Episode 3

311 25 1
                                    

*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO...*✍🏻

*_MASOYANA DON GIRMAN ALLAH KUYI MANA SUBSCRIBE DIN WANNAN CHANNEL DOMIN SAMUN LITTAFAN SAURARE DA KOYON SANA'O'IN HANNU DA SAURANSU NAGODE👇🏻_*
https://youtube.com/channel/UCY1pIcI2DlVykTz57m6Q3TA

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💋 Sa'eed'''

*Episode 03*

*...* Ko kaɗan basu taɓa jin son Amina da ƴarta Amatullah ba, hatta ɗan uwansu Jamilun ba wai sun so shi bane tsakani da Allah ba, kawai sun so shi ne don abin da yake da shi, a lokacin da yake raye suna nunawa Amatullah so na ganin ido, amma yanxu ƙiri² suke nuna ƙiyayyarsu gareta, gida ne Babba me ɗauke da ɗakuna domin Alhaji Jamilu ya narka kuɗi sosai akan wannam gidan a tsare yake tsaf kowa ya ɗauki nasa da na iyalen sa, Allah ya taimake ta basu kama ɗakin ta ba, tun bayan bakwai bata ko leƙowa parlour'n sai dai tana jiyo hayaniyar su, Satin ta guda baci ba sha sai ruwa tuni ta fita a hayyacinta yanzu ko ruwan tasha ma harar dashi za tayi, ko salla gagararta tayi, a yanzu ma kwance take a kan sallaya tana ta maida numfashin wahala dan yanzu ta gama kela amai na zallan ruwa, Mama Baraka ne matar Baffa Gambo jin har an doshi sati ba Amatullah ba motsin ta yasa ta nufi cikin ɗakin dan ganin halin da take ciki, Mama Baraka ka tana da ɗan tausayi ba kamar sauran matan da mazajen nasu ba, domin su kam summa mance wata Amatullah sharholiyar su kawai suke yi, Mama Baraka tun da ta doshi ɗakin take jin wani tsami gabanta ne ya faɗi tace "kar dai yarinyar nam mutuwa tayi, yau da mun shiga uku.
Da sauri ta ƙarasa daɗin hango ta tayi a chan ƙasa a zube tana mai da numfashi da hanzari ta ƙarasa tana faɗin "innalillahi! Amatullah me yake damunki haka? ta isa tana kamata jikintan nam taji zafi rau, Amatullah bata iya magana ba sai ido kawai, kuka ne yaxo wa Mama Baraka tace "sannu Amatullah bari naje na samu Baffan naki yazo a kaiki asibiti. bata jira jin amsar ta ba dan tasan baza ta samu ba saboda wahalar da tasha, Mama Baraka tana zuwa ta samu duk suna falon ma, hawayenta ta share tace "Amatullah fa ba lafiya dan ko magana bata iyayi dan Allah kuzo muje a kaita asibiti kada ƴar mutane ta mutu, ta ƙarasa tana matsar ƙwalla dan gaba ɗaya tausayin yarinyar ya kamata.
Baffa Jibo ne yace "to ta mutu man ina ruwan mu ba wani asibitin da za a kaita.
"Ah toh! cewar Baffa Haruna.
Baffa Gambo yace "kin dai ji abin da Yaya ya faɗa dan haka kiyi maza ki ɓace min da gani baza a kaita asibitin ba.
