Episode 41&42

230 20 2
                                    

*TAUFEEK*
NA
*Hafsat A Garkuwa*
_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*
*Episode 41&42*
… "Yau nice na ke ɗauke da cikin wanda baya sona wanda yake min tsana mafi muni wai nice da cikin sa a jikina! 
Ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani irin kuka me ban tausayi.
Ruɗu, mamaki, tausayi, kunya a tare suka ziyarci Taufeeq dake zaune kamar hoto yana kallonta gaba ɗaya jikinsa yayi matuƙar sanyi bai taɓa tunanin hakan daga garetan ba, sai yanzu yake tuna duk wani irin tsana da yake mata, sai yanzu yake jin kunyar abun da ya mata, ya sani bai cancanci ta haihu da shi ba saboda tsanar da yake mata amma kuma yanzu dolen ta ta haifa masa abun sa cikin dauriya ya ce
"Nabeeha….!
Da sauri ta katse sa ta hanyar ɗaga masa hannu alamar kar yace mata komai cikin kuka tace
"Yaa Taufeeq ka sani na sani ba sona kake ba taya zan haihu da kai? ya zama dole a yau kuma a yanzu a zubar da wannan cikin dan bazan taɓa iya haihuwa da kai ba kuma…
Cikin tsawa yace
"Ke! ashe baki da hankali nan sani ba? cikin nawa kike faɗar a zubar ɗana gudan jini na? to wlh in mafarki kike ki farka, dan ko da wasa wani abu ya samu cikin nan za kisha mamaki na a lokacin za ki ga asalin waye ni a lokacin za kiyi ladamar abun da kika aikata.
Wani irin kuka ta fashe da shir ta miƙe tana bubbuga ƙafa kamar ƙaramar yarinya da hasken gaske take faɗin
"Wlh ni kam bana son cikin nan sai na zubar da shi, ni dai bazan haihu da kao ba.
Ganin fa da gaske take ne yasa da sauri ya kamota don kar ta masa asara yana ji yana gani dan wannan buga ƙafar da take in tazo da tsautsayi sai cikin ya iya zubewa, haɗata da jikinsa yayi yana ɗan bubbuga bayanta alamun rarrashi cikin sanyin murya yace
"Wa ya faɗa miki bana sonki? duk wanda ya faɗa miki ya miki ƙarya, Ƴar tsana baby ni kaina ban san a yaushe ne na fara sonki ba amma ina miki wani irin so da baki na bazai iya furta shi ba kin kasance Macen da murmushinta ke haska duhun dare, macen da sautin muryarta ke sanya nutsuwa a zuciyata kin samar da farin-ciki a cikin zuciyata, kin zamo ɗaya tilo da babu kamar ta a cikin duniyata, kece kika kaini duniyar da ban taɓa tsammanin zuwanta ba gashi a yau kin bani babban kyautar da ban san da me zan biya ki ba, wannan zancen da nake miki daga cikin zuciyata take fitowa.
Ya faɗa yana me hura mata iska a wuyanta
Nabeeha tun da ya fara magana taji wani irin daɗi da shauƙi suna huɗa ƙasusuwanta suna shiga sai taji ta a wata duniya ta daban cikin gajimare tuni ta mance ɓacin dan da take ciki wani irin farin ciki maras misaltuwa ne ke ziyartar zuciyarta a hankali ta ɗago tace
"Abwaan wai da gaske kake kana sona?
Ƙayataccen murmushi ya mata tare da kama kumatun ya ɗan ja tare da faɗin
"Ai dole na so Ƴar tsana babyna ko dan shagwaɓanta da madarar da take ba ni.
Dariya tayi tare da rufe fuskanta alamun kunya tace
"Tabbas ba kowa bane ake faɗa wa sirrin zuciya sai mai cikar matsayi da cancanta kuma wanda ya dace, babu komai a cikin tawa zuciyar nima sai kai.
Hannunta ya kama wanda ta rufe fuskanta ya janye tare da faɗin
"Ashe dai Ƴar tsana babyna ta iya soyayya kamar kin san ko irin macen da nake fatan samu kenan.
Ya faɗa tare da hura mata iskar bakinsa akan fuskarta.
Da sauri ta buɗe ido cike da mamaki wai yau Abwaan ɗin ta ne suke hira da shi ba tare da ya haɗe mata fuska ba, ta wani ɓangaren kuma son sa da ƙaunarsa ne ke ƙara shiga zuciyarta.
A hankali tace 
"Abwaan yunwa nake ji!
Kallonta yayi yace 
"Sorry bari yanzu za mu wuce dan dama jira nake drip ɗin ya ƙare sai mu tafi za ki iya tafi ko na ɗagaki?
Da sauri ta rufe fuskanta tana dariya tace
"A'a zan iya mu je!
Tare suka jero yana riƙe da hannunta suka har harabar asibitin Osim yana ganin fitowarsu yazo yana gai dasu tare da yi mata sannu backseat suka shiga basu wani yi tafiya ba suka iso san basu da wani nisa,sai da ya sanar wa da Osim ya musu order sannan ya rike hannunta suka tafi, suna shiga ta zauna a kujera tana maida numfashi dan yunwa take ji sosai kamar taci babu kallonta yayi cike da kulawa yace
"Me yake damunki?
Cikin shagwaɓa tace "to ba yunwa nake ji ba.
"Baki ga na sa Osim ya kawo mana ba wannan Babyn ya gano Oum ɗinsa kenan, ya faɗa cike da zolaya
Kamar za tayi kuka tace
"Babu wani ai ni bana ci da yawa kawai shi yake sani ci.
Zai bata amsa sukaji ana danka bell tashi yayi ya bude Osim ne ya risina ya miƙa masa ya rufe ƙofar ya juyo, ajiye mata yayi yace 
"To gashi acici kar dai a cinye bari na watsa ruwa na zo.
Da "tom ta amsa masa tare da sauƙowa ta fara ci...

TAUFEEƘWhere stories live. Discover now