Episode 10

268 15 2
                                    

*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO...*✍🏻

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💋 Sa'eed'''

_Wannam shafin gaba ɗaya naku ne *SARAUNIYA HERWIEY* da kuwa *ZARAH ABBA KYARI* walle saboda ku na yi ina matuƙar alfahari da ku ina jin daɗin hot comment ɗinku ina yinku over_✨🌹

*Episode 10*

*...* "Wlh baka ga dogon jawabin da ya dinga yiwa Sayyid akan haka ba, ni dai wlh ban jin son zai amince da wannan maganar" Ajiyar zuciya Papa ya sauƙe sannam yace "Yaya ai ko yaƙi ko ya so aurensa da Nabeeha babu fashi dan sai anyi gwara ma ya bar wannam aƙidarsa ta ƙin auren zumunci. "To Allah dai ya baka ikon cika wannam alƙawarin da ka ɗauka, Allah yasa ya amince ba tare da ankai ruwa rana ba, (ni ko nace wai ku ta Taufeeq kuke kun mance Nabeeha ne da sam bata son haɗa hanya da shi?) Lol.
Sun ɗan taɓa hira kafin daga bisani sukayi sallama akan Oum kar ta yiwa Sayyid magana zai samesa da kansa ya masa bayanin da zai fahimta, da daddare kuwa Papa ya ƙirasa suna zaune a parlon sa, Papa yana kan kujera Sayyid na risine a kan carpet Papa ne ya kallesa a nitse ya fara magana "Sayyid ina so ka saurareni da kunnen basira, kar ka dubi maganata a bai² kayi masa duba na tsanake, Kai Nabeeha da kuma Taufeeq duk ƴayana ne babu bare a cikin ku, ina kuma alfahari da ku, ba komai yasa nake maka wannan maganar ba sai dan share wata ƙura data taso take son bulemu gaba ɗaya, Sayyid! Papa ya ƙara ƙiransa a hankali, Sayyid da tun da Papa yake magana gabansa ke faɗuwa ya ɗago a hankali ya kalli Papan nasu cikin cool voice yace "na'am Papa" "Sayyid ina so ka cire son Nabeeha a zuciyarka ya zamana so na ƴan uwanta ka ne a tsakanin ku, saboda nayi wa mahaifinta alƙawarin zan haɗata da M.T aure in da bamuyi wannam alƙawarin ba da babu abun da zai hanaka auren Nabeeha amma kuma ƙaddara ta riga fata Allah yasa ba itace matarka ba, in sha Allah zaka samu wacce tafi Nabeeha, tun da jimawa na fara zargin kana sonta amma ganin bani da hujja yasa na bar maganar da tun farko hakan ma bazai faru ba zan yiwa tufkar hanci, kayi haƙuri my son. Sayyid da yayi zaman dirshan ya tisa Papa da ido ko ƙiftawa bayayi ya zama kamar mutum-mutumi, tunda Papa ya furta cewa ya cire Nabeeha a zuciyarsa jinsa da ganinsa da kuma hankalinsa suka daina aiki na tsawan mintuwa, gaba ɗaya baya fahimtar me yake cewa. Papa ganin yadda Sayyid yayi kamar ma baya jin me yake faɗa, da ɗan ƙarfi yace "are you okay Sayyid" da hanzari ya ɗagowa yace "sure Papa, but ni dai gani nake kamar in aka haɗasu kamar akwai matsala Papa duba da yadda sam basa jituwa kuma shi baya son auren zumunci, kamar dai baza su jitu ba gaskiya" Murmushi Papa yayi yace "kar ka damu son ko suna son junansu ko basa so dole na cika wannam alƙawarin, in yaso daga baya gaba ɗaya su koyi son junansu, kai ma ka fito da wata pls son sai a haɗa bikin baki ɗaya, murmushin ƙarfin hali yayi yace "a'a Papa ni kam kuma ba yanzu ba sai kuma wani lokacin in Allah yasa muna da rai da lafiya ya faɗa yana furzar da iska, "sorry son" Papa ya faɗa cike da tausayinsa sai yanxu yake jin haushin jinkirin da yayi na rashin auren tun da wuri saboda ƙarancin shekarun ta da kuma yanayin aikin M.T amma yanzu kam dole ayi a gama, Sayyid ne ya katse masa zancen zucin da yake yace "Papa zan wuce sai da safe Allah yasa haka shine mafi alheri. "Amin son Allah ya maka albarka.
Da ƙyar yake iya ɗaga ƙafarsa saboda nauyin da take masa ga wani irin duhu da yake gani, babu kowa a parlon har zai fita yaji muryar Nabeeha tana faɗin "Yaa Sayyid yaushe kazo? juyawa yayi yaga har ta iso inda yake, kallonta yayi da idanunsa wanda suka sauya kala yayi murmushin ƙarfin hali ya juya ya wuce ba tare da yace mata uffan ba, mamaki ne ya kamata ta jima tana tsaye tana kallonsa har ya ɓace daga ganinta, baki ta turo sannam ta juya ta koma ciki dafatan Allah yasa lafiya.
Yana isa gida Oum ya gani zaune a parlor tana kallon tv a hankali ya ƙarasa inda take zubewa yayi a gabanta ya fashe da matsanancin kuka me ban tausayi kamar ƙaramin yaro, hankalin Oum in yayi dubu sai da ya tashi, domin tun lokacin mutuwar mahaifinsu bata sake ganin kukan ɗanta ba sa a wannan lokacin, da sauri ta kamosa ta zaunar dashi kusanta kansa yana kan cinyarta,tana ɗan bubbuga kansa da alamun rarrashi, cikin kuka yake faɗin "ashe Oum Nabeeha ba itace za ta kasance uwar ƴaƴana ba, ashe duk shirin da nake ba ita bace zata kasance tawa ba ta har'abada ba, ashe ta ɗan uwana ce" Cike da tausayin ɗan nata Oum tace "kayi haƙurin son Allah yayi ba kai ne mijinta ba ɗan uwanka ne, me zai sa baza ka rungumi ƙaddarar da tazo maka ba, kar ka mance kowa a duniyar nam, rabonsa yake ci baya cin rabon wani kayin haƙuri Allah zai musanya ma da wacce ta fita. "A'a Oum bazan taɓa samun wacce ta fita ba" "My son kar ka fidda ƙauna daga rahamar ubangiji in sha Allah zaka samu wacce ta fita, haka Oum tayi ta bashi baki da nasihu a haka har ya saduda suka koma wata hirar amma a ransa ya gama yanke hukunci ƙasar zai bari dan bazai iya zama yana kallon Nabeeha a matsayin matar ɗan uwansa ba.
Washegari kuwa ba tare da sanin kowa ba ya tarkata duk wani abu nasa me mafani ya ɗaga birnin London sai da yayi wanka ya hutu ya ƙira mahaifiyarsa ya shaida mata inda ya tafi saboda kar hankalinta ya tashi, ya ƙara da cewa "Pls Oum kar kice in dawo wlh bazan iya zaman Kaduna ina kallon Nabeeha ba kimin rai" Murmushi Oum tayi tace "na maka rai My son dan ita kanta ta tausayawa yaron nata, nasiha tayi ta masa akan ya kula da addininsa da kuma lafiyarsa kar yasa abun a ransa, yace "in sha Allah duk da yasan abu ne mawuyaci ya iya cire abun a ransa amma ya ma ta alƙawarin zai kwatanta haka,sun jima suna waya kafin yayi mata sallama.
Papa ne zaune shi da Sweetie bayan ya gama shaida ma ta abun da yake faruwa daga farko har ƙarshe ya ƙara da cewa "ni dai yanxu bana son auren nam ya ɗau lokaci tunda kin ga irin abun da yake faru gaba ba a sam me zai faru ba" Ajiyar zuciya Sweetie ta sauƙe tace "ikon Allah! Allah ɗaya gari bam²
To yanzu Papa'n su anya haɗin nam zai yiwu kuwa? duba da yadda naga sam babu jituwa a tsakaninsu kamar da matsalafa ni nasan halin son kar yaje ya cutar musu da ƴa mu shiga uku fa, Papa yace "in sha Allahu babu abun da zai faru sai alheri duk da nima ina tunanin haka amma mu bisu da addu'a kawai ina ga hakan yafi. "To Allah yasa a dace, Allah kuma ya nuna mana lokacin biki ai ni nafi kowa farin ciki akan wannan haɗin kawai tsoro na yadda basa jituwa ne. Cewar Sweetie tana murmushi, Papa ne ya jawota jikinsa yana faɗin "nima kin manta auren zumunci mukayi? dan haka ki kwantar da hankalin ki babu abun da zai faru, fuskarta ta rufe tana ƴar dariya da alamun kunya Lol.

TAUFEEƘOnde histórias criam vida. Descubra agora