Episode 7

235 14 2
                                    

*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO...*✍🏻

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💋 Sa'eed'''

*Wan da suka ƙira ni da wanda suka min text da masu min magana ta whatsApp ina godiya sosai da addu'arki gareni Allah Ubangiji ya saka da alheri na gode da kulawarku sosai musamman TAUFEEƘ FAN'S GRP 2 na gode sosai Allah ya ƙara mana lafiya baki ɗaya, Hafsat Jiboota😘 ina yinki irin sosai ɗin nam ke ɗin ta daban ce a waje na.*🤞🏻

'''My fan's ina matuƙar godiya a gareku dan gane da yadda kuka amshi wannam labari hannu biyu, banyi tunanin zai karɓu haka ba, na gode sosai da nuna ƙaunar ku gareni Allah ya bar zumunci kuyi ta suburbuɗo comments nima bazan yi ƙasa a gwiwa ba wajen zaɓaɓɓako typing.😹'''
*One love Mutane na*🤞🏻💞

*Episode 07*

*...* Tun lokacin da ta zuba ƙara Sweetie ta fito a guje cike da tsoro da farga ba, turus! tayi ganin yadda Yaa Taufeeq yake ta zuba mata mari, ita kanta sai da tsikar jikinta ya tashi domin ko bata san yadda dukan ɗan nata yake ba tana jin labari tun yana yaro hannunsa yana da matuƙar zafi musannam ma da hagu dan da hagu yake mari, sai da ya nufi ɗakin sannam ta iso, Nabeeha tun tana iya kuka har ta koma na zuci,tuni fuskarta ta tashi abun ka da ba saban ba kuma jiki ɗan hutu, fuskar tayi raɗo² na shatin hannunsa a take wani zazzaɓi ya dirar mata, Sweetie ne tazo ta kamata tana faɗin "wai me tayi masa ne hak?
Nam Samha cikin kuka ta faɗi mata komai, ranta ne ya ɗan sosu ai tunda ta riga tayi marin bai kamata ya mareta ba.
Sannu Nabeeha kiyi haƙuri ki barni dashi in yazo sai na tsaɓa masa maza ku tashi kuje kuyi sallah kunji har an idar.
Miƙe wa tayi tana tangaɗi dan sam bata ganin gabanta sosai Huda ne ta kamata suka shiga ɗakin su, toilet ta faɗa a daddafe tayi wanka ta ɗauro alwala bayan tayi salla ne ta kwanta tuni zazzaɓin ya sake rufeta me matuƙar zafi numfashi take fitarwa cikik azaba, kan kace me ta fara sambatu, Samha ne ta sanarwa Sweetie da hanzari ta shigo ɗakin tsoro ne ya cikata ganin abun sa ƴar mutane take kamar zata mutu a fili tace "na shiga uku Taufeeq zai kashe musu ƴa!
Hawa gadon tayi ta kamota da sauri ta ɗage hanunta jin yadda jikinta yayi matuƙar zafi kamar wuta, Tsoro ne ya ƙara shigarta dan tasan dole akan sai ta faru saboda tun da take ba a taɓa lafiyar jikin ta haka ba, ɗakin ta ta haura ta ɗauko mata maganin zazzaɓi da ruwa, ta tada ta sha, sannam ta komar ta ta kwanta tana mata sannu, ba jimawa bacci ya ɗauketa domin har da na bacci Sweetie ta haɗo mata, zuwa jimawa jiki dai ya kuma rikicewa dole tasa Papa yace maza su tafi asibiti, suna zuwa aka bata gado ruwa aka sa mata tuni ta saku bacci, Sweetie ne a ɗaki da Papa da kuma Huda da Samha, Nazmar, Taufeeq, da Jawaad duk basu san me ke faru ba sai da Papa ya sanar da su ba jimawa sai ga su Jawaad dan shi yafi kowa damuwa, sarkin miskilaye kuma da aka sanar masa shi haushi ta fashi ma tsabar tsakalci ɗan dukan da na mata ne har zata kwanta a asibiti ai ko in dai haka ne na dinga naɗarta kenam in yaso ta zama ƴar Hospital,tun da aka gaya masa abun da yake ta faɗa kenam.
Sai bayan i'sha sannam ya iso asibitin nam ma sai da Papa ya masa da gaske tukun na, yanzu ɗakin Sweetie ne kawai dan duk ta kora su gida dan kwana ya kama su saboda yana yin jikin nata bai mata da sauƙi ba, har yanzu bata samu ta farka ba saka makon maganin da suka sa a cikin ruwan na sa bacci yana da ƙarfi, Sanye yake da blue ɗin shadda wacce ta amshi fatarsa ɗinkin tazarce sai baza fitinannam ƙamshi yake, gaishe da Sweetie yayi bai ko kalli in da gadonta yake ba bare ya tambayi ya jikin nata, Sweetie ne tace "ka ga yanda ka mai da musu da ɗiya ko? kai baka san yadda hannunka yake da zafi bane? ta jero masa tambayoyin cikin faɗa, cikin sanyin muryar sa yace "Sweetie naga yarinyar ta cika rawar kai ne shi yasa na gwada mata nawa salon dan tasan ni ba amin iskanci da tsiwa dan naga hakan tattare da ita.
"Koma dai miye ka kiyayi taɓa musu lafiyar yarinya.
"Tom" ya faɗa a taƙaice.
Motsi ta fara a hankali da sauri Sweetie ta miƙe dan sanarwa likita dan ya faɗa musu cewar tana farkawa a kirasa, fita tayi tana faɗin "ka zauna a wajenta bari na ƙira likita, bata tsaya jin amsarsa ba tuni ta fice.
A hankali ta fara buɗe idanunta da take jin sun mata nauyi sosai tar ta buɗe su a kansa dake zaune a ɗaya kujerar da ke ɗakin yana danne danne a wayarsa, a zabure ta miƙe tana ƙare ware idanunta, leƙe² ta fara kamar wanda take neman wani abu, tuni idanunta suka cika da ƙwalla, gani tayi kamar wani marin yazo ƙara mata, tuni ta fashe da kuka, kukan da yaji tana yi ne ya da ɗa ɓata masa rai a hankali ya miƙe yazo in da take, cike da tsawa yace "ke! bana son shashancin banza, uban me aka miki da zaki cikawa mutane da banzan kukanki, bari kiji ni bana ɗaukar raini dan haka tuni ki kama kanki dan naga yana rawa in ba haka ba kuma ni zan daidaita miki zama banza kawai.
Daga haka yaja dogon tsaki yayi waje, dan sam ko kaɗan yarinyar Baffan nasa bata masa ba, ko kallonta yayi ransa ɓaci yake, duk da hakan ba halin sa bane ƙin jininsa amma ita sam jinin nasu bai haɗu ba, (Niko nace dama kai akwai wanda jininka ya haɗu da nasu ne, ai sai dai su Ali🤣) Kiciɓus sukayi da Sweetie da doctor baya ya komai domin ya basu hanyar da zasu shigo, Sweetie ne tace "ya zaka fita ka bar min ita kai da na baka ajiyarta.
Kayin sa ya sosa yace "zan ɗan amsa waya ne"
Wuce wa kawai tayi dan ta fahimci ƙarya yayi mata, doctor ne ya sake dubata ya tambayi me take ji yanzu, "kai na ke ciwo sosai kamar ana saramin da adda ta faɗa kamar za tayi kuka hakan yasa ya sake ɗaura mata wani ruwan take ta sake komawa bacci, Sweetie zama tayi tayi jigum tana kallonta tausayinta ya ɗaga kamata, yana fita suka bar hospital ɗin, gida suka nufa yana shiga bai taras da kowa a palor'n ba part ɗinsa ya nufa ya sake wanka yasa kayan bacci yayi kwanciyarsa hankali kwance.
Tun da su Samha suka dawo take neman hanyar da zata bar gidan amma ta rasa, Aunty Sa'a ta ƙira ta sanar da ita akan ta ƙira Yaa Taufeeq tace tana son ganinta, dariya tayi musu sosai tace Allah shi ƙara da ya sauka a chan kuma ita ba ruwanta tayi ƙit! ta kashe ƙiran ganin sun dameta da ƙiran ma ta kashe wayar gaba ɗaya.
Jawaad yafi kowa shiga damuwa akan rashin lafiyar Nabeeha sosai yake jin haushi Yaa M.T dan wani sa'in haka suke ƙiransa, Yaa Sayyid da aka gaya masa bai ji daɗi ba dan sai da ya nunawa Taufeeq ɓacin ransa amma shi ko a jikinsa.
Washegari tun safe su Samha suka gama komai suka haɗa nasu Sweetie a basket haka na Taufeeq ma dana Papa kame² suka fara ta yadda zasu sanarwa Taufeeq tafiyarsu asibiti, dan sun san in suka tafi basu sanar masa ba nam ma laifi ne, gashi kuma tsoron zuwa ta dashi suke dan sun san hakana laifi ne dole suka nemi waje suka zauna, sai wajen 10 sannam ya fito sai baza ƙamshi yake, a tare suka gaidasa Huda ne tace Yaa Taufeeq dama zaman jiranka muke zamu sanar maka zamuje hospital kaiwa su Sweetie abinci.
Kamar bazai yi magana ba dan har yakai ƙofar fita sai kuma yace "babu inda zakuje ku kawo min basket ɗin cikin mota, ya faɗa ba tare da ya juyo ba ya fice.
Babu yadda suka iya dole suka kai masa suka juyo Samha kamar za tayi kuka dam ba haka taso ba taso in ta tafi Momynta tazo ta bita ta gudu ko Yaa Sayyid.
Da Sallam ya shiga cikin ɗakin da suken Sweetie nr a ɗakin dai Aunty Sa'a da Yaa Sayyid dasu Nazmar, gaba ɗaya suka amsa masa ya shigo tare da ɗaya yaronsa dake riƙe da basket ɗin abincin, rusunawa yayi ya gaida Aunty Sa'a da Sweetie sannam suka gaisa da Yaa Sayyid su Nazmar suka gaidashi, kallon gadon da Nabeeha take yayi ya ganta zaune kamar batayi ciwo ba azuciyarsa yace "munafuka dama ai lafiyarki ƙalau ciwon munafirci ne kin sa mutane jelan asibiti haka kawai wlh sai na miki hukuncin zuwa asibiti da kika sa nayi ta jele.
A fili kuma ya furta "Sweetie ga breakfast ɗin ku I hope za mu iya tafi ko?
"Eh za mu iya tafi dan sun bamu sallama dama zaman jiran ta muke ta gama shan tea sai mu tafi, sai kuma gaka, ƙara kallonta yayi karaf suka haɗa ido ba zato ba tsammani ta rafka masa wani harara wanda bata san yaushe yayi karam banin suɓucewa ba, ido ya zaro alamun "ni kike harara, kansa ya girgiza sannam ya kalli Sweetie yace "ku tashi mu tafi kawai ai ina tunanin ta kammala, waje ya fita nam suka fito suma suka nufi gida gaba ɗayan su.

*★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★*

Sai da ya tsotsi bakin sa son ransa duk yakushin sa da take amma a banza sai da ya bari dan kansa, kuka ta fashe dashi tana faɗin "meye haka Yaya Sadiq? ka mance ni ƙanwarka ce? wallahi kar ka ƙaramin irin wannam abun in ba haka ba kuma zanje na sanarwa su Baffa wannam ai iskanci ne. ta faɗa cike da ɓacin rai.
Murmushi yayi yana jan sajensa yace "Yarinya kenam kinji daɗi zaki wani lauye da kukan munafurci, zancen zaki gayawa Baffa kin jima baki faɗa ba, ai sai ki bari nayi me gaba ɗaya sannam ki sanar da shi but yanzu yayi wuri. ya faɗi yana fashe mata da dariya yayi waje abun sa.
Mamaki ya bata batayi tunanin zai mata haka ba, addu'a take ta yi na Allah ya tsareta daga sharrin sa duk da bata gane cewar da yayi, ta bari yayi me gaba ɗaya ba, Tun daka wannam lokacin suke kurun ɓoye dashi, da ya zo waje zata bar wajen ko ta tafi tun kan yazo, wahala kuma kullum cikinsa take baya raguwa sai dai ya ƙaru gaba ɗaya ta fige tayi baƙi tayi wani iri da ita, makaranta kuwa tuni su Baffa suka hanata zuwa sai ƴaƴan su, dole ta haƙura dan tasan bata da matallafi, yau ma kamar kullum zaune take a ɗakinta ta gama girki kenam ta shigo da nata tana ci, kamar daga sama ta gansa a kanta tsaye yana mata wani shu'umin murmushi, gaban ta ne ya faɗi da sauri ta mike ta ɗauki mayafi ta yafa a jikinta ganin yadda idonsa yake yawo a jikinta, murmushi ya sakar mata ya matso inda take yana faɗin "haba ƴar baby na meye kuma na firgita haka? ki dai na wani tsoro na ki saki jiki dani, zan zame miki gata na har'abada, ya ƙarisa faɗin haka yana isa gareta tare da riƙe hannunta, fuske hannunta tayi tace "haba Yaya Sadiq wannam wani irin abu kake min haka karfa ka manta ni ƙanwarka ce kai ma so kake na fara tsoron ka kamar yadda nake tsoron ƴan gidan? ta faɗa hawaye na sulalowa daga idanunta.
Murmushi yayi yace "ko ɗaya abar ƙaunata kiyi haƙuri ki daina kuka bazan miki komai ba bari naje na samu su Baffa su fara maganar auren mu kawai.
Daga haka yayi waje ta bishi da idanu cike da mamaki, gado ta faɗa ta saki wani marayan kuka na tausayin kanta.'''(Kar dai ku manta akwai zazzafa mai zazzafan salo wanda zai zo muki nam nada jima wa ba akan fara shi me sauƙi'''
*AMRISH AL'IMASH*
'''A rayuwa ko wani bawa da irin ƙaddarar da take zuwa mishi, walau me kyau ko maras kyau, kamar nima hakan ce ta kasance da ni, sai dai ni kash! bana iya babbancewa ta yadda duk wani abu a me kyau nake nake sama masa matsuguni, rayuwa nake kamar ba mutum ba, hakan yasa nake samun kyara da tsangwa ta ko wani fanni hakan yasa mutane suke min kallon anya ni MUTUM ce?)'''
_daga ji kunsan akwai ƙura akwai tirka² ku dai kuyi hanzar motsa aljihunki domin nuna min haƙiƙanin ƙaunar ku a gareni domin ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannam number 08132761212_

*ONE LOVE*💞🤞🏻

TAUFEEƘOnde histórias criam vida. Descubra agora