Episode 01

997 57 6
                                    

*TAUFEEƘ*

NA
*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO...*✍🏻

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

'''Alhamdulillah!Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah nagode maka da ka bani ikon dawowa a karo na barkatai, Allah ka bani ikon rubuta abunda Al'umma zasu amfana dashi, ka tsare alƙalamina da rubuta sharri, Real fan's gani na sake dawowa ƙaunar da kuke nunawa book ɗina ne yasa na dawo muku tare da zazzafan littafi wanda ke ɗauke da darusa da dama, dafatan zakuci gaba da bani haɗin kai domin da bazarku nake takawa, kar na cika ku da surutu ku dai mu haɗu cikin labarin mai taken''' *TAUFEEƘ* '''wanda yazo muku da sabon salo.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🚴🏻‍♀️'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💞 Sa'eedina matuƙar gdy a gareka da gudummawar da kake bani tare da ƙarfafamin gwiwa Rabbi ya tsare min kai a duk inda kake, ya ƙara maka lafiya da nisan kwana amin ya rabbil izzati.🤲🏻'''

*Episode 01*

'''Kaduna'''

*Millonium city* anguwa ce wacce ta tara manyan attajirai masu faɗa aji a cikin Kaduna, tare da rantsartsun gida tamkar wanda aka dasasu saboda yadda tsarin gidajen anguwar yake kai kace kawai tsirowa sukayi, haka gidan *Alhaji Nasir Adam Salwa* yake shima, da sauri na ƙarasa ganin kaf anguwar gidansa yafi na kowa haɗuwa ina saka kaina kiɗa na faraji yana tashi, na babban mawaƙin nam *Justin bieber* cikin waƙarsa mai taken *Let me love you* sosai kiɗan yake tashi kai kace gidan disko ne, filin gidan na shigo wanda suke ƙayace da Flower masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali gefe guda kuwa babban compound ne mai cike da rantsartsun motoci masu matuƙar tsada da kyau guda 12 ga fili nam wanda zai iya ɗaukar fiye da 10 tsakiyan gidan zagaye yake da wasu flowers masu fidda wuta da dare ga wani ɗan rami dake fidda ruwa fari sal, abun gwanin birgewa, kamar daga sama naji wani mutum na cewa "wlh yaran nam sam basu da ta ido ku zauna ku ƙurewa mutane sauti kamar wanda kuke gidan disko. kallon inda naji maganar nayi wasu ƴan matasa ne su biyar suna zaune a wata ƴar runfar shaƙatawa amma kana kallonsu kasan masu aiki ne ɗaya ne ɗan dattijo sosai a cikinsu duk da manya ne amma ɗayan ya girmesu, dariya suka saka jin abun da Ali yace, na kusa dashi ne yace "kai dai ka bari Ali wlh lamarin Yaran yana bani haushi. Ɗan dattijon ne yace "ai ba ku kaɗai ba wlh shiyasa bana so Yallaɓai *TAUFEEƘ* ya bar gidan nam dan da yana nam sai dai kaji ƙira'a yana tashi duk da shima yana sa kiɗam amma ba irin na mahaukatan nam ba na su marigayi Shata yake sakawa duk da yana ɗan saka nasu Adamu zango.
Gaba ɗaya suka sa dariya Garba yace "Baba zancenka haka yake wlh amma kaga su *Nazmar,* *Jawaad,* *Nabeeha* sam basa ji kamar masu kunnen ƙashi in har Yallaɓai *TAUFEEƘ* baya nam to sufa sallarsu ce shiyasa nake addu'a Allah ya dawo da yallaɓan mu lfy, gaba ɗaya suka amsa da "Amin ya rabbi.
Sallau ne yace "ai baku san wani abu ba kunga wannam ɗan chakurkurin Yaron? mai sunan larabawa *Ka'aaf* ko? to wlh shima ya shiga cikinsu dan ko jiya da Mai gida ya aikeni a tsakiyansu na tsince shi yana ta tiƙar rawa. gaba ɗaya suka bushe da dariya Sani harda riƙe ciki dan kaf cikinsu ya fisu iya dariyar mugunta.😹
Wajen na barsu suna ta tsaigumin su dan nima sai da na dara dan yanayin yadda suke maganar dole ya baka dariya, nufar cikin gidan nayi wata ƙofa ce ta glass da glass gabana sai da ya faɗi ganin ina hango kaina a ciki, ƙarasa wa nayi a hankali na danna wani rame wajen handle ɗin kawai sai naga ƙofar ta buɗe wani irin sanyayan iska tare da ƙamshi naji ya bugi hanci na takawa na farayi a hankali na nufi cikin katafaren falon, Ji nayi ƙafata ta nitse a cikin wani abu mai matuƙar laushi da taushi da sauri na kalli wajen domin naji yadda ƙafata ke lumewa ba tare da nasan inda take shiga ba, wani jahilin carpet na gani mai matuƙar ɗaukar hankali ɗan madaidaici ne jikinsa ko bayan kuliya albarka tsabar laushi, ban tsinke da lamarin ba saida naga yadda tsarin falon yake, Babban falo ne sosai wanda yake Ƙayate da kayan more rayuwa masu ɗaukar hankali tsayawa faɗa muku yadda fallon yake ma ɓata lokaci ne, gefen da nake jiyo sautin ƙiɗa na kalla, masha Allah na furta domin ganin wasu wanda nake tunanin sune su *Nazmar* maza ne guda biyu sai kuma mace ɗaya wacce baza ta wuce 19 year's ba sanye take da riga iya gwiwa Pink colour wacce taɗan kamata tana da manyan na fulani wanda suke a tsaye ƙyam kamar zasu faɗo ƙasa, sanye take da wando fari sol wanda ya matuƙar matseta da kaɗan ya wuce gwiwarta doguwace amma ba sosai ba sai dai farace sol, ƙafarta sanye yake da takalmi mai tsine mai igiyoyi pink colour kayinta ba kwali sai uban tilin gashi da ya zubo mata har gadon bayanta baƙiƙƙirin a tsefe fuskarta ƴar madaidaiciya ce mai ɗauke da manyan idanu wanda yake cike da gashin ido giranta ba a cike take ba, dogon hancinta ɗauke yake da ɗan ƙaramn bakinta kallan pink sai motsi yake da alamar waƙar take bi, a duk motsinta dimple ɗinta sai sun lotsa rawa take cike da burgewa duk wani sassa na jikinta motsawa yake duk da batayi kwalliya ba amma *Nabeeha* ƙarshe ce wajen kyau dole duk namiji mai jini a jika in dai ya kalleta sai yaji wani sauyi a cikin jikinsa lokaci ɗaya zata tafi da imaninsa.

TAUFEEƘWhere stories live. Discover now