Episode 47&48

245 17 2
                                    

*TAUFEEK*
NA
*Hafsat A Garkuwa*

*Episode 47&48*
… Zaune take a falo gaba ɗaya tunda suka haɗuwa da Haseena ranta baya mata daɗi duk da ya sanar da ita basu da wata alaƙa da ita amma taƙi amincewa gani take kamar kawai ƙarya ya mata, "in ƙaryar yayi miki ma ina ruwan ki tunda ba son shi kike ba? wata zuciyar ta tambayeta haka, fashewa tayi da kuka ko za taji sanyi a zuciyarta, da sauri ya fito daga kitchen jin kukanta kallonta yake da mamaki sai kuma ya zauna a musanta tare da sanyata a cikinsa jin haka ta ƙara sake wani kukan cike da damuwa yace 
"Dan Allah Baby kiyi haƙuri duk da nasan bazai wuce akan Haseena kike wannan kukan ba na 'fa sanar dake bani da wata alaƙa da ita kin san dai kuma bazan miki ƙarya ba ki daina wannan kukan ko dan saboda abun da ke cikin ki kinji!
Ya faɗa da alamun rarrashi turo baki tayi tare da harararshi dariya yayi yace
"Oh Ƴar tsana Baby ashe dai ana so ana kaiwa kasuwa ne haka kike da kishi?
Dariya tayi tare da rufe fuskanta da tafukan hannunta tana dariyar ƙasa-ƙasa shima dariyar yayi.
Bayan sun dawo da sati ɗaya ne ya fara fita office tun da ya fara fita yake jinsa wani irin kasancewar Nabeeha bata tare sa shi gaba ɗaya tunaninta ya hanada sukuni shi kansa mamakin sauyawarsa yakeyi wai a yau macen da nafi tsana a duniya ita nake mutuwar so har in bana tare da ita na kasa sukuni wai anya kuwa a da ɗin ma tsanarta nake kuwa ba sonta ne ya jawo tsanar ba? ya tambayi kansa shiyasa ba a son ɗan adam ya dinga fariya ya kuma tsauwala akan baya son mutum domin Allah zai iya jarabtarsa da wani irin so gashi a yau shima Allah ya masa wannan jarabtar dan yana jin Nabeeha a zuciyarsa ba ɗan kaɗan ba musamman in ya tuna da gudan jikinsa da ke jikinta sai ya jisa wani daban,ita kansa Nabeeha tana tsananin son mijinta matuƙar tare da wani irin kishin sa tayi alƙawari za ta fashi duk wani irin kulawar da yake buƙata tare da shimfiɗa nagartacciyar soyayya me cike da farin ciki tare da kafa tarihi cikin jadawalin soyayya, Larai taji dariya da taga Nabeeha sai da ta tuna mata da cewa da tayi ita da Abuja sai sai hanya ta biyo da ita, Nabeeha ma tayi dariya sai yanzu ta tuna da wautar da take yi a baya ta basu tsarabar su tana nan ajiye sa na su Sweetie da masoyinta Ka'aaf.
Tsaye take a kitchen ta rasa me za tayiwa Abwaan ɗinta dan sam ta gaji da sayo musu da yake bacin ita ma ta iya hakan yasa yau tace gwara ta fara musu kawai shima kuɗin sa ya huta dirty rice tace za ta musu hakan ko a kayi gashi kamar haka
Bayan ta tanadi su 
1. Niƙaƙƙen nama
2.Oil
3.Green pepper
4.Albasa, tafarnuwa
5.Rice
6.Spices
7.Salt, maggi
8.Tarugu
  Sai ta ɗaura non stick pot a wuta da ya fata zafi ta zuwa niƙaƙƙen namanya ta zuba mai ɗan kaɗan ta soya shi, sai ta zuba yankakken green pepper ɗinta da niƙaƙƙen tarugu, taci gaba da juyawa har sai da ya koma brown, sannan ta zuba albasarta wadatacce sannan ta zuba spices ɗinta wadda take da shi ta sanyi su maggi da gishiri sai ta ɗan rage wuta, sai ta ɗauko shinkafa ta juye a ciki ta ɗauko ruwan namanta da ta adana ta juye a ciki tana ruwan daɗai wanda zai dafa mata shikafarta ta rufe shi.
