Episode 15&16

199 17 0
                                    

*TAUFEEƘ*

NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO…*✍🏻

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul 💋'''

_My fan's kuyi haƙuri da rashin jina kwana biyu hakan ya faru ne saka makon wasu dalilai, amma yanzu dai Alhmdllh ga ni na dawo za mu ɗaura daga in da muka tsaya fatan dai kun shirya bani daddaɗan comment? to a kafta!🤾🏻‍♀_

*Episode 15&16*

*...* Sun sauƙa Dubai lafiya Amatullah wani irin iska me daɗi da ƙamshi take shaƙa, sam sai taji iskar duniyar da ta baro da wanda take ciki sunsha bam² tuni motocin Alhaji Tahir sun iso Yaron sa Saif ne yazo ɗaukan su da mamaki yake kallon Amatullah da ta gaishe shi, sannam suka ranƙaya gida "hasbunallahu wani'imal wakin" gidan Alhaji Tahir anguwa ce guda me zaman kanta, gida ne me girma wanda ya amsa sunansa gida, tsayawa fasalta muku yadda gidan yake ma ɓata lokaci ne masu karatu ku ƙiyasta shi a mizanin fahimtar ku, parlon gidan suka nufa Alhaji Tahir yana gaba Amatullah tana bin sa a baya, su na shiga wasu ƴan mata wanda sa'annin Amatullah ne suka yiyo kan Alhaji Tahir cike da farincikin dawowar sa, suna zuwa suka faɗa jikinsa suna faɗin "sannu da dawowa Abba ya hanya?" "lafiya ƙalau my Ɗaughter's fatan dai na sameku lafiya?
"Lafiya lau Abba"
"To masha Allah, Allah ya muku albarka ya faɗa yana shafa kansu jerowa sukayi suka shigo falon, duk abunda suke Amatullah tana kallon su wani abu ne ya tsaya mata a rai sun burgeta sosai, hawaye tuni ya cika mata ido tunowa da tayi da mahaifinta mafi soyiwa a gareta, Abba ne yace "Raudah! Zarah! baku ga da baƙuwa nake ba, ya faɗa yana nuna musu Amatullah da ta rakuɓe a gefe, ya ƙara da faɗin "Daughter tashi ki zauna a sama mana ki daina zama a ƙasa nam gidan ku ne.
Tashi tayi ta zauna tace "na gode Abba"
Zarah ne ta kalleta cike da fara'a tace "sannunki da zuwa"
"Yauwa na gode"
Ta bata amsa a taƙaice, Raudah ne ta mata wani banzan kallo ta dauke kai ba tare da tace komai ba, Abba ya ganta sarai kansa ya girgiza ya juya wajen matansa da suke fitowa suna masa sannu da zuwa Hajiya Fatima itace uwar gida mutumiyar kirkice faran-faran take da mutane kowa nata ne yaranta uku Saif shine babba sai Habiba dake aure a London sai kuma Zarah da autarta Ruƙayya saɓanin Hajiya Balkisu bata da mutunci ko kaɗan ta tsani wani ya raɓe su tafi son komai daga ita sai ƴaƴanta, ko su Hajiya Fatima ta rasa yadda za tayi da su ne shiyasa ta bari har yanxu take zaune a gidan yaranta uku ita ma ita suka gado duk abunda suke cikin tarbiyarta ne Raudah sai kuma Shamsiyya
cike da farinciki suka iso parlon Hajiya Fatima ne ta kalli Amatullah cike da fara'a tace "Abbansu da baƙuwa kuka zo ashe? sannu da zuwa baƙuwa Zarah maza kuje ɗakin ku tayi wanka sai ta fito taci abinci.
Cike da girmamawa Amatullah ta gaidasu Hajiya Fatima ne kawai ta amsa saɓanin Hajiya Balkisu da ta mata banzan kallo kamar yadda ɗiyarta Raudah ta mata, Amatu ganin kamar Hajiya Balkisu bata ji gaisuwar bane yasa tace "Mama ina kwana?
Wani tsawa Hajiya Balkisu ta mata tace "ke dahalla dakata min ban san ko ke waye ba ki ƙirani da wata Mama kul ko da wasa kama kanki"
Zarah ne tazo ta kama hannunta tace "Sis tashi mu shiga ciki kiyi wanka"
"Tom" tace a taƙaice suka tafi
Hajiya Balkisu ne ta wurga mata wani harara tana faɗin "haka kawai ba a tsaya anji waye ita ba kuma daga ina ta fito ba har an fara janta a jiki a jawo mana masifa tsabar gwaninta tayiwa mutum yawa, ta faɗa tana wurgawa Hajiya Fatima harara, murmushi Hajiya Fatima tayi tace "ai hakan shine girmamawa kuma shine karamci, nasan dai duk abun da me gidana ya shigo dashi har muhallin iyalansa nasan ba ƙaramin muhimmanci ne da shi a gunsa kinga dole mace ta gari ta ɗauki abun da muhimmanci
Ke komai ma da ya fito daga wajen me gidana me muhimmanci na ɗaukesa, kuma a ko ina ana so ka girmama baƙonka saboda baƙonka annabi ah to!
Taɓe baki Hajiya Balkisu tayi tace "kya dai ji dashi a rage shishshigi dan Allah..."
Abba ne ya wurga mata wani kallo wanda yasa tasha jinin jikinta, Hajiya Fatima ne tayi gaba ya bita a baya domin ɗakinta yake yau, da tsaki Hajiya Balkisu ta rakasu ta kalli Raudah da ke zaune tana kallonsu dan haka mahaifiyarta ta koya mata duk abun da ake kar ta yarda ta bar wajen har sai taga ƙarshen abun.

TAUFEEƘDonde viven las historias. Descúbrelo ahora