Episode 69&70

251 23 5
                                    

*TAUFEEƘ*
NA
_Hafsat A Garkuwa_

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
           ✨W.W.A✍🏻
https://www.facebook.com/Women-Writers-Asso-106752595253176/

BA EDITING🥺

*Episode 69&70*
… Gaba ɗayansu da sauri suka fice Saif na riƙe da hannun Raudah dan tun farin maganar  Dr. Ta miƙe jin tana jin jiri ne zata faɗi Saif ya riƙe ta suna tafiya a hankali har suka isa ɗakin da Momy take a kwance take hawaye ne kawai yake sintiri a idanunta ji take ta tsani kanta da kanta, Ammy ne ta iso wajenta hawaye na zuba a idanunta tace
"Balkisu ba kuka za kiyi ba addu'a za kiyi Allah ya baki lafiya."
"Hmmm! Ammy kenan baza ki gane kukan da nake ba, ba wai ina kuka ba ne akan abun da ya samen ba ina kuka ne na tsanar kai na don Allah ina so kilu taramin kowa da kuka san ya shafeni a yanzun nan domin nasan ni tawa ta ƙare."
Daga haka ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi Raudah ne tazo ta rungumeta suka cigaban da kukan tare.
Abba ne ya ƙira gidan su Momy ya sanar musu da kuma bukatar ta haka ma gidan sa, ba jimawa asibiti ya cika maƙil bayan sun gama hallarar ne Momy cikin kuka tace
"Ba komai yasa na buƙace ku ba sai dan muyi ganawa ta ƙarshe domin ni dai tawa ta ƙare sannan kuma naja hankalin ku, ni da kuka ganni na kasance mutuwa, azzaluma wacce bata son wani yayi farin ciki in ni banyi ba, Ammy ta riƙeni da zuciya ɗaya amma ni ban sonta bana ƙaunarta hatta yaranta bana so dalilin wannan hatsarin da nayi ma…
Nan ta zaiyane musu duk abun da ya faru cikin kuka ta ƙara da cewa
"Sai kuma gashi abun da nayi ya koma kaina ku kalleta don Allah kafin wani nawa ya fara zuwa kai na itace tq fara zuwa har kuka take na tausayi na amma a haka ni bani da buri da ya wuce naga ta shiga damuwa kaico na! Allah wadaran duk wani mai irin halina don Allah don girman Allah Ammy ki yafemin don Allah ina roƙon ku da ki yafemin!
Gaba ɗaya ɗakin baka jin komai sai sheshsheƙan kuka domin Momy tayi mugun basu tausayi cikin kuka Ammy tace
"Balkisu na yafe miki duniya da lahira Allah ubangiji yq baki lafiya Allah kuma ya yafe miki laifukan da kika aikata ki dai na kuka."
Abba ji yayi hawaye sun zubo masa yasan tabbas yayi dace da mace ta gari wacce aka mata laƙabi da Mar'atu saliha cike da tausayi yace 
"Nima na yafe miki Balki Allah ya ƙara sauƙi Fatima fito mu tafi."
Daga haka yayi waje yana goge ƙwalla.
Kowa sai da ta nemi yafiya a wajen su suka kuma yafe mata dan duk rashin imaninka in ka kalleta sai Momy ta baka tausayi matuƙa anan tq fara yiwa yaranta nasiha da kar su ɗauki hali irin mata domin kaf halayanta ba masu kyau ba, sai 12 suka tafi gaba ɗaya a lokacin anyi mata allurar bacci saboda fisge fisge da ta fara gaba ɗaya cikinsu a matuƙar sanyaye suka tafi cike da tausayin Momy.
Suna komawa aka cigaba da hidimar biki ƙarfe 2 daidai aka ɗaura auren Zarah da angonta Nabil ba zato ba tsammani maroƙi yace an ɗaura auren Amatullah da angonta Lamir Ahmad akan sadaki dubu ɗari biyu lakadan ba ajalan ba nan na hango ango Lamir bakinsa n nan kamar mai tallan makilin yasha shadda fara sai walwali yake sai dai ya rame domin ba ƙaramin jinya yayi ba a lokacin da mahaifiyarsa ta sanar da shi ya rabu da Amatullah yayi magiyar har ya gaji tq kuma kwace wayoyinsa dan ko ƙiran da su Amatullah suke masa wayar tana wajen mahaifiyarsa sannan kuma tace muddin yaje wajen da Amatullah take Allah ya isa bata yafe ba hakan yasa ya shiga matsanancin damuwa baya zuwa ko ina daga ɗaki sai ɗaki
Ana haka Abba ya samu mahaifin Lamir ya sanar dashi gaskiyar lamari akan Amatullah jininsa ce a tare suka je wajen Mahaifiyar Lamir suka sanar da ita tayi matuƙar farin ciki sosai domin dama ba a son ranta ba ne harda zigin Momy da kuma ƴan uwanta da ta sanar musu hakan yasa suka cigaba da shirye shirye har ta kai ga yau an ɗaure aure sai dai kuma ta ɓangaren Abba babu wanda ya sanarwa a gidan sa domin yana so ta musu bazata, koda aka sanarwa Lamir ji yayi kamar an amsa albishir da gidan aljanna tsabar farin ciki ji yake ina ma zai ganta ya san yata a jikinsa ɗumin jikinta da nasa su haɗu, a rana ɗaya ya sanar da abokansa na nesa da na kusa Allah Allah yake gobe tayi yaji an ɗaura aure, zuwa yayi suka taya juna murna shi da angon zara gaba ɗaya kowa fuskar nan tana cikin walwala basu wani jima suka ranƙaya cika tumbinsu sai da Abba ya gama da abokansa sannan ya nufo gida ransa fes.
Tuni Amatullah taji zancen ɗaurin auren ta ta wani ɓangaren tana farin ciki ta wani ɓangaren kuma haushin Lamir take ji saboda yadda ya ɗauketa ya zubata a kwandon shara, Ammy ma da taji tayi farin ciki sosai haka duk wanda yaji har da na Amatullah akayi binsu yake da addu'ar zaman lafiya sai yamma lis Abba ya tarasu ya musu nasiha mai ratsa zuciya sannan ya dawo kan Amatullah ya ɗaura da cewa
"Jikata ina so ki zauna da mijinki lafiya kar ki duba abun da ya faru ki ɗauki hakan a matsayin jarrabawa sannan kuma zancen su Baffa Jibbo in kika yi ƴan kwana biyu za muje da ke da sannan zamu makasu a kotu domin su girbi abun da suka shuka Allah ubangiji ya muku albarka za ki iya tafi."
Gaba ɗaya kuka suke yi Ammy ne ta kamasu suka fito ba jimawa akazo ɗaukar amare Zarah aka fara kaiwa tamfatsetsen gidan ta sannan aka kai Amatullah itama aljannar duniyar gidan ta daga jin sunan ma ba sai an tsaya faɗa muku ba kuma kunsan gidajen karshe ne ku kimanta amare sai dai muce Allah ya baku zaman lafiya.
Gari yayi tsin ko wani ango an masa rakiya yayi kuma duk abun da addini ya tanadar tuni Nabil ya fara kashe arna sai dai kuma duk yadda Zarah ta ɗauki harkar yafa wuce tunaninta ihu ta fara da naiman ɗauki a wannan rana har zagina sai da Zarah tayi lol😅
A bangaren Amatullah kuwa Lamir kamar zai sanyata ciki yake wani irin kulawa yake bata Amatullah taso ta turje amma jin yadda gogan nata yake binta yasa ta lafe a jikinsa aka shiga kashe arna dan Lamir ma ba sauƙi.

TAUFEEƘWhere stories live. Discover now