Episode 45&46

220 28 4
                                    

*TAUFEEK*
NA
*Hafsat A Garkuwa*
_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*
*Episode 45&46*
… Juyi yake ta yi akan kujeran dake office ɗinsa idonsa a lumshe ba dan yana jin bacci ba sai dan tsananin ɓacin ran da ke addabar zuciyarsa tun lokacin da ya baro Amaa da Lamir gaba ɗaya ya rasa nutsuwarsa sai yanzu yaji da ma ya korata gida sai dai duk abun da zai faru ya faru, iska ya furzar a bakinsa me zafi ya miƙe  yanufi freezer ruwa ya ɗauko me matuƙar sanyi ya sanya a bakinsa sai da ya sha fiye da rabi sannan ya ajiye, ya ɗan ji zuciyarsa tayi sanyi kaɗan ba ta sake gaba ɗaya.
Amaa kuwa tun da ta hangi Yaa Saif ji tayi kamar ƙasa ta tsage ta shige take ji tsabar kunyarsa da take ji har lokacin da ya bar wajen da sauri tayi sallama da Lamir bata jira amsar sa ba tayi cikin gidan da sauri hada haɗawa da gudu murmushi Lamir yayi kawai ya shiga motansa ya tafi cike da farin ciki.
Tun daga wannan ranar kullum Lamir sai yazo Abba ne ya mata magana akan in tana son shi ya turo magabatansa duk da Baban Lamir abokin Abba amma bazai yi abu gaba gaɗi ba.
Tana sanar da shi kuwa cikin kwana biyu suka iso aka kammala magana aka tsaida biki nan da wata biyar tare da na Zarah za ayi tun da Mom taji ta kasa zaune ta kasa tsaye hanyar da zata warware auren ya koma kan ƴarta ko kuma a fasa gaba ɗaya kawai take nema a ƙarshe ta samu mafita guda ɗaya ai cike da ɗoki da farinciki ta shirya tare da Raudah suka nufi gidan su Lamir.
Saif kuwa da yaji haka gadan gadan ya nufo Abba cike da damu yana zuwa ya samu Abba zauna a falonsa bayan sun gaisa yace 
"Abba bai kamata a aurar da Amaa tun yanzu ba kar ka manta 'fa karatu take yi sannan ya kamata a san wani nata ko guda ɗaya ne kuma…
Da sauri Abba ya dakatar dashi tare da ɗaga masa hannu yana murmushi dan tun ba yau ba ya gama gane take-taken ɗan nasa 
"Saif ka mance me Amaa ta faɗa mana ne bata da kowa 'fa haka zalika in ban aurar da ita ba me zan mata karatu kuma ko a gidanta zata iya ƙarasasu dan haka ka bar wannan maganar kawai da addu'a za mu bi su gaba ɗaya Allah ya basu zaman lafiya.
Jiki a sanyaye ya baro part ɗin Abbansu gate ya nufa domin bazai iya zuwa wa Nana a haka ba dan dama ta kasa gane kansa a ƴan kwanakin nan gaba ɗaya ta tada hankalinta, bata san hankalin yafi tashi fiye da nasa ba shirye kansa bai san meke damunsa sa amma san baya ƙaunar yaga Amaa tare da wani wa namiji ji yake kamar zuciyarsa za ta caso daga ƙirjinsa.
Suna isa a falo suka tarar da mahaifiyar Lamir babbar macece kamar Ammy cikin shiga ta alfarma da fara'a ta karɓesu duk da basa wani shiri da Mom sun fi shiri da Ammy bayan sun gaisa ne Mom ta kalli Hajira Rabi cike da gulma da munafunci tace
"Hajiya Rabi kin san ko me yake tafe da ni?
"A'a sai kin faɗa Hajiya Balki!
"Uhum gani nayi Hajiya Rabi kuna ƙoƙarin faɗawa halaka
"Subhanallahi Halaka kuma Hajiya Balki?
Hajiya Rabi ta faɗa cike da mamaki.
"Eh mana halaka mana kina ji kina gani za kisa yaronki ya auri ƴar tsuntuwa wacce ba a san danginta ba wa ya sani ma ko cikin shege akayi aka haifeta.
Ciki da ƙosawa da maganar Hajiya Rabi tace 
"Wani irin magana kike Hajiya Balki nan 'fa gane inda maganarki ta dosa ba.
"Yo taya zaki gane tun da an rufe miki ance miki Yarinyar da Lamir zai aura Ƴar Fatima ce,ti bari kiji ba ƴar kowa bace wannan tsintacciya ce, Abbansu ne ya tsintota a chan wani gari ya kawo mana ita wlh ni har yanzu ban gama aminta da ita ba kina kallonta ma za kiga zubinta na karuwa kuma aj tambayeta danginta tace bata da kowa, taya za ayi ace baka da kowa a duniya sai kace daga sama ka faɗo ba haifarka akai ba.
Ciki da mamaki Hajiya Rabi take kallonta tace "Kina nufin yarinyar nan Amatullah ba ɗiyar Hajiya Fatima bace shine Alhaji yace min ɗiyarta ce?
Ganin Hajiya Rabi ta fara ɗaukar maganan ne Mom ta gyara zama ta inda take shiga ba ta nan take fita ba duk wani maganar da tasan zata ruguza auren sai da ta faɗawa Hajiya Rabi ta ƙara da cewa
"In banda yarinta ma irin na Lamir ga yara a gidan masu asali irin na su Raudah ya zaɓi ɗaya a cikin su mana.
Ta faɗa tana nuna Raudah da take ta yauƙi kamar wata karkashi.
Hajiya Rabi tace 
"Na gode sosai Hajiya Balki Allah ya saka miki da alheri in sha Allah in dai haka maganarki take auren nan babu shi anyi an gama wlh ni duk ɗauka na a cikin yaran Hajiya Fatima ne tunda yaranta biyu ƴan mata.
A haka Hajiya Balki suka yi sallama ranta fes ganin haƙarta zai cimma ruwa, cikin raɗa tace "dan Allah Hajiya kar kice nice na faɗa miki.ta amsa mata da to kawai.

★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★
"Shegiya mayya kawai ya faɗa a hankali dan bai son Nabeeha ta ji da mamaki take kallonsa dan ta jisa sarai tace
"Abwaan ka santa ne?
Da sauri ya ɗago ya kalleta san ba ɗabi'arsa ce ƙarya ba hakan yasa a hankali yace
"Eh na santa sunanta Haseenah.
Ya faɗa a taƙaice taɓe baki kawai tayi a haka Haseenah ta iso wajen tana wani yauƙi da karairaya tace
"Pls ki ɗan ba mu waje za mu ɗanyi magana.
Kallonta Nabeeha tayi har za tayi magana sai kuma kawai ta maida maganar tata ta wuce ta basu waje motar da aka zo ɗaukarsu ta shiga ta yima direban magana a fusace tace
"Malam wuce ka kai ni gida.
Da mamaki diraban ya juyo yana faɗin "Yallaɓan fa?
"In ka kaini sai ka dawo ka ɗauke shi ko ya shiga motar masu jiniyoyin chan ai nasa.
Bai mata musu ba yana suka bar wajen tana jin zuciyarta kamar zata fashe dan baƙin ciki

Taufeeq cike da mamaki yake kallon Nabeeha gaba ɗaya ransa yaji ya ɓaci wato ita bata son da za ta barwa wata shi dole ya tsaya tunda wacce yake karewa kansa ba ta damu da shi ba,tsayawan da yayi bai sai ya sakewa Haseenah na cikin ɓacin rai

"Uwar me zan miki da za kizo cikin jama'a kina ƙwallamin ƙira? bance duk inda kika ganni matuƙar bani na buƙaci zuwanki ba kar kizo inda nake? ke wacce kalar jarababbiya ce wawiya kawai.

Tunda ya fara maganar take ƙwalla dan Allah ya ɗora mata son Taufeeq tun suna school ita kanta bayin kanta bane cikin kuka tace

"Dan Allah kayi hakuri na ganka ne sai kuma na kasa nutsur da kaina har yasa na maka magana amma pls Dear ka jiƙaina ka amshi muradina.

Wani banzan kallo ya mata ganin ƴan jarida suna shirin taruwa ne yasa yayi saurin barin ta a wajen ya nufi mota tana tsaye tana kuka har suka wuce.

A falo ya tadda Nabeeha idanunta nan yayi ja kana kallonta za ka gane taci kuka har ta gaji murmushi yayi ya zauna a kusa da ita tare da kamo hannunta ya sanya a bakinsa yana hura mata iskar bakin cikin yatsunta

"Baby shine kika taho kika bar mata ni ko wato in ma gwaɗani za tayi ke ba ruwanki ko? duk irin nuna miki son da nake miki amma kin kasa yarda da hakan me yasa bakya kishi na Baby? Ya faɗa cike da zolaya.

Harara ta galla masa ta yadda bazai ganta ba amma bata san ya gantan ba a zuciyarta tace

"In da kasan me naji a lokacin baza ka faɗi haka ba. A fili kuwa tace

"To ni ina ruwana da kai me ya shafeni da kai da zanyi kishinka?

Dariya yayