Episode 13&14

226 20 0
                                    

*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO…*✍🏻

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul💋'''

*Episode 13&14*

*...* Kawu yaci gaba da cewa "wlh ka bani mamaki Taufeeq ni kai na ka bani kunya bare kuma mahaifinka da yake matuƙar alfahari da kai, ni dai shawaran da zan baka shine kawai kayi haƙuri ka rungumi auren nam in sha Allahu za kaci ribar sa ina tabbatar maka kaji ko?

    Taufeeq da haushin tsohon ya gama kamashi bai iya amsa masa ba, Papa ne yaja goron numfashi cikin dattaku ya fara magana "Taufeeq in dai har ni na haifeka umurni na ke baka ba shawara ba ka fara shirye-shiryen auren ku da Nabeeha  kai wlh nam da 2weeks zan ɗaura maka aure da ita, in har na isa da kai, in ma ban isa da kai ba zan gani get out kar in saɓa maka yanzun nam.
  Fitowa yayi duk ransa a dagule bayan gidan ya nufa a bakin swimming pool ya zauna ya kamo lips ɗin sa na ƙasa sai tsotsa yake, lokaci zuwa lokaci yake furzar da iska gaba ɗaya kansa ya gama kullewa tunanin mafita kawai yake amma ya rasa, hannu ya sanya ya cire sigari a aljihun sa ya kunna ya sanya a bakinsa cikin wani irin salo gwanin birgewa yake shan sigarin yana furzar da iskar ko rabi bai gama sha ba ya jefar tare da jan tsaki, Nabeeha da tun zuwansa take zaune a wajen tunanin Yaa Sayyid ne ya addabeta tun ranar da yazo ya shareta har yau bata ƙara sa shi a idon ta ba kuma ko ta ƙira layinsa baya shiga, hakan yasa ta shiga damuwa shiyasa tazo wajen ta zauna, ta kafesa da idanu tana kallon abun da yake sai dariya take ƙasa-ƙasa dan kar yajita, mamaki ne da kaɗuwa suka taru suka mata yawa, idanunta ta zaro me matuƙar sheƙi da ɗaukar idanu, ganin sa da tayi yana shan sigari, taɓe baki tayi a fili tace "ashe ma ɗan iska ne Yaa Taufeeq ɗin tun da gashi har sigari yake sha, sai yana yiwa mutane wa'azi kamar na Allah mtsww ta ɗan ja tsaki ta tashi ta bar wajen dan karma ya ganta.

   Ya jima zaune a wajen a juma yace "why? why? why!! Papa zai min haka kamar ni a rasa da wacce za a haɗani da ita sai wacchar figigiyar yarinyar wanda hankali bai gama isarta ba, gaskiya ni ba a kyauta min ba wlh.
    Sai da aka ƙira magriba sannam yabar wajen wanka yaje yayi ya nufi masallaci har yanzu ransa a dagule yake, ko da dare tayi kasa bacci yayi juyi kawai yake a gado amma sam bacci yaƙi ziyartar sa, kalaman Sweetie da ya tuna ne suka ɗan kwantar masa da hankali dan da yaje ya sanar mata taje ta samu Papa ta masa magana a fasa maganar aure nasiha tayi ta masa dangane da bin umurnin iyaye tare da azabar duk wanda ya saɓawa iyayensa duk da ya sani amma jin zancen ta yake sabo kamar bai taɓa jiba ranar dai bacci ɓarawo ne ya ɗaukesa.
Washe gari da yamma Nabeeha sukayi shiri za suje shopping Sweetie suka sanar wa tace sai dai taje ta gayawa Yayansu ita ba ruwanta, su Samha suka ce su dai babu inda zasu gwara a haƙura da zuwan, Nabeeha kuwa tace dole sai anje domin sayayyan kayayyakin partyn su za suyi, part ɗin sa ta nufa rai ɓace, knocking tayi har sau uku shiru hakan yasa ta tura ƙofar ta shiga, parlorn fes yake sai tashin ƙamshi yake, ido tayi ta warewa chan ta hangoshi kwance a kan kujera ya lumshe idonsa, kallonsa tayi taga kamar ya ɗan rame, taɓe baki tayi ta ƙarasa wajen sa tace "Yaa Taufeeq ina wuni dama za muje supermaket ne shine Sweetie tace sai munzo mun gaya maka, ko motsi baiyi ba balle tasa ran ko ya jita, da ɗan ƙarfi tace

"Yaa Taufeeq ka ji muje ko?"
     "Yaa Taufeeq!
A fusace ya miƙe ya kifeta da mari ya sake kifa mata mari yasa ƙafa ya jideta ji kake guf! ta ɗagu ta rimu da ƙasa wani azababben ƙara ta sake sai kuma ta sulale ƙasa sumammiya, cikin matsanancin ɓacin rai yace

"Dan ubanki da kin san tsanar da na miki baza kina dosowa inda nake ba, ke in ba marar hankali ba a kwance kika zo kika sameni fa, kin san dai da yamma bana bacci tunda ni dai ba jahili bane, tun da kika yi maganar farko da kika ji ban amsa ba, sai ki koma in da kika fito salin alim, amma da yaje ƙwaƙwalwar kifi gareki ai ga abin da kika jawa kanki wawiya kawai wlh na tsaneki!

TAUFEEƘTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon