Episode 19&20

228 14 0
                                    

*TAUFEEK*

NA

*Hafsat A Garkuwa*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

_Walle ba yawa kuyi haƙuri da wannam_🥳

*Episode 19&20*

*...*"Saif ina so kamar yadda kake kula da ƙannenka ita ma ka ke kulawa da ita duk wani abun da zaka yiwa su Zarah ya zama da Amatullah a ciki domin ita ma ta zama ƴar gidan nan insha Allahu har'abada aure ne kawai zai raba mu da ita dafatan dai ka fahimce ni?

"Eh na fahimta Abba insha Allah kuma zanyi ƙoƙarin hakan dan wlh ta bani tausayi nima sosai gaskiya duk wanda akace mahaifansa basa duniya kuma bai samu iyayen riƙo nagari ba yana cikin gararin rayuwa Allah yasa mu dace, ya faɗi cike da tausayawa.
   Da "Amin" su Ammi suka bisa, sannan Ammi tace

"Wlh nima ina mugun jin tausayinta kuma na karɓi ragamar zame mata uwa kuma tagari in sha Allahu baza tayi kuka da ni ba"

"Masha Allah, Allah ya miki albarka na gode muku sosai Saif zaka iya tafiya ka gaishe da Nana da jiki"

"Za taji Abba ya faɗa tare da ficewa daga part qin

Washe gari Amatu suka fita da Zarah siyayya duk wani abu da mace take amfani dashi sai da Zarah ta saiwa Amatu, Amatu dai kallonta kawai take dan Zarah tace kada ta yarda ta mata zancen kayan sunyi yawa sai dai suka cika mota maƙil da kaya, basu zarce ko ina ba sai wajen telan su ta bashi wasu kayan kala talatin su atamfa, shadda, les da yadika masu matuƙar kyau bayan kananan kaya da ta jida mata da su doguwar riga, ya sanar dasu nan da sati zai kawo kayan ta bashi kuɗi suka tafi.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya wa Amatullah cikin farinciki dan tuni ta mance baƙin cikin su Baffa Jibo sai dai duk kwanan duniya sai tayi kukan rashin iyayenta duk da bata bari iyalan gidan su ganta tana kuka, domin za suga kamar suna mata wani hali ne duk da ta ɓangaren Hajiya Balkisu da su Raudah tana samun tsangwama da kyara amma hakan baya damunta acewarta ƴan uwanta na jini ma sun mata abun da yafi haka kuma ta shanye balle su, hakan yasa duk abun da suke mata baya damunta, a wannan lokacin aka sanyata makarantar da su Zarah suke babban makaranta ce ta ƴaƴan manyan attajirai duk wanda ka gani a wannan makarantar to sunci sun take ne a masu kudin ma manyan su ne, duk da bata da takaddu amma anyi mata gwaji sannan Saif ya sake musu kuɗi hakan yasa ba wata wahala aka sanyata Level2 in da su Zarah suke dan dama a nan ta tsaya da zuwa makaranta.
  Haushi agun su Raudah kamar me ko da ta sanarwa Hajiya Balkisu sai da tayi ta sababi kamar bakinta zai fita Hajiya Fatima dai kanzil bata ce mata ba.
Yau ta kama Monday da wuri suka shirya su huɗu sunyi kyau sosai sai dai duk kyansu basu kamo Amatullah ba tayi kyau sosai cikin atamfa ɗinkin riga da siket Saif ne yau zai kaisu saboda driver baya nan tuni su Shamsiyya sun jima da fita har sun shiga motar da sallama suka ƙarasa gaba daya suka gaida Saif dake jingine jikin motar yana jiransu amsawa yayi cike da ƙaunar yan ƙannan nasa, cikin zolaya ya kalli Amatu yace

"Dafatan in kuka je yau baza ki sake ɓata irin na rannan ba?
Ranar da ta fara zuwa ne sunje masallaci ta fito ta nemi hanyar ta rasa kuma bata ga su Zarah ba maimakon ta yiwo waje sai ta ƙara wucewa ciki ga makarantar gari guda ce.

"Dariya tayi tana rufe fuskarta cike da kunya gaba daya suka sa dariya Ruky tace
'Yaya ai ranar ma saboda bata san hanya bane amma yanzu ai tasan ko ina"

"Yo dama ita ta sani matar da take ƙauye talakace tukuf bata taɓa zuwa dubai ba sai yanzu da Abba ya kaso mana ita ai dole tayi gidadanci ta kasa gane hanya"
Raudah ce dake daga cikin mota take jefowa Amatullah magana