Bata ƙara magana ba ta juya ta nufi ɗakinta dan tasan iya gaskiyar su suka faɗa baza su kaitan ba, fita tayi ta samu mai gadi tace maza yaje ya sayo mata maganin zazzaɓi da ciwon kai, dan tasan bazai wuce su suke damun Amatullah ba da kuma rashin abinci, amsa yayi ita kuma ta dawo direct ɗakin Amatullah ta koma a yadda ta barta haka ta sameta, taimaka mata tayi ta shiga toilet ta haɗa mata ruwa tace tayi wanka, ba musu kuwa ta ɗaga kai dan dama tana buƙatar me taimakon ta, kafin ta fito Mama Baraka ta gyara ɗakin yayi fes ta ɗauko mata kaya, bayan ta fito ne tace "maza ki chanza kayanki bari na kawo miki abinci, da "to" ta amsa mata shima da ƙyar dan wankan da tayi ta samu kuzarinta ya fara dawowa, kayan ta sanyi bata ko kalli in da mai yake ba ta koma gado ta kwanta, Mahaifanta ta tuna, ta tuna lokacin da in bata da lafiya gaba ɗaya suna tare da ita wannam na mata sannu wannam na bata abinci a baki a kullum suna manne da ita har ta warke basa yarda ko na second ɗaya ne ta zauna da yunwa, amma yau gashi sati na biyu ban saka abin kirki a cikina ba, wani marayan kuka ta sake a haka Mama Baraka ta dawo ta sameta hannunta ɗauke da plate Da yaƙe shaƙe da abinci wanda sai da suka kai ruwa rana da su Mama Marka da Mama Talatu akan baza ta ɗibi abincin ba in Amatullah ta matsu tazo ta girka mana, sai da ta musu da gaske sannam ta ɗiba ta fito, ajiye mata tayi tace "maza Amatullah tashi ki ci kisha magani sai ki kwanta ba musu ta miƙe dan ba ƙaramin yunwa take ji ba, tuwon shikafa ne miyar ganye da yaji tattaƙwashi da man shanu luma ta fara baji ba gani tuni taci rabin abincin, Mama Baraka kallonta kawai take cike da tausayawa, sai da ta cinye tas sannam ta miƙa mata maganin da Iro me gadi ya sayo sha tayi tasha ruwa sannam taje ta wanke hannunta ta dawo tace "Mama Baraka na gode miki sosai Allah ya saka da alheri.
"Babu komai Amatullah ki kwanta ki samu bacci Allah ya ƙara sauƙi, ta faɗa lokacin da take fita daga ɗakin.
Da "amin" ta amsa sannam ta kwanta, tana kwanciya bacci ya ɗauketa.
Cikin bacci taji an ɗira mata wani wawan duka zambar ta miƙe cike da tsoro dan dukan ya shigeta, buɗe idonta tayi Mama Marka ta gani a saman gadon ba shakka tasan ita ce ta daketa gefenta ga Mama Talatu da Baffa Jibbo Baffa Haruna Baffa Gambo da kuma Mama Baraka, mamaki ne ya cikata a zuciyarta tace "waɗan nam ko me suka zo yi ɗaki na oho.
Baffa Jibo ne yace "sannu maras kunya dan iskance ace muna gida ɗaya tsawon sati biyu baza ki fito ki gaida mu ba ko kuma ki taya matayen mu aiki ba, tsabar iskanci sai dai ki kwanta ki ta sharar bacci to maza ki buɗe kunnenki da kyau, daga yanzu ki za kiyi sharar gidan nam da girki ke dai komai ma na gidan nam ke zaki na yi in kin ƙi kuwa jikin ki zai gaya miki, tun da naga alamu kin ɗau baƙin halin uwarki, gaba ɗaya matan suka sa shewa banda Mama Baraka da tausayin yarinyar ya gama cika mata zuciya a yanzu.
Baffa Haruna yace "kinji dai abun da Yaya ya faɗa ko? ya faɗa cikin tsawa, da sauri ta buɗe baki tace "eh naji insha Allahu zan yi" ta ƙarasa maganar wani kuka na zuwan mata.
Baffa Gambo yace "kar ma kiyi mana ai na lahira sai ya fiki jin daɗi sai kin tafi inda iyayenki suka je, daga haka suka fice daga ɗakin damman saƙon da suka zo isarwa kenam gareta.
Wani marayan kuka take a fili take furta "why? Why? Why? me yasa ku ka tsaneni haka? me yasa baza ku tausaya min ba ko dan maraicin da nake ciki tashin farko a lokaci guda na rasa iyayena duka biyu me yafi wannam ƙuna, bani da wanda zai kula da lamurana, ba ni da wanda zai na sharemin kuka wayyooo Allah nah...
Tun daga wannam rana ta fara fuskantar uƙu ba da wahalar rayuwa ita ke komai na gidan duk da ga ƴan mata kamarta har ma wanda suka fita amma sam babu me taimaka mata, sai tayi ma suce bashi suke so ba dole zata koma ta sake musu abin da suke so, haka gyaran daɗi ma tana yi zasu ɓata su sake ƙiranta dole sai ta gyara, yanzu ma tsaye take a kitchen tana girkin rana, jalouf rice take da yasha kayan lambu Zainab ce ta shigo ƴar Baffa Jibo wacce zata kai shekara 28 ƙatuwa ce baƙa kana ganinta kasan tsohuwa ce yauƙi take tana yamutsa fuska tace "ke Amatu me kike girka wa ne? maza ki sauƙe ki dagamin Indomie me ruwa ruwa taji hanta sosai.
Kallonta Amatullah tayi tace "Anti Zainab kiyi haƙuri ki ɗan jira yanzu shinkafar zata ƙarisa sai kici.
"Dan ubanki ni kike cewa na jira ki kammala? to bazan ci shinkafar ba Indomie nake so ki dafa min nam da minti biyar ki kawo min falo ina jiranki in kin ƙi kuma jikin ki ne zai gaya miki wawiya kawai. ta faɗa tana jan tsaki ta fita, ba yadda ta iya dole ta ɗaura mata dan tasan ba abu me wuya bane ta kamata ta jibga, tsoron kar a taɓa mata lafiya yasa tayi hanzarin gamawa ta kai mata a falon ta sameta tana zaune ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya, rusunawa tayi ta ajiye mata, Shema ce da ke zaune gefen Anti Zee tace "Nima Amatullah ki girka min kamar yadda kika yiwa Anti Zee ɗin nam yaji hanta da kifi sosai...

*★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★*

A haka suka shiga gidan a dining suka hangi su Sweetie da suke zaman jiran su dan ƙa'idar gidan ce basa fara cin abinci sai gaba ɗaya wanda suke cikin gidan sun hallara, da sallama suka shiga direct suka nufa inda suke zama sukayi Papa yana cewa "ashe dai har yanzu ana so mu,an tsaya jiran ƙara so war mu"
"Ba dole a so ku ba" cewar Sweetie tana haɗe fuska, Nabeeha ce ta zubawa kowa amma banda Papa Sweetie ne ta zuba masa da kanta, white Rice ne da stew sai kuma haɗin salad, da ita da Sweetie ne suka girka dan sam Sweetie bata yarda ƴar aiki ta dafawa ke gidan ta abinci ba, tafi so komai tayi masa da kanta...

*Note...*
'''Da yawa wasu matan sukan bani mamaki wai dan kuna da kuɗi zaki ɗauko ƴan aiki masu gyara miki gida shara wanke² girkin oganki gyaran room ɗinsa zai zamana bakya aikin komai a gidan ki, wannam wani irin zaman aure kike? bakya samun ladan aure sai dai na sex🤔 ƴar uwa komai da kika yi a gidan ki me kyau kar ki manta lada kike samu tun daga shara wanke² wanke musamman tsaftace shimfiɗar me gida da kuma girkinsa, duk kuɗin ki ace dai a babu a babu ke kike yiwa me gidan ki girki da hannunki ki kuma gyara masa muhallinsa sauran aikin gida kuma kya barwa ƴar aiki, amma dan sakarci ace ƴar aiki babu abun da bata sani ba na mijinki tun daga room ɗinsa har izuwa cimarsa, wlh mata mu gyara kar daɗin duniya ya shagaltar damu, za kaga mace wai tafi ƙarfin yin aiki a cikin gidan ta ita ga me kuɗi hmm ai ko ba kiyi komai ba kyayi aikin me gidan ki, wannam aiki da muke yiwa mazajen mu su kansu ba ƙaramin daɗi suke ji ba ace yau ga Matarka ta gyara maka muhalli sai zuba fitinan ƙamshi yake gata a kitchen tana tsara maka abinci me sa motsin kunne, ko ace gashi ta kammala ta jeresu kai kawai take jira, wlh ko da ɓacin rai ya dawo sai kin ga murmushi ya kuɓece masa, amma yau ya dawo ya tarar ƴar aiki ce me gyara masa room sannam ita take haɗa masa abinci ita zata zo ta zuba masa abinci ke kina chan ɗaki ko kuma ma bakya gidan baga ɗaya🤔 ko bashi da niyar ƙara miki kishiya wannam abun shi zai ja hankalin sa izuwa ya dan ƙara miki kishiya ni dai ba ruwana.'''🤣🚴🏻‍♀️

Papa yana cin abincin yana zuba santi sai dariya suke masa Sweetie tace "ko dai mu saka maka waiji ne Papa? dariya suka yi yace "ai girkin ne na rasa da me zan misaltashi wajen daɗi wlh, sai da suka kammala sannam suka dawo falo aka ci gaba da hirar gaba ɗayansu, Kaa'af ne yace "Papa yaushe Yaa Taufeeq zai dawo ne? Papa ne ya kallesa yace "nam da 1month insha Allah my son kayi missing ɗinsa ne? tun da Papa ya ambaci Yaa Taufeeq zai dawo bara'ar matasan gidan ta ɗauke Nabeeha, Jawaad, Nazmar dan sam basa ƙaunar ace yana gari sun fi so kullum ace yana chan wata ƙasar su kuma suna nam dan koman su yafi tafiya dai² acewar su.
Su Papa duk sun gane me ya dishar da fara'ar da suke yi, Yaa Sayyid ne yace "an ƙira muki mutuwar ku ko? Su Khairat ma hakance take faruwa da su in har akace Taufeeq zai dawo sai kace wani ance gobe zasu mutu, aiko suma zanje na basu wannam labarin. ya ƙarasa yana dariyar mugunta.
Sweetie ne tace "ba dole suyi haka ba tun da yana maganinsu ai ni wallahi Allah Allah nake ya dawo domin ya min maganin waɗan nam ja'iran kana gani gida suke mayar min kamar wani club. ta faɗa tana dangwarin goshin Nazmar da yayi kicin² kamar zuciyarsa zata fito.
"Wato so kike yazo ya hana min yara sake wa ko? aiko zance ya ƙara shekara guda a chan muga ta tsiya, cewar Papa yana ƙunshe dariyarsa dan shima yasan sarai abun da suke aikatawa da ya dawo zasu koma zana firzin...'''(Kar dai ku manta akwai zazzafa mai zazzafan salo wanda zai zo muku nam ba da jimawa ba akan fara shi me sauƙi'''
*AMRISH AL'IMASH*
'''A rayuwa ko wani bawa da irin ƙaddarar da take zuwa mishi, walau me kyau ko maras kyau, kamar nima hakan ce ta kasance da ni, sai dai ni kash! bana iya babbancewa ta yadda duk wani abu a me kyau nake nake sama masa matsuguni, rayuwa nake kamar ba mutum ba, hakan yasa nake samun kyara da tsangwa ta ko wani fanni hakan yasa mutane suke min kallon anya ni MUTUM ce?)'''
_daga ji kunsan akwai ƙura akwai tirka² ku dai kuyi hanzar motsa aljihunki domin nuna min haƙiƙanin ƙaunar ku a gareni domin ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannam number 08132761212_

*ONE LOVE*💞🤞🏻

TAUFEEƘWhere stories live. Discover now