Episode 71&72

133 8 0
                                    


*TAUFEEƘ* 
NA 
_Hafsat A Garkuwa_ 
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 
_(Domin Marubuta Mata)_ 
           ✨W.W.A✍🏻 
https://www.facebook.com/Women-Writers-Asso-106752595253176/

Episode 71&72 
…. Yana shiga bedroom ɗinsa yaji wasu hawaye masu matuƙar zafi da ƙuna d'un fara sintiri akan kyakkyawar fuskarsa dafe kansa yayi yana faɗin 
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Allahumma a jirni fi musibati wa'akilni khairan minhan!! Kiyi haƙuri Baby na hakan shine mafita a gare ni da ku baki ɗaya… 
A hankali ta turo ƙofan bakinta ɗauke da sallama idanun nan nata yayi matuƙar ja ya kumbura kana kallonta kasan ta ci kuka ba kaɗan ba tana zuwa ta sanya gwiwowinta a ƙasa cikin kuka tace 
"Abwaan! Don Allah in har na magana wani abu ne wanda baka ji daɗinsa ba dan girman Allah kayi haƙuri ka yafe min na tuba bazan iya rayuwa kana fushi da ni ba wlh bazan jura ba Abwaan na tuba." 
Ta ƙarisa maganar tana fashewa da wani irin kuka na ban tausaya 
Tun da ta fara magana yaji gaba ɗaya kansa ya masa wani irin mugun sarawa ji yayi kamar ya jawota ya sanyata a jikinsa ya rarrashe ta amma ina lokacin hakan ya ƙore masa sam bazai iya ba ji yake duk wani sauti na kukanta kamar ana buga masa guduma a tsakar ka jarumta ya aro ya haɗe fuskar nan kamar hadiri yace 
"Ke za ki tashi ki ɓace min da gani ne ko sai na saɓa miki kamanni wlh Nabeeha kika sake zuwa inda nake sai na ba ki mamaki tashi ban waje ko na bigeki wlh." 
Ya ƙarasa maganar yana jin kansa kamar zai tsage. 
Ciki da mamaki tsoro da kuma fargaba ta ɗago tana kallonsa a zuciyarta tana faɗin 
"Anga kuwa wannan Abwaan ɗina ne? 
Cikin kuka ta miƙe da ƙyar ta zuba masa ido ganin kallon da take masa ne yasa yayi saurin rufe idanunsa yana jin wani irin bugun zuciya a hankali ta fice tana jin wani irin jiri na iɗbarta gaba ɗaya ji take duniyar gaba ɗaya tayi mata zafi ji tayi tama gaji da rayuwar duniyar ina ma za faɗi ta mutu a yanzu dan baza ta iya rayuwa a haka tare da shi, ɗakinta ta tafi da ƙyar a ƙasa ta zauna tana sakin wani irin narayan kuka ta jima a haka gashi sam ba ta so ta sanarwa kowa sirrin gidan ta bata jin za ta iya sanarwa kowa sai dai in ma kasheta zaiyi ya kasheta amma san baza ta buɗe baki ta sanarwa kowa ba, wayarta ne ya fara kuwa a hankali ta sa hannu ta ɗauka ganin Sweetie ne yasa taji wasu hawaye ya zubo mata ɗaga tayi tana ƙoƙarin danne damuwar ta gaisawa sukayi kana ta ƙara da cewa 
"Nabeeha lafiya kuwa kwana biyu ina ƙiran son amma baya ɗaga min ko ya ɗauka ma baya wata magana sai dai yace ya gaji da safe zai ƙiran daga haka bazai ƙira ba sai na ƙirasa gaba ɗaya ya sauya 'fa sosai anya kuwa lafiya?" 
Wani kuka taji ya tokare ta da sauri ta sa hannu ta rufe bakinta da ƙyar ta samu ta maida kukan tace 
"Lafiya ƙalau Sweetie kawai kwana biyun nan aiki ne suka masa yauwa kullum sai ya fita yanzu haka ma fa har yayi bacci babu wata matsala." 
Ajiyar zuciya Sweetie ta sauƙe wanda har Nabeeha sai da ta jiyo cike da hamdala tace 
"To shikenan Allah ya muku albarka Allah ya sauƙe ki lafiya in ya tashi kice ina gaida shi." 
"Amin ya rabbi Sweetie mun gode, tom san faɗa masa sai da safe." 
A haka sukayi sallama tagumi tayi wani kukan ya sake zuwa mata sabo fil! sai da ta gaji don kanta ta miƙe ta ɗauro alwala duk da nauyin da cikin ta yake haka tayi ta sallah tana kaiwa Allah kukanta. 
Washe gari kamar yadda ta saba tun da tayi salla ta fito ta gyara ko ina ta shiga kicin abinci marar nauyi ta girka musu ta jeresu sannan ta nufi ɗakinta tayi wanka ta shirya cikin atamfa ɗinkin doguwar riga dan yanzu ba ko wani kaya ne yake mata ba a hankali ta fito direct ɗakinsa ta nufa duk da tana jin zuciyarta yana wani irin bugawa da sallama a bakinta ta shiga zaune ta sameshi yana aiki a system ɗinsa risinawa tayi cike da tausayin kanta tace 
"Abwaan ina kwana! 
A hankali ya ɗago ya kalleta ji yayi tayi mugun bashi tausayi da sauri ya daina kallonta bai kuma amsa ba ya cigaba da abun da yake. 
Nabeeha ganin kamar bai jita ba ne yasa ta ɗan ɗaga murya ta sake gaishe shi. 
A hassale cikin harshen turanci yace  
"Dahalla tashi ki fice min daga ɗaki ba nace kar ki sake zuwa inda nake ba ne kam?" 
Jikinta na rawa hawaye na biyu ɗan uwansa tace 
"Don girman Allah Abwaan ko ma mai na maka kayi hakuri ka yafemin ka dai na horani wlh bazan iya jurar hakan ba dan Allah kayi haƙuri ga chan breakfast yana jiranka." 
"To naji ta shi ki barmin ɗaki." 
Cikin kuka tace 
"Tom! Na gode miƙewa tayi da ƙyar ta fice a ɗakin zuciyarta kamar za ta fito daga ƙirjinta zama tayi a falon duk yunwar da take ji sai taji a yanzu sam babu ita tana nan zauna taga ya fito cikin shirin fita sai baza ƙamshi yake ko kallon inda take ba ma yasa kai har zai fita ya ciro damin kuɗi ya ajiye mata ya fice, da idanu kawai take binsa tuni hawaye sun cike fuskarta kuka take kamar ranta zai fita faɗi take 
"Abwaan mai na maka da zafi haka? Taya za ka dinga wahalar da zuciyata kamar baka da imani? Anya kuwa da ɗin ma kana so na? Wannan wani irin zalunci kake min haka? Wayyoo Allah na ka cire mu daga cikin wannan SARƘAƘIYA (na Hafsat A Garkuwa yana nan tafe) Allah ka dube mu da idon rahma! Abwaan ya sauya min ban san mai na masa ba tun da muke tare shaƙuwa ci da sassanyar ƙauna da zaman lafiya ke wanzuwa cikin rayuwar mu, amma gashi a ƴan kwanakin nan yana ƙoƙarin kifa mu da ƙasa." 
Tun daga wannan ranar haka suke rayuwa baya kulata ba ya kuma cin abincinta sai da a kullum zai ajiye mata damin kuɗi tare da duk abun da za ta buƙata gaba ɗaya ta fice a haiyacinta yi baƙi ta rame, a ɓangaransa ma gaba ɗaya ya fita rama dan sam baya cin abinci sai ruwan liptoa su Sweetie ma a yanzu baya sake musu kamar da duk da yana kula da su yadda ya kamata a yanzu cikin Nabeeha ya shiga wata tara cikin ya sake tolele tana tafiya cikin zaka fara hangowa kafin ita Sweetie tayi tayi ya dawo da ita yace sam bazai yiwu ba dole tasa Sweetie ta tattaro tazo, ta sha mamaki sosai yadda ta gansu gaba ɗaya sun sauya ko da ta tambayi Nabeeha ce mata tayi ba komai dan tayi alƙawari ko namanta yake yankawa yake gasawa ya ci baza ta sanarwa kowa rayuwar da suke ciki ba sai Allah n da ya halicce su a kullum za ta kai talatenin dare tana kaiwa Allah kukan ta. 
Zaune take a ɗakin ta gaba ɗaya tun safe take jin gabanta na faɗuwa Sweetie ta shigo duk ta fice hayyacinta tace  
"Nabeeha Taufeek ne yake ta aman… Sai kuma tayi shiru tunawa da lalurar da ke tattare da ita tace 
"Taufeek ne ba lafiya an kaisa asibiti bari naje na gani yanzu zan dawo in naga jikin da sauƙi zuwa safiya kuma sai muje tare da ke." 
Ai zambar ta miƙe ta ɗauki mayafi tace 
"Sweetie dan girman Allah ki bari mu tafi tare ko kin barni a nan bazan samu nutsuwa ba wlh." 
Ba yadda Sweetie ta iya dole suka fito suka tafi tare, basu wani tafiya sosai ba suka iso katafaren asibitin ko da suka iso basu samu ganinsa ba saboda ana bashi taimakon gaggawa zama sukayi tun Nabeeha na tsumayin fitowar su har tq karaya wasu hawaye masu zafi suka fara sintiri akan fuskarta Sweetie ma da take daurewa sai da tayi ƙwalla sai ƙarfe 11 na dare suka fito fuskar sunan duk ta kachame da gumi da sauri Papa yayi wajen su wanda basu jin da zuwa ba har su Anti Sa'a abun ka da masu naira office ɗin Papa yayi Dr. Bayan sun zauna ne Papa yake tambayar Dr. Meye matsalar son ɗinsa nan Dr. ya gyara zama yace 
"I'm so sorry Alhaji a iya binciken mu mun gano blood cancer ne yake damun ɗanka kuma yana stage na karshe da babu abun da za mu iya masa sai yadda Allah yayi sam ba a taɓa mata magani ba hakan yasa taci ta cinye shi tas duk da bata bayyana ba amma nasan dole za ta nuna masa alama, sai dai kuma Alhaji kar ku karaya akwai wani ƙwararran likita da ke London zai zo nan a gobe zai iya dubashi ko zai iya masa aiki a wannan stage ɗin in akayi sa'a sai kuga an dace amma gaskiya yana cikin matsanancin hali duk da binciken mu ya nuna yana ɗan shan sigari duk da ba wai itace ba amma shan sigarin ma ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa ciwon." 
Papa cike da mamaki tsoro fargaba ya zauna tamkar mutum mutumi yana kallon Dr. Gaba ɗaya ji yayi duniyar tana wani irin juya masa gumi ta ko ina tsatstsafo masa take cike da tashin hankali yace 
"Blood cancer!! 
"Ya Allah! 
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun son ke ɗauke da blood cancer?" 
"Kayi haƙuri Alhaji abun da binciken mu ya nin kenan." 
"Amma likita kana da tabbaci gobe Dr. Zai zo in bazai zo ba gwara na ɗauke shi na fita da shi." 
"Kar ka damu Alhaji insha Allahu gobe zai sauƙa da safe kuma a asibitin nan zai fara sauƙa in-sha Allahu yallaɓo shi za a fara dubawa da izinin ubangiji zai samu lafiya." 
"To Allah yasa hakan Dr." 
"Amin ya Allah. 
Fitowa Papa yayi jikinsa duk a mace hayaniya ce take tashi na ɗumbin jama'ar da suka zo duba Taufeek babu masaƙa tsinke tuni gidan radio da TV sun watsa bashi da lafiya saboda a wajen meeting ya faɗi yana aman jini babu yadda ba ayi,ba akan su tafi amma sunƙi addu'a suke tayi na Allah ya bashi lafiya Nabeeha tayi kukan har ta gode wa Allah.  
Ko da Papa ya iso ganin yadda jikinsa ke mace ne ya ƙara kashe musu jiki Nabeeha ta kuma fashewa da kuka Sweetie ne tayi ƙarfin halin tambayarsa me likita yace. 
Ƙaƙalo murmushi Papa yayi yace 
"Yace jikinsa da sauƙi kar ki damu." 
Ya faɗi haka ne dan yasan in ya faɗa musu gaskiya sai sun shiga damuwa fiye da wanda suke ciki ɗakin da aka kaishi suka shiga kwance yake kamar gawa baya ko motsi oxygen ɗaure a hancin sa yayi wani irin fayau ya rame fuskar nan tasa tayi wasai sai sheƙi take yi  
Nabeeha ta ƙora masa idanu ko ƙyaftawa batayi babu mai cewa ɗan uwansa kanzil har wajen ƙarfe ɗaya Dr. Yazo yace su fita amma sam Nabeeha taƙi dole aka barta ta kwana da shi su kuma suka tafi gida ba don sun so ba sai dan haka dokar asibitin take jama'a dake waje kuma sam sunƙi tafiya sai ma ƙaruwa da suke yi. 
A hankali Nabeeha ta ƙaraso gabansa ta zauna a kujerar dake gefen gadon sa hannunsa ta ɗauka ta ɗaura a wuyanta ta kwanta a jikinsa a tare suka sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya sai a yanzu taji hankalin ta ya kwanta duk da ba ta san mai yake damun Abwaan ɗin ta ba amma ganin Papa bai faɗa musu ba tasan ba wani ciwo ba ne mai zafi a haka bacci ya ɗauketa. 
Cikin bacci taji ana shafa kanta a hankali ta ɗago suka haɗa ido ya sakar mata sqssanyar murmushi itama murmushin ta mayar masa cike da ɗoki dan rabun da yayi mata murmushi har ta manta cikin sanyin murya tace 
"Abwaan ya jikin naka? 
"Da sauƙi Baby na ya babyn mu fatan duk suna lafiya? 
Shagwaɓe fuska tayi kamar za tayi kuka tace 
"Bayan ka manta da mu baka kulamu baka zuwa in da muke." 
Murmushi yayi cikin sanyin muryar marar lafiya yace 
"Baby baza ki gane ba ne amma dai nasan yau komai ya zo ƙarshe ina neman yafiyar abun da na miki duk da ina da dalilin da yasa na miki haka amma sai bayan ba na nan za ki san dalilina duk da nasan ba lallai abun da nayi yasa abun da nake gudu qin faruwa ba ina roƙon ki da ki yafe min baby na." 
Cikin rashin fahimtar inda zancen shi ya dosa tace  
"Ni ba ka min komai ba Abwaan Allah ya baka lafiya mu komai gida abun mu." 
Murmushi yayi tare da girgiza kai a zuciyar sa yace 
"Ai ni da gidan nan kuma har'abada sai dai in gawata." 
Likita ne yazo ya duba shi ya gansa ras kamar,ba shi ke jinya ba hakan yasa ya cire masa na'urorin da taimakon Dr. Yaje yayo alwala itama tayi shi ya ja su salla sannan suka haye gado ɗaya ya rungumeta tsam a jikinsa sukayi bacci Nabeeha ji take duk wani damuwarta na duniya ya kau bata da wani sauran damuwa tun da Abwaan ɗinta ya bar fushi da ita. 
A haka su Sweetie suka zo suka taddasu rungume da juna sunyi farinciki sosai jin samun sauƙin sa hayaniyar su ne ya tadda nan suka fara gaisawa da tambayarsa jiki Nabeeha suka zubawa abinci domin shi bazai ci komai ba dan yanzu za su shiga tiyata karɓa tayi ta ɗan lakita ta barshi. 
Dr. Yazo yace za a shiga tiyata yanzu gaba ɗaya mamaki ne ya kama ƴan ɗakin har Taufeek Papa ne yace 
"Masha Allah! Allah yasa ayi cikin nasara." 
Da mamaki Taufeek ya kalli Papa yace  
"Papa tiyata kuma? Don Allah kar ma a soma ko anyi ko ba ayi ba tafiya ta zaman wajibi a gareni kar a ɓatawa likita lokaci akwai masu bukatar tiyata da yawa ba saura ba dan Allah mu bari." 
Gaba ɗaya ƴan ɗakin jikinsu yayi sanyi har Papa domin Papa bai san Taufeek yasan yana da blood cancer ba yaso har sai an dace sannan ya sanarwa kowa. 
Sweetie ne cikin tashin hankali tace 
"Wai ni kam akan me kuke ta magana ne ban 'fa gane ba." 
Papa ne ya sanar da su komai ya manta sha ɗaf da Nabeeha tana wajen sai jin ƙaranta kawai sukayi ta zube ƙasa sumammiya! 
da sauri Taufeek ya tallafeta ta faɗa jikinsa cike da tashin hankali yak jijjgata gaba ɗaya ya fice a hayyacin sa su Samha tu ni sun fara kuka Sweetie da Anti Sa'a ne suka ɗauketa suka kaita ɗakin da likita ya ke nuna musu Taufeek kuwa cikin umurnin Papa aka fara shirin yi masa aiki gaba ɗaya hankalin sa na wajen matarsa har sai da yaji ta farka lafiya hankalin sa ya kwanta sannan suka shiga. 
Sun shafe awa 3 sannan suka fito da shi kwance kamar gawa sai dai kuma aikin yayi kyau saura a jira tashin sa, Nabeeha tana chan an hanata zuwa sai da ya shafe awa 1 sannan ya fara buɗe ido a hankali yana sakin murmushi ganin ahalinsa tsaye a kansa cikin sanyin murya yace 
"A ƙira min baby don Allah a ƙiramin Baby! 
Anti Sa'a ne ta kawota tana zuwa ta faɗa jikinsa ta saki wani irin marayan kuka murmushi yayi yace 
"Baby kece? Baby na so na rayu da ke amma ba dama, mutuwa zan yi ina roƙonki da ki yafe min duk abun da na miki nasan na ɓata miki sosai kin kuma yi haƙuri ba ki nuna gazawarki akan hakan ba tabbas ke ɗin ƴar aljanna ce Allah ubangiji ya miki albarka. 
Cikin kuka tace 
"Abwaan baza ka mutu yanzu ba in sha Allahu mutuwar ka ba nan kusa ba ka dai na faɗar haka don Allah!
Murmushi ya sake mata tare da ƙara riƙe hannunta yace
"Baby ina so ko bayan ba raina ki kulamin da kan ki da kuma abun da zaki haifa mana ku rayu cikin farin ciki."
Sai kuma ya kalli Papa da murmushi akan kyakkyawan fuskar shi yace
"Papa kazo kusa da ni don Allah!
A hankali Papa ya ƙaraso jikinsa a matuƙar sanyaye zai yi magana suka ji hayaniya na tashi
Shugaban ƙasa ne ya shigo da tawagar sa mutane kamar tsaki duk ƙusosi ne a mutunci suka gaisa gaba ɗayan da tambayar ya mai jiki ba su wani jima ba suka tafi bayan aun ajiye musu tulin kuɗi da kayan dubiya duk da su Papa basu da buƙatar kuɗi domin sun tara amma sun nuna murnan su ainin suna fita Taufeeƙ ya kamo hannun Papa da na Sweetie yana sakar musu murmushi
"Don Allah ku yafe min abun da na muku tun ina yaro har izuwa yanzu."
Sweetie ne cikin kuka tace 
"Wai me ye haka kake Taufeek duk kana karyar mana da gwiwa fa."
Murmushi yayi yace
"Karki damu Sweetie na ki yafe min don Allah."
"Na yafe maka Son duk da ni dai baka taɓa,min laifi ba."
Papa ne yace
"In-sha Allahu za ka samu lafiya na yafe maka duniya da lahira."
Wani sanyi yaji tun daga kan yatsan ƙafarsa har izuwa tsakar kansa, nan yayi ta roƙon yafiyar su har ƙannansa yace
"Za kuga ina takura wa rayuwar ku ba dan komai nake haka ba sai dan naga gobenku yayi kyau ko bayan bana nan ina roƙon ku da kada ki sauya a yadda na sanku ku cigaba da yiwa iyayen mu biyayya."
Da gudu suka iso garesa tare da sakin kuka suna faɗin
"In-sha-Allahu Hamma ka dai na faɗar haka tare za mu rayu har ƙarshen rayuwar mu."
Murmushi ya kumayi ya shafo kan Nabeeha da take ta kuka kamar ranta zai fita yace
"Baby ki dai na kuka kinji ko?
"Kina so nayi fushi da ke ne?
Da sauri ta girgiza kai alamar a'a.
"To ki sharw hawayenki ki dai na kuka kinji!
Da sauri ta goge hawayenta tace
"Na bari Abwaan!
Ahankali ya fara ƙoƙarin tashi ganin haka ta taimaka masa Papa yace 
"Ina zaka!
"Papa ban biya sallolin da ake bi na ba.
Da taimakon Nabeeha yayi alwala ta shinfiɗa masa darduma ya tada salla cikin raka'ar ƙarshe yayi sujjada tun da yayi bai kuma motsi ba har kusan na minti goma ganin haka ne yasa Papa isa garesa ya taɓasa kawai sai yaga ya ɓingire ya faɗi.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajioun! 
Shine kawai abun da gaba ɗaya ƴan ɗakin suke faɗa cikin dauriya Papa ya taɓo shi ya fara taɓa shi duk wajen da yasan zai ji alamun rai a tattare da shi babu shi komai ya saya chak! rai yayi halinsa Inna lillahi wa'inna ilaihi rajioun…

TAUFEEƘWhere stories live. Discover now