Ran Saif ne ya ɓaci ya buɗe motar ya wanke Raudah da mari ya ƙara da cewa
"Shi talakan an faɗa miki banza ne da a ko da yaushe za kina fada masa duk maganar da tazo bakinki? wlh kikiyayeni dan naga kanki na mugun rawa kuma zan daidaita miki shi bana son iskancin kin nan"
Sannan ya juyo ga Amatu yace "Pls kiyi haƙuri kinji"
Murmushi kawai Amatullah tayi ta tuni lokacin da mahaifinta yana raye babu ƙasar da bata zagaya ba a faɗin duniyar nan sai dai ɗai-ɗai amma yau ita ake yiwa gori murmushi ta sake tare da girgiza kanta, Zarah ne ta kama hannunta suka isa bakin motar shamsiyya ta shiga sai Zarah ta kalli Amatullah tace
"Sis pls ki shiga gaba wajen zai mana matsi"
Jim tayi kaɗan sai kuma ta buɗe gaban ta shiga ya tada motar suka fice, har suka isa babu wanda ya ce da ɗan uwansa uffan.
5pm suka dawo a gajiya waka Amatullah tayi ta sa doguwar riga mai kawai ta shafa amma tayi kyau sosai falo ta fito domin su Zarah sun jima da fita abinci suka ci sannan Zarah ta jata suka nufi part ɗin Saif da Sallama suka shiga Nana dake zaune a falo cikin ado ta amsa musu cike da fara'a, zama sukayi suka gaisa cike da jin daɗin zuwansu tace
"Wlh kamar kunsan zaman shirun ya isheni ba abokin hira ga Yayanku sai 8 shi da ya dawo gidan nan tun ɗazu nake saƙe-saƙen na tafi part ɗinku amma na kasa dan kunyar Ammi nake ji da wannan ƙaton cikin.
Dariya Zarah tayi tace
   "Aunty meye kuma abun kunya nifa wlh cikin kin nan kyau yake min"

Ta faɗa tana rufe idonta Amatullah ne ta ɗaga mata dukan wasa tana faɗin
"Wlh Zarah baki da kunya a gaba na da gaban Aunty kike faɗin haka ko kunyar mu baki jiba.
  "Ah! toh faɗa mata dai Amatullah, cewar Aunty tana dariya.

Harara Zarah ta gallawa Amatu tace
    "Kaga ƴar rainin wayo ke zanji kunya? ashe ko na rasa wacce zanji kunya, Aunty kuma ai normal ne ta faɗa tana kanne mata ido ɗaya suka sa dariya gaba ɗaya.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Mamaki ne ya kama Taufeek ganin a kwana ɗaya an gyara gidan ya zama tamkar sabo duk da dama ba wani abu yayi ba amma komai na gidan an sauya hatta penti yasan ba kowa zaiyi wannan aikin ba sai Papansa oh! wannan tsoho ya nace dai sai ya haɗani da wannan alaƙaƙan a haka ya wuce ɗaya part ɗin gidan, su Nabeeha kuma suka shiga Part ɗinta wanda ya ƙayatu da kayan more rayuwa su Aunty Maryam ƙanwar Sweetie sai santin gidan suke dan duk yadda kuka san haɗuwar gida wannan ya take su, in ka shiga gidan baza kaso ficewa ba, iskarsa ma ta musamman ce lol.
     A ɗaya daga cikin ɗakin saman suka sanyata basu wani jimaba suka juya tunda suka taho Nabeeha take kuka har yanzu kuka take kamar ranta zai fita sai yanzu take ƙara nadamar amincewa da tayi da wannan auren, gani take ta kawo kanta da kanta kabarin da za a binneta tunawa da tayi da nasihar Sweetie na duk lokacin da ta lula duniyar tunani tayi ƙoƙari tayi alwala tayi ta sallah domin korar duk wani tunani da Yazo zuciyarta, hakan yasha ta miƙe tana haɗa hanya dan wani irin yunwa da takeji rabonta da abinci tun jiya sai tea da tayi ta sha, Alwala tayi tazo ta gabatar da sallah sai da taji tana jin bacci sannan ta sallame, agogo ta duba ƙarfe 11;00pm kayan baccinta ta sanya ta kashe wuta ta kwanta duk da yunwar da take ji amma haka ta kulle idonta ko baccin zai zo amma yunwa ya hana hakan, kuka ta sanya na tausayin kanta dan tasan da a gida take Sweetie baza ta barta haka ba.
   Taufeeƙ dake ɗakin dake kusan nata har ya fara bacci cikin bacci yaji Papansa yana ƙara jaddada masa amanar da ya damƙa masa, da sauri ya miƙe ya sauƙo gadon a hankali ya fara tafiya direct ɗakin Nabeeha ya nufo kansa tsaye yana tafe yana totsan lips ɗinsa...

_Uhumm to gashi dai anyi aure ko me zai wakana a wannan gida oho!_

_Tofah me Taufeek zai je yayi a ɗakin Nabeeha?_

_Shin ko dai ya yarda da amaryar tasa ne?_

_In ko haka ne anya Nabeeha zata amince da shi?_

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212

TAUFEEƘWhere stories live. Discover now