Episode 23&24

194 11 0
                                    

*TAUFEEK*

NA

*Hafsat A Garkuwa*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*Episode 23&24*

*...* Kamar daga sama suka ji yana cewa "lallai Zarah ban san baki da kunya ba sai yau, ashe kema fallalliya ce ban sani ba? ya faɗa yana riƙe da haɓansa tare da ƙarasowa cikin falon a hankali Nanah ta miƙe ta tari mijin nata tare da masa sannu da dawowa, da sauri ya riketa yana faɗin
"Baby ba na hanaki saurin tashi wajen tara na bane, bayan kinsan ga yadda kike zama da ƙyar tashi da dabara.
Murmushi Nanah tayi tace "haba Dear taya ka dawo kuma ina kallon ka bazan zo na tare ka ba ni kam gaskiya bazan iya ba kalan kaga wata ka auromin, ta ƙarashe maganar cikin sigar shagwaɓa.
Hannunsa ya ɗaura akan cikin da yayi wani uban tsini yace
"Ɗan Baka kaji dai abun da Momyn ka take faɗa ni dai bance zan ƙaro ba amma kullum maganarta kenam kayi mata faɗa ya ƙarasa maganar yana shafo mararta.
Da sauri ta buge hannunsa cikin raɗa tace "ka mance su Zarah suna wajen ne.
Zaro ido yayi dan gaba ɗaya ya mance a tare suka kalli indasu Zarah suke amma ba bu su ba alamar su, basu san tun lokacin da ya fara baɗin Baby ba na hanaki saurin tashi ba Zarah ta kama hannun Amatu suka gudu, tana godewa Allah da yasa ya mance shafinta ya koma shafin matarsa.
Murmushi Nanah tayi tace "kawai ka kunyatar ni gaban bayin Allah.
"To ai bani nace su zomin falo dai-dai lokacin da zan dawo ba ai gobe baza su sake ba, ya faɗa yana rungumarta a jikinsa.
Haka Amatullah taci gaba da rayuwa cike da farinciki, a school ɗinsu Allah ya zuba mata farin jini maza da mata hakan ya sake jawo ƙarin tsana a zuciyar su Raudah ne man hanyar da zasu kunyatata suke amma sun rasa yau Raudah tayi alƙawarin sai ta kunyata ya a idanun wanda suke kallonta da muhimmanci, zaune suke a gindin wata bishiya ta hango Amatu da Zarah da wata ƙarsu Kausar da sauri Raudah ta miƙe ta nufi inda suke tana zuwa ta wacce gyalen jikin Amatu tare da hankaɗeta da ƙarfin tsiya ta tafi luu! zata zube ƙasa kamar an jefoshi da hanzari ya tareta ta faɗi a kafaɗar shi ta lafe a jikinsa tana maida numfashi kamshin turarensa ne ya tuna tar da ita a inda take kuma sannan a jikin wani take da sauri ta miƙe yayi hanzarin fizo gyalen dake jikin Raudah ya yafawa Amatullah kallonsa tayi a hankali kyakykyawa ne ajin karshe bashi da tsayi sosai yana da haske amma ba sosai ba, fuskar nan nashi cike take da fara'a cikin cool voice tace
"Na gode fa sosai"
"Kar ki damu ai yiwa kaine amma shawaran da zan baki ki daina kula irin mahaukatan yaran nan irin su wannan da ta miki shirme ya faɗa yana nuna Raudah da gaba ɗaya kunya ta gama rufeta dan bata tsammaci ƙaiƙayi zai koma kan masheƙiya ba harara ya balla mata.
Cike da burin kunya tace
"Ai kai ne mahaukacin wawa kawai kai kasan waye ubana a garin nam kuwa? kasan matsayin mahaifini kuwa?
Harara ya ƙara watsa mata cikin ko in kula yace
"Ke ƴar gidan ɗan adam ne me kunne biyu, ido biyu, hanci ɗaya, da kuma baki ɗaya, hannunsa guda biyu haka zalika ƙafansa biyu a ko wanni ƙafa da hannu suna ɗauke da yatsu biyar, kin tabbatar na masa farin sani ko?
Ya faɗa yana ɗage mata gira gaba ɗaya wajen suka sa dariya, Zarah ta kama Hannun Amatu tace
"Kunga mu shige a nan wlh ni yunwa ta isheni kuma yau ban jin zan iya cin abincin skul d'in nan.
Wuce wa sukayi da sauri ya biyo su yana faɗin ni ma ko bazan iya ci ba ko za muje wani eatry ne mu samu abun taɓawa da sauri Kausar tace
"Wlh kuwa kamar kasan abun da ke raina"
Harara Amatu ta galla mata tana faɗin
"To ni dai ba dani za ayi haka ba
"Bare kuma ni! cewar Zarah tana nuna kanta da hanxari ya dawo gefen da Zarah take yace haba "Sis wannan wacce irin mugunta ce haka ya ina ji ina gani za kisa na rasa damar da na samu a yau.
Murmushi Zarah tayi dan ta gane mai yake nufi sarai dan tun ba yau ba ta gane take-taken shi kawai damace da bai samu ba cikin zolaya tace
"To ni dai babu abun da zance in Lil sis ta amince to nima na amince.
Ɗaka mata duka Amatu tayi tace "wato ni so kuke yaga baƙi na ko? In nace baza mu je ba shikenan sai kusa ya ƙullace ni a ransa to baruwa na.
Dariya yayi yace "yanzu dai kin amince ko?
Kai ta ɗaga tare da faɗin "to ya na iya.
Cike da farin ciki ya ɗaga hannunsa ɗaya tare da naushin iska yana faɗin

TAUFEEƘWhere stories live. Discover now