Ta haɗa musu lemon kwakwa ta sanya a freezer sannan ta duba dirty rice ɗinta da take ta buga ƙamshi ta samu ta nuna ta ɗauko foodflks me matuƙar kyau ta juye ta gyara ko ita daga kitchen har falo da ɗaukunansu. sannan ta kunna turare dana tsinke tuni gidan ya gauraye da ƙamshi ta nufi ɗakinta tayi wanka ko ina na lungu da saƙo na jikinta sai da ta wanke cike da shaƙi da begen mijinta take komai bayan ta fito ta tsane jikinta ta zauna gaban madubi ta shafa lotion tare da tsantsara kwalliya kao kace wani taro za taje ƙananan kaya ta ɗauko riga da wanda rigan bata iso cibiyarta ba fara ce sol storn ne jere a gaban rigar sai walwali take hannun ta ɗan gajere ne sai wandon da kaɗan ya wuce gwiwa pink ne me ratsin fari tufke gashin kanta tayi bayan ta mulke jikinta da humra sannan ta feshe jikinta da turare masu matuƙar ƙamshi flat ɗin takalmi tasa fari sanya ɗan kunne pink sai ta fito a ƴar tsana Babynta sak ƙarfe biyar ta sauƙo ƙasa taje ta cire key ɗin da ke jikin ƙofar dan ta shiryawa wannan rana a yau tayi alƙawari za su fara gina tsaftacacciyar rayuwa wanda iyayensu za suyi alfahari da su dawo tayi ta zauna a falon ta kunna data tare da shiga Whtspp nan da nan saƙonni suka fara shigowa har da na Abwaan ɗinta duk kalamai ne na irin tsantsar son da yake mata tare da jaddada mata ta kula da kanta tare da abun da ke cikinta cike da so ƙauna, bege, shauƙi take karantawa gaba ɗaya jinta take tana keta hazo tana cikin wannan yanayin ne taji an murza ƙofar falon tare da sallama, da sauri ta ɗago dan sam bataji shigowar motarsa harabar gidan ba.
Yana shigowa yaji wani irin ƙamshi ya daki hancinsa sai da ya lumshe ido domin yana matuƙar son ƙamshi bai ƙara susucewa ba sai da ya hangi Ƴar tsana Babynsa tana nufowa inda yake cikin wani irin salon taku komai na jikinta rawa yake tana zuwa ta faɗa jikinsa cikin wani irin murya da baisan tana da shiga tace Barka da dawowa My Abwaan na godewa Allah sa ya dawo min da kai gida lafiya ba tare da wani abu ya samarmin kai ba ta faɗa tare da hura masa iskar bakinta a kunnensa da sakar masa kiss a kumatunsa.
Ji yayi gaba ɗaya ƙafafuwansa sun gaza ɗaukarsa domin yarinyar ta gama kasheshi da salonta ƙara rungumeta yayi a jikinsa tamkar wani zai ƙwatar masa ita ji yake kamar ya haɗiyeta duk wani gajiya da ɓacin ran da ya taho dasu sai yaji babu su babu labarinsu ɗagata yayi ciɗak ya shigo da ita falon ya fara juyin da ita a tsakar falon aiko nan ta fara dariya ba ƙaƙƙautawa shima dariyar yake gaba ɗaya suka birkita gidan da dariya sai da sukayi me isarsu ya zauna tare da ita a jikinsa cike da ƙauna yace
"Baby ashe haka kika iya tarairaya shine ni bakya min?
Ya faɗa cike da shagwaɓa kamar yadda take masa dariya tayi cike da farinciki domin a yanzu ne zata fara biya abun da Sweetie ta koya mata tare da darasin da ta ɗauka na zaman da tayi a wajen Sweetie yadda suke gudanar da rayuwarsu da Papa hakan yasa ta kuɗira a ranta itama irin rayuwar soyayyan nan za ta gudanar a gidanta sai kuma gashi a yau lokacin yazo dariya tayi tace
"Ba gashi yau na maka ba kuma in-sha-Allahu bazan gaza ba zan cigaba da maka har ƙanshen rayuwata"
Haɗe bakinsu yayi waje guda suka fara musayar yawun bakinsu sai da suka shanye tas sannan suka saki juna yana faɗin 
" I love so so much My wife aud always will. you have filled a space no one could fill I love you more.
Allah ya miki albarka dake da abun da zaki haifa mana da saura masu zuwa.
"Amin ya rabbi"
Ta faɗa cikin sanyi miƙar da ita yayi ya miƙe yace "maza muje ki tayani nayi wanka sai naje na amsa mana abun da za muci.
Ba musu ta miƙe suka nufi ɗakinsa tana ƴar dariya a tare suka yi wanka duk da tasan tayi amma lokacin da yace dole sai ta sake bata masa gardama ba dan da ƙidira a ranta babu faɗi in faɗa tsakaninta da mijinta dan hakan yana ƙara wa juna ƙaunar juna amma mijina na faɗa kema kina faɗa sam babu girmamawa a ciki duk yadda miji yake sonki in kina haka wataran za a wayi gari ya tsaneni.
A tare sukayi wanka suka fito ta shafesa da mai shima ya shafa mata sannan ta ɗauko kasa boxer wanda ta ɗan wuce gwiwansa da singilet kallonta yayi yace
"Kina nufin da waɗan nan kayan zan fita na sayo mana abinci?
Ɓata fuska tayi tace
"Kai kan tunda na ɗauko maka ka saka mana kawai.
"Tom an gama Madam!
Ya faɗa yana dariya tare da sanyawa itama dariyar tayi ta feshe jikinsa da turare kayanta ta mayar domin bata da kaya a ɗakinsa kuma dan yanzu ta sanya su hannunsa ta kama suka fito shi dai binta kawai yake cike da mamaki dinning yaga sun nufa kula ya hango da babban jug tunani ya fara ko su Larai ne suka yi wani abun suka aiko mata dan sun san tana da cike koko dai da wannan tunanin ta zaunar da shi tare da faɗin 
"Abwaan rufe idanunka!
Hararar wasa ya mata yace
"Me za amun da zan rufe idona?
Cike da shagwaɓa tace
"Ayya dan Allah ka rufe kaaaaji!
Hannunsa ya sanya ya rufe fuskarsa yace 
"To na rufe My rigima ta!
A hankali ta zuba musu sannan ta zuba lemon kwakwan da yayi sanyi ca mug ta ɗago tace 
"Buɗe bakin ka!
Taufeeq da tun da yaji waji irin ƙamshin abinci ya bugi hancin sa ya buɗe idanunsa tare da ware hannayensa ta yadda zai iya kallon duk abun da take ba tare da ta sani ba yana kallo ta gama komai tuni ya,haɗiye miyau dan dama yunwa yake ji sosai buɗe idonsa yayi tare da buɗe bakinsa ta sa masa mug ɗin ya kurɓa wani irin daɗi da karɗi yaji ba yau ya saba shan lemon kwakwa ba amma zai iya faɗar bai taɓa shan wanda ya kai wannan daɗi ba sai da ya shanye mug ɗin da ta miƙo masa tass sannan ya zaunar da ita a cinyarsa itama ya zuba mata ya bata a baki ta sha yace 
"Wlh kinfi wannan abun daɗi"
Ya faɗa tare sa nuna mata lemon kwakwan.
Da sauri ta rufe idanunta cike da kunya shiko ko a jikinsa kamar ma bashi yayi maganar ba, ɗibo abincin yayi ya bata sai da taci ta ƙoshi sannan ta basa ci yake yana korawa da lemon kwakwa amma ji yake kamar baya ci tsabar daɗi sai da kusa cinyewa sannan ta barshi tana da dariya shiko sai buga mata santi yake sai da ya gama ya kalleta yace
"Uhm kar kika ina ta santin abincin nan walle kin fisu daɗi duk da tun da nayi ajiya har yanzu an hanani mu gaisa da Babyna kuma nasan yana ta kewar mahaifinta.
Ya faɗa da gasken gaske dan a matuƙar bukace yake kawai yayi alƙawari bazai ƙara tunkararta bace matuƙar ba ita ta kawo kanta ba.
Cike da tausayawa ta kallesa sai yanzu ta gane sam bata masa adalci ba ai ko baya sonta mijinta ne ko kullum dukanta yake dole ta bashi haƙƙinsa amma gashi duk wata kulawa ta duniya yana mata baya son yaga ta wahala bai son ganin ɓacin ranta amma gashi tsawon lokaci ta tauye masa haƙƙinsa sam sai taji babu daɗi ƙima da darajarsa da soyayyarsa sun ƙara ninkuwa a zuciyarta dan tasan in da wani ne ko da ƙarfi sai ya ƙarɓa cike da nadama ta kallesa tace
"Kayi hakuri in-sha-Allah zaku gaisa.
"Allah ya yarda"
Ya bata amsa a taƙaice sai kuma ya tsume ya ɗago ya kalleta yace
"Malama wa ya baki ikon shiga kitchen har ki ɗaura girki me na faɗa miki?
Ita abun ma dariya ya bata sai da ya gama ci yana zuba santi zai biyota da wata magana ta daban ƙunshe dariyarta tayi ganin da gaske yake tace
"Tuba nake ganin tun da mukayi aure baka taɓa cikin girki na bane shiyasa nace bari na zo na maka duk da kace baza ka taɓa cin jagwalwalena ba sai gashi har da santi kayi.
Ta faɗa cike da zolaya da tuna masa abun da ya taɓa ce mata wai bata iya komai ba sai jagwalgwale wa zai ci abincin ta.
Dariya yayi sosai dan shima ya tuna ya kuma gane zolayarsa take kunnenta ya kamo yace
"Wato kema kin iya baƙar magana ko?
"Ba wata baƙar magana kawai ma tuna maka abun da ka manta ne.
"To naji dai kuma bazan yi zuciya ba ko gobe kika yi girki sai naci amma ni dai gaskiya bana so ki wahalarmin da Baby na fa.
A hankali tace
"Sam banga dacewar kana da Mata kana fita sayo abincin ba darajar mace shine tayi girki mijinta ya zauna yaci ya kuma yaba mata ba wai yaje yaji na waje yazo ya yaba musu ba, ina mamakin mata da suke barin mazajensu suna sayo abinci a waje bayan da ransu da kuma lafiyarsu amma tsabar wauta baza su girka ba sai dai a sayo musu mata da yawa mijinsu bai san ɗanɗanon abincin su ba wasu kuma ƴan aiki suke bawa sai dai kaji miji yana cikin abinci yana yawa ba ƴar aiki ƙarshe sai da kiji ya auro miki ita ta ƙara da cewa
"Ni dai ka barni na sabar maka da abinci na bana ƙaunar ko da ruwa ne kasha a waje ba a gidan ka ba.
Cike da ƙauna yake kallonta sai yaji duk duniya yafi kowa dacen samun Mace ta gari sai yanzu yake jinsa yayi aure cikin zolaya yace
"Kenan kina nufin baza a kawo miki ƴar aiki ba?
Hararar wasa ta wurga masa tace 
"Wlh bana so ko zanyi sai dai nayi koyi da Sweetie wacce Ƴar aikin mu dattijuwa ce kuma aikinta bai wuce wanke-wanke ba kaga su Yadikko sun isheni Larai ma so nake in muka zauna na tambayeta ko tana da wanda take so kawai ka aurar da ita tunda kai ne katanta.
Sarai ya gane dan me bata son ƴar aiki yarinya kuma ya san mai yasa tace a aurar da Larai bata san mijinta ya rufe ƙofa ba tunda ya sameta yo ƴan matan da suka amsa sunansu ma bai so ba balle kuma Larai dariya yayi yace
"Oh Baby ina jin daɗin yadda kike nuna kishinki a kaina hakan ne yake ƙaramin ƙaunarki dan ina ƙaunar naga ana kishina ya faɗa cike da farin ciki.
Shagwaɓe fuska tayi tace
"Ni kam ba wani kishin ka da nake yi.
Dariya yayi ya miƙe yana faɗin 
"Ai sai kiyi kuma tashi maza kije kiyi salla gashi an'a ƙira nima masallaci zan je in na fita zan ɗan biya wani guri amma bazan jima ba tare suka haura tayi ɗakinta tare da faɗin 
"Allah ya dawo da kai lafiya.
Ya amsa mata da amin ya shiga ya sauya kayansa ya ɗauro alwala ya fice.
Haka kuwa akayi bai dawo gidan ba sai da yayi sallar i'sha sannan ya shigo a falo ya sameta tana zaune tana chat sai dariya take domin wani grp aka sanyata DOMIN UWAR GIDA wata ce take tambayar ya za tayi ta raba ƴar aikinta da mai gidanta kowa da shawaran da suke bata shine abun ya bata dariya wasu har da zagi suke haɗawa shigowa yayi yana faɗi
"Mai kike gani haka a wayar da yake ta baki dariya?
Ya faɗa yana karɓar wayar ya duba ya ɗan bi chat ɗin shima dariyar yayi ya zauna yana faɗin
"Ga irin wacce kika gama faɗa ɗazu sai ki bata shawara Madam.
Dariya ta kuma yi tace
"Walle ba ruwa na ai bani nace ta ɗauko ƴar aiki ba.
Ledar da ya shigo da ita ya miƙa mata gasasshiyar kaza ce sai ƙamshi take yi yace
"Ga mutumiyarki, ya faɗa yana dariya
Ƙwaɓe fuska tayi dan sai da taji tashin zuciya har ga Allah yanzu san bata son ko ƙamshin kaza taji cikin shagwaɓa tace
"Wlh ni dai Abwaan ba son ko ƙamshin ta Fara nake so na ci"
Ji yayi kamar zaiyi amai da ta ƙira sunan faran ya kalleta da mamaki yace
"Fara kuma Baby? wannan ai za kisa nayi amai.
Kuka ta fara masa tana faɗin "ni wlh fara nake so mai zafi ma.
"Na shiga uku baby ina nasan zanje na samo miki fara kuma?
"Koma ina kaje ni wlh ita nake so aiko nan ta fara rigima ita fara za taci kuma farar ma mai zafi gaba ɗaya ya rasa ya zaiyi da ita yayi rarrashin har ya gaji shi dai har ga Allah bai san in da zai samu ba suna a haka ne Sweetie ta ƙira bayan sun gaisa ne take tambayarsa Nabeeha duk da tana ji kamar ita take kuka, aiko kamar ta sosai masa inda yake masa ƙaiƙayi tace wlh Sweetie gata nan sai rigima take wai ita Fara za taci kuma fararma mai zafi ni kuma ban san inda zan samo wannan ƙazamin abun ba in na samu ma bansan da wanni hannu zan riƙoshi ba dan wlh bana son taɓawa.
Dariya Sweetie tayi sosai dan bata mance lokacin da take da cikin ƴan biyu ba su Nazmar shi take aikawa ya sayo mata in dai ya riƙo farar nan sai yayi ta amai a ƙarsh in ta aike sa sai dai ya bawa Sayyid ya riƙe shirye bazai karɓawa inko ya ganta sai yayi amai tsabar ƙyanƙyaminta da yake cike da tusayin Nabeeha Sweetie tace
"Son kasan cike mai tsarbe-tsarbe yana da matuƙar wahala za ta iya jin gwaɗayin abun da ba lalle a sameshi a inda kuke ba kaga Fara akwaita sosai a kaduna har ɗanye ma ka kawo ta gida ta ɗan kwana biyu har cikin ta ya ɗanyi girma sai ka ɗebi matarka ku dawo in ma tare za kuzo sai ku zo ku sauƙa a gidanka da ke nan ɗin kaga dai ai muna kusa da ku sai tana zuwa tana wuni in ka taso sai ka biyo ka ɗauketa ku wuce ko ya ka gani?



★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★

Cike da farin ciki suka dawo gida dan yadda taga Mahaifiyar Lamir ta nuna bata ganin zata yarda ayi wannan auren sai dai ta wani ɓangaren tanaji ba lalle kuma ta amince da maganar da ta faɗa mata ba amma tana fatan ta amince ɗin domin baza ta taɓa jurar Amatu ace ta aure ɗan Baban mutum ba sai dai ta auri irinta tsintacce, anyi kwana ɗaya, biyu, uku sati ɗaya sati biyu wata qay shiru bataji wani abun da zai sa a ka soke auren Amatullah ba kuma kullum Lamir sai yazo gaba ɗaya zun shiga damuwa daga ita har Ƴaƴanta, haka ma Saif har ga Allah baya son wannan auren na Amatullah ya rasa kuma dalilinsa na hakan gaba ɗaya baya cikin nutsuwar tun Nana tana damuwa har lamarinsan ya dawo bata haushi ma ana haka har ta haihu ta haifi Ƴa ta mace taci sunan Ammy wato Fatima ko da aka tuntuɓeshi da mai za a na ƙiranta yace Amatullah tun daga nan Nana ta fahimci mijinta son Amatullah yake daɗinta ɗaya Amatullah ta kusan aure amma duk da haka sai da ta tsinci kanta da kishin Amatu Allah, Allah take a ɗaura auren Amatullah ko za su nutsu ita da Mijinta.
Saura Sati huɗu biki wani al'amari y faru ba tare da sanin kowa ba ranar laraba da yamma ƙannen mahaifiyar Lamir suka zo ɗaukan kayan auren da suka kawo wa Amatullah tare da faɗin cewar Mahaifiyar Lamir ta fasa auren Momy ji tayi kamar ta zuba ruwa a ƙasa dan daɗi saɓanin Ammy cike da tashin hankali ta kallesu tace
"Mai ya faru haka auren da saura ƴan satikai kuma ace an fasa?
Momy ne ta galla mata harara tace
"Yo mai zai faru kuwa zai wuce suce sun gano yarinyar ba yar gidan nan bane tsintarta akayi? kin san dai zancen duniya ai baya ɓuya ko aj ɓoye sai ya fito fili.
Ammy ne tayi mata wani banzar kallo tace
"Dama muddin akace da irinku a duniya a komai zai iya faruwa.
Ƙanwar Hajiya Rabi ne tace
"Kun ga mu dai ba cece kuce mukazo muji ba cewa mukayi mun zo ɗiban kaya domin mun fasa auren sai kuma a nemi wani amma ba ɗan mu ba.
Momy ne tayi ƴar dariya tace
"Kuna da gaskiya kam bari mu shiga mu kawo muku ki wuce dan dama ba kowa zai amince ba.
Ta faɗa tana nufar ɗakin Ammy dan anan kayan suke.
Cikin ɗaga murya Ammy tace
"Balkisu karki yadda ki kuskura ki shigar min ɗaki.
Turus! Momy tayi tace
"To ai ke sai ki wuce ki basu kayansu ta faɗa tare da wurga mata banzan kallo ta dawo ta zauna cike da farin ciki duk da ta tsammaci in suka zo ɗauka ba tafiya dashi za suyi ba na ɗauka za suce a bawa Raudah domin ita aka zaɓa masa amma sai taji saɓanin haka duk da haka ma nayi farin ciki tun da dai anfasa da waccar tsintacciyar.
Ammy ne ta kallesu tace
"Kuyi haƙuri bari na ƙira Abbansu na sanar da shi duk abun da yace shikenan.
Ɗakinta ta shiga t ɗauki waya ta ƙirasa bugu ɗaya biyu ya ɗauka cike da tashin hankali ta sanar masa ya shiga damuwa sosai amma bai nuna mata ba kawai yace ta barsu su ɗauki kayan gudun rigima in ya dawo zai samu Alhajin yaji mai yake faru.
Haka kuwa akayi ta ƙira Zahra da su Sumy d suke ɗaƙi su tayata fitar da kayan, cike da mamaki Zahra take tambayar ina za a kaisu amma kanzil Ammy bata ce mata suka fito da shi falon gaba ɗaya dan dama basu taɓa komai ba Abba yace baza su taɓa ko ƙyalle ba shi zai musu ɗingi in suka je gidan miji sa ɗinka nan suka rinƙa ɗauka suna kaiwa mota Momy har taya su tayi zuciyarta ƙal…



#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212

TAUFEEƘOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz