin a kira sallah,ta fada tana ficewa daga kitchen,jakarta ta rataya ta cire hijab da kayan ta ta daura towel ta shiga wanka mintin ta 10 a bayi ta fito ta sa inner wears dinta sannan tasa dogon riga ko mai bata shafa ba taje ta sami Mama a kitchen ta kama mata aiki,suna kammalawa ana
Kiran magarib,daki Mama ta nufa dan tayi sallah Lailah kuma ta tsaya jera coolers a dining area,bayan ta kammala ta haura sama dan tayi sallah,bayan ta idar tayi azkar da karatun Al-qur'an kafin ta sauko,Husna ce kawai a parlor tana kallo,wuri ta naima ta zauna suka cigaba da kallon tare suna yi suna hira jefi-jefi,suna nan zaune akayi kiran sallah isha'i,Daddy ne ya fito daga part dinshi za shi masallaci,gaida shi duk suka yi da girmamawa,amsawa yayi da kulawa yace suje suyi sallah sannan ya wuce masallaci dan anfara tayarwa,ba Daddy ya dawo ba sai 8:30,da sallama dauke a vakin shi ya shigo,amsawa duk suka yi hadi dayi mai sannu dazuwa,Mama ajiye littafin dake hannun ta tayi tace duk suje dining dama Daddy yayi gaba abun shi su Husna ne suka taso,Husna ce tayi serving dinsu,bayan sun kammala su Lailah suka kwashe kwanonin suka nufi kitchen,Mama da daddy suka nufi parlor,Husna ta tsaya wanke su Lailah kuma ta koma parlor tayi masu Daddy sai da safe akan zataje tayi karatu suna da test gobe suka ce toh Allah ya bada sa'a,da Ameen Ameen Lailah ta amsa,ta juya ta nufi dakin ta,tana shiga ta dauko littafin da zata karanta tafara baita tagama karatun ba sai 2,shima dan barci ya ci karfin ta ne,kwanciya tayi ta rufe jikin ta da bargo bayan tayi Addu'a..........

Washe gari lecture din afternoon suke dashi,kuma daya da rabi dai-dai suke da test,tana gama aikin da zatayi tazo ta cigaba da karatun ta sai wurin 12:30 ta tashi ta shiga wanka,Sha biyu da minti hamsin ta kammala shirin ta,hijab tasa ta tayar da sallah tana idarwa tayi addu'a ta mike taje ta dauko abincin ta taci,tana gamawa ta tsuri jakarta ta rike handout dinta a hannu ta fito,a parlor ta sami Mama tayi ma mama sallama har tafara tafiya mama ta ce taje ta duba dressing mirro akwai 1000 ta dauka tace to Mama ta juya ta je dakin Mama ta dauko ta dawo tayi mata sallama ta fita minti 20 ya kaisu saboda go slow dake hanyya 1:26 suka kai school har kofan hall ya ajiyeta ta sauka ta shiga ciki tanemi wuri ta zauna tafara maraja'a kafin malamin ya shigo daya da rabi dai-dai nayi ya shigo yana shiga ya fara dube dube har ya hango abinda yake nema yana ganin ta ya sauke ajiyar zuciya a boye sai yace yanzu zamu fara test are u all ready,da yes sir duk suka amsa,"yace ok",ya juya ya rubuta questions din yace a fara the test is for 30min,zagaya ajin ya fara yi yana duba student har yakai kan Lailah,tsayawa yayi yana kallon abin da take,ta amsa 3 saura daya da yake 4 questions ne,yana tsayawa akanta ta bar rubutun,yace tacigaba taki sai yayi murmushi yayi gaba.

bayan angama test din yace Lailah ta kawo office dinshi tace ok sir,ya fita,ta bishi da shi a baya,yan aji suka fara gulma,balle matan dama malamin badai kyau bah yanada fara'a sossai ga surutu amma ba sossai ba, suna isa office dinshi ya bata hayya ta shiga ya bita a baya ta ajiye books din ta juya zata koma ya kirata,khadija ta amsa da na'am yace i want to talk to u tace okh sir ya bata izinin zama ta zauna.......

Kubiyoni dan karanta cigaban labarin.

Comment and share.

💝💝💝.

💞💞💞LAILAH💞💞💞(COMPLETE) Where stories live. Discover now