Episode 4

327 20 0
                                    

*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO...*✍🏻

*MASOYANA DON GIRMAN ALLAH KUYI MANA SUBSCRIBE ƊIN WANNAN CHANNEL DOMIN SAMUN LITATTAFAN SAURARE DA KOYON SANA'O'IN HANNU DA SAURAN SU NA GODE*👇🏻
https://youtube.com/channel/UCY1pIcI2DlVykTz57m6Q3TA

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💋 Sa'eed'''

*Episode 04*

*...* Domin in ya dawo duk wani shi ge da ficen su sai ya sa ni har ta kai ta kawo ma in har zasu fita sai sun sanar dashi har inda zasu shi kuma zai faɗa musu lkcn da za su dawo, hakan yasa sam basa so ya dawo ƙasar sun so kawai yana zama a chan in ganinsu yake su yayi ya ƙirasu video call, yana mamakin yadda yaran basa so su ganshi a gida Kaa'af ne kawai ke son kasancewa dashi a ko da yaushe.
Nazmar ne yace "wlh Papa kawai ka ƙara masa shekaru yaje yayi ta zaman sa ka aura masa ƴar cham ma su tare a chan ba sai ya dawo ba mu sai muna zuwa muna duba shi.
Dariya gaba ɗaya sukayi saboda yadda suka ga yayi maganar, Papa ne yace "in ban da wauta irin taka ai dama bani na turashi ba Shugaban ƙasa ne ya turasa, saboda shi bazai samu damar halartar taron ba, ni nayi mamaki ma da wannam karon ya jima haka, haka suka yi ta hira akan Taufeeq ya zauna a chan Papa yana musu tsiya Sweetie kam ta cika tayi fam saboda ita bata ƙaunar Taufeeq yayi nesa da ita ko kaɗan amma su burin su ya zauna a cham ma kar ya dawo, amma kuma ba ranar da baza su ƙirasa a waya su jima suna waya ba, amma kuma basa ƙaunar dawowan sa oh! har ƙarfe goma da ƙyar Papa ya kora Yaa Sayyid dan hirar tayi daɗi an bar batun Yaa Taufeeq an shiga wata hirar duniyar.
Haka suka cigaba da guda nar da rayuwarsu cikin farin ciki da ƙaunar juna, lokacin Taufeeq na dawowa yana ta ƙara towa yanzu haka saura 2weeks Yaa Sayyid in bai zo yau ba zai zo gobe, gaba ɗaya ya mace akan son Nabeeha ita kuma yanzu sam bata sake masa fuska kamar da, dan tana jin kunyar sa da nauyinsa sosai, yanzu ma zaune take a parlour sanyi take da doguwar riga ash color an ƙayata sa da stone work red sosai ya mata kyau kanta babu ɗan kwali bata yi wani kwalliya ba amma tayi kyau, chat take da friend ɗinta sai ƙyalƙyale dariya take kana ganinta kasan abun dariya take gani a cikin wayar tata, Sallamar sa taji gaban ta ne ya faɗi sai kuma ta dake tace "wa'alaikas salam Yaa Sayyid sannunka da zuwa.
"Yauwa sannu My Queen"
Ya faɗa yana ƙaraso wa cikin parlou'n sanye yake da t-shirt white me ratsin dark blue da jeans kannan sai yalƙi yake alamar yasha gyara murmushi ya sakar mata sai ta tsinci kanta da maida masa, zama yayi ɗan nesa da ita yace "My Queen yau ke ɗaya ce a gidan?"

"Eh wlh Yaa Sayyid sun tafi Habila cream gaba ɗayan su ni yau sam ban jin fita ne shiyasa ban bisu ba.

"Kece rabun dai nazo na ganki ne yasa baki je ba ko Queen? ya faɗa yana dariya.
Dariyar ita ma tayi tace "ai kuwa dai Yaa Sayyid, "yanzu sai ki tashi mu tafi mu bisu ko dama tafiyar masoya tafi daɗi, dan haka ɗauko mayafinki mu tafi.
Kwaɓe fuska tayi cikin shagwaɓa tace "wlh ni Yaa Sayyid bana son zuwa ko ina yau zaman gidan yafi min daɗi, ta faɗa tana ƙara turo ɗan ƙaramin bakinta.
Murmushi yayi a zuciyar sa yana faɗin "me yasa ita ko me tayi ƙara kyau take ne? ganin bazai samu amsar tambayar sa bane ya ƙarasa ya kama ɗan ƙaramin bakin tan ya matsa cikin sigan wasa yace "aiko dole sai kinje maza je ki ɗauko mayafin ki kinji *My Queen*.
Ƙara ta sake dan yadda ya riƙe bakin nata ya ɗan mata zafi, baza ta iya masa gardama ba dole taje ta ɗauko mayafi ta yafa a kanta ba tare da ta ɗauki ɗankwali ba kyanta ne ya sake fitowa, hannunta ya kama suka nufo far fajiyar gidan su Sani sai zuba hirarsu suke kamar yadda suka saba, gaban mota ya buɗe mata ta zauna sannam shima ya shiga ya tada suka tafi, suna tafe suna hira, basu zarce ko ina ba sai *NAF Club Kaduna 4.9* Sosai wajen yayi mata kyau duk da ba yau ta fara zuwa ba amma an sake ƙa wata wajen yayi kyau sosai cike yake maƙil da mutane, sayyaya sukayi sosai duk da tayi masa ƙorafi akam ya barshi haka amma fir yaƙe sai da gaji sannam ya bari biya sukayi suka nufo motar zama tayi ta buɗe ice cream tana sha shima ya zauna yana fuskantar ta fuskarsa ƙunshe da murmushi, dan shi mutum ne me matuƙar fara'a a ko da yaushe baza kaga fuskarsa a tsome ba kullum cikin fara'a take.
Kallonsa tayi ganin ya ƙure ta da ido tace "wai Yaa Sayyid kallon me kake min haka ne?
"Uhumm! kin ƙaramin kyau ne Queen, ya ƙara da cewa "na rasa miye lefina dan nace ina sonki ko dai ban miki ba ne? Murmushi tayi tace "kai Yaa Sayyid wace macece za tace baka mata ba, kawai dai in kayi duba da ƙarancin shekaru na, sannam kuma ni Ƙanwarka ce halak malak kaga ba aure tsakanin Yaya da kuma ƙanwarsa.
"Wannam ba hujja bane Nabeeha wlh ina matuƙar ƙaunarki ni babu ruwa na da wani ƙarancin shekarun ki ai auren yarinya ɗanya sharaf wanda kai zaka raineta da kanka yafi daɗi, nasan ni Yayanki ne amma kuma akwai aure tsakanin mu tunda ba ciki ɗaya muka fito ba.
"Ni yadda na ɗauka ciki ɗaya muka fito Yaa Sayyid kaga ba aure kenam, dan Allah mu bar wannam maganar. ta faɗa da ɗan ƙarfi.
Ran sa ya sosu amma ya danne domin yarinya ce dole sai ya fuskanci haka dama, kuma ba ya so ya mata dole ko kuma yasa a mata dole da sai yaje ya sanarwa iyayensu, amma zai bi da ita a hankali har ya shawo kanta, a fili kuma yace "I'm very sorry My Queen bazan ƙaraba. ya faɗa yana kama kunnen sa, dariya haɗe da kunya ya bata ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana cewa "kayi hakuri Bro na ɗaga maka murya.
"Ba komai Queen. A haka suka ƙarasa gida yana janta da hira saboda ta ware suna isa motar su Papa na shiga a tare suka shiga, mamaki ne ya cika su Sweetie ganin Nabeeha domin ba magiyar da basu yi ba akan tazo su safi amma fir taƙi sai gata kuma da Ya Sayyid, gaban Papa ne yayi mummunar faɗuwa...
A zuciyarshi yace "ba dai abin da nake zargi bane yake shirin zama gaskiya? Allah kasa ba haka bane, domin in har hakan ta kasance zumuncin mu zai iya taɓarɓarewa, wanda bazan taɓa lamunta ba, Alƙawari nayi kuma insha Allahu sai na ciki wannam alƙawarin da yardar Allah... Sweetie ne ta katse masa zancen zucin da yake tace "Papa baka ga Nabeeha bane? ta faɗa tana son tabbatar da ya ganta ne ko bai ganta ba.
Dariya yayi yace "na ganta kun san halinta ai ƙila gidan ya mata shiru ne shiyasa suka fita da Sayyid amma muje muji dai, Nabeeha dai dariya taƙe ƙasa² dan tasan za tasha magana wajen su Jawaad wanda ba magiyar da basuyi ba amma taƙi binsu, Jawaad ne yake jefa mata wani banzan kallo na kin raina mana hankali, Nazmar kuwa zungurinta yayi yace "ya miki kyau Nabeeha"
Gaba ɗaya suka ɗunguma sukayi cikin gidan sai mita Nazmar yake akan yaƙi binsu tabi Yaa Sayyid, zama sukayi gaba ɗayan su a falon, Sweetie ne tace "wai ina kuka je ne?"
Yaa Sayyid ne ya kwashe komai ya faɗa musu ya ƙara da cewa "da ƙyar fa ta yarda muka tafi sai da na mata da gaske.
A ɓoye Papa ya sauƙe ajiyar zuciya jin ba zargin da yake bane, dariya yayi yace "ai halin Nabeeha sai ita muma baka ga magiyar da mukayi ta mata ba akan mu tafi amma taƙi ai kai kaci sa'a ma wlh, gaba ɗaya suka saka dariya, nam suka baje abun da suka sayo suka fara ƙaramin party sai a sannam Jawaad ya saki fuskarsa (Ni ko nace oh kai kuma miye naka na ɗaukar zafi haka🤔) sai da sukayi sallar i'sha sannam Yaa Sayyid ya tafi, anguwar Rock road ya nufa domin anam gidan su yake, a wani katafaren gida yayi horn duk da gidan baza a taɓa haɗasa da gidan Papa ba amma shima ya amsa sunansa gida, me gadi ne ya leƙo ya gansa sannam ya koma cikin sauri ya buɗe masa, filin gidan nasu ɗan madaidaici ne wanda a ƙalla zai ɗauki mota 7 yana Parking bayan sun gaisa da Kamilu me gadi ya nufi cikin gidan, yahaniya yayi ta jiyowa yasan kuma bazai wuce Huda itace me bi masa wanda take da shekara 24 sai kuma Samha da take shekara 19 sa'ar Nabeeha sai kuma autarsu Nihal me shekara 5 da sallamar sa ya shiga, Aunty Sa'a ne da ke zaune chan gefensu tana kallon ta amsa masa, babbar mata ce wanda a ƙalla za takai shekara 68 tana da ɗan jiki kana kallon ta za kaga kamar da suke yi da Papa, murmushi ta sakar masa tace "har ka dawo ɗan gidan Papa? (da yake kowa sunan da yake faɗa masa kenam Papa tun daga kan Taufeeq) "eh wlh Oum na dawo suna gaida ki ma, ki shirya duk da nasan kin sani ɗan gidan ki saura sati biyu ya dawo, ai ɗif ɗakin ya ɗauke wuta babu hayaniyar su Huda ko motsi ƙwaƙwara babu sai TV dake aikinsa, gaba ɗaya shi da Oum suka fashe da dariya, Oum tana cewa "Ƴan ƙaniya tun ɗazu nake binki ku min shiru amma sam ƙun ƙi saurarena ma yanzu da kuka ji dodonku ya kusa dawowa ai kun nutsu tun kafin yazo, Allah dai ya dawo min da yaro na gida lafiya.

"Amin ya Allah" cewar Sayyid yana dariya.

Samha ce tace "wlh sam bana son Yaa Taufeeq ɗin nam ya dawo ya cika takura, Allah yasa yanxu ba anam zai sauƙa ba dan in anan ne wlh tattarawa zanyi na koma gidan Papa dan bazan iya wannam takurar tasa ba. ta ƙarasa maganar ƙwalla na taruwa a idanunta.
Huda ne tace "ai ni tun yanxu zan fara haɗa kayana dan nasan ba makawa a nam zai sauƙa, ni wlh na so Shugaban ƙasa a ko da yaushe ya rinƙa turasa yana wakiltar sa, ya zama kawai shine me zuwa duk wani taro da ake.
Nihal tace "yeee! Yaa Taufeeq zai dawo, saboda ita dai tasan yadda yake janta a jiki su ne dai yake musu abubuwa na azaba kala² dan duk da yarintarta ta fahimci komai, harara Samha ta balla mata tace "ke dama ai dole kiyi murna tunda duk abun da kike so yi miki yake nima ina ma kamarki ce ni da bani da wata matsala wlh rigimata zan nayi son rai na.
Yaa Sayyid ne yace "duk zaku gama ai dama ni sam bakwa jim maganata shiyasa nake ta addu'ar dawowan ɗan uwana yaxo ya cigaba daga inda ya tsaya, su Nabeeha ha ma suna chan suna baƙin ciki da dawowarsa.

Oum ne tace "Kai wannan yaro nawa Allah ya zuba masa farin jini, ta faɗa da alamun tsokana"

"Um su farin jini manya wlh wannam ba farin jini bane tsantsar baƙin jini ne ita tausayawa wanda zata auri miskilin mutum kamar Yaa Taufeeq ga mugunta ga bai son mutane😏 ta faɗa tana murguɗa baki.
Ya Sayyid yace "to ko dai da ke za ayi ne dama Papa yana cewa in ba mu fito da mata ba zai sa ayi wuf! damu, ya faɗa suna saka dariya baki ɗaya.
Zaro ido Huda tayi tare da dafa ƙirjinta tace "na shiga uku! Yaa Sayyid ka rufa min asiri kada a binneni da rai na, wlh ko a mafarki bana fatan nayi mafarki zan auri irin me halin Yaa Taufeeq bare kuma shi da kansa ai na ma haƙura da auren, bari ma kaga tun yanzu na fara haramar haɗa kayana dan wlh gobe²n nam zan bar gidan nam ba sai lokacin dawowarsa yayi ba kar ya mana bazata kamar yadda yawancin yake yi. ta faɗa tana nufar ɗakinsu dan bilhaƙƙi da gaskiya take.
Samha ma meƙewa tayi tace "ai ƙafata ƙafarki Aunty Huda a barin gidan nam.
"Ni kam babu inda zani zan jira Yaa Taufeeq ɗina,cewar Nihal tana kwaɓe fuska.
"Yauwa ɗiyar Albarka rabu dasu su suka sani mu dai muna murna da dawowarsa, cewar Oum.
Nam suka ɓingire da hira ita da Yaa Sayyid.

*★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★*

Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo ganin yadda ake almubazzaranci da abinci, su ko tunanin taya aka samo abincin basayi su dai kawai su banzatar dashi kawai suka sa ni, muryar Shema ce ta katse mata tunanin da ta ke tana cewa "ko dai baza ki girka bane na ɗauki mataki? da sauri ta girgiza kai cikin sanyin murya tace "kiyi haƙuri yanzu zanje na girka.
Daga haka tayi tafiyarta bata ji me suka ce ba sai dariyarsu da taji, tasan kuma maganarta sukayi, tana zuwa ta kwashe jallof ɗin da tayi a food flack's sannam ta ɗaura mata ba jima ta kawo mata ta gyara kitchen ɗin ta ɗibo abincin ta tayi shigewarta ɗaki, cike da tunanin baƙar rayuwar da ta fara a cikin gidan ubanta wanda ko a mafarki bata taɓa mafarkin irin wannan rayuwar ba sai gashi tana riskarsa wanda bata san ƙarshensa ba addu'arta a kullum bata wuce, Allah yasa komai da zai zo mata yazo mata me sauƙi, tana cikin wanna tunanin taji an banko ƙofar da sauri ta kalli ƙofar Mama Marka ne fuskar nam ta ta tamau da ɓacin rai, cikin masifa tace "ke dan uwanki har kin isa su Shema su saka ki abu amma ki ƙiyi ke ga ƴar iska ko? Mamaki ne ya cika ta a zuciyarta tace "me kuma nayi musu? duk abun da suka sakani babu abunda banyi ba, ko dai akwai abun da suka ce na kawo musu ne ban jiba? kafin ta kai ga samun ansa taji wani irin sanyi yana rasa ɓargo da jikinta wani sanyi ne da bai taɓa riskar jikinta Mama Marka ce hannunta ɗauke da plastic tana ƙara kuza mata ruwan sanyi me haɗe da dusar ƙanƙara...'''(Kar dai ku manta akwai zazzafa mai zazzafan salo wanda zai zo muku nam bada jima wa ba akan fara shi me sauƙi'''
*AMRISH AL'IMASH*
'''A rayuwa ko wani bawa da irin ƙaddarar da take zuwa mishi, walau me kyau ko maras kyau, kamar nima hakan ce ta kasance da ni, sai dai ni kash! bana iya babbancewa ta yadda duk wani abu a me kyau nake nake sama masa matsuguni, rayuwa nake kamar ba mutum ba, hakan yasa nake samun kyara da tsangwa ta ko wani fanni hakan yasa mutane suke min kallon anya ni MUTUM ce?)'''
_daga ji kunsan akwai ƙura akwai tirka² ku dai kuyi hanzar motsa aljihunki domin nuna min haƙiƙanin ƙaunar ku a gareni domin ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannam number 08132761212_

*ONE LOVE*💞🤞🏻

TAUFEEƘHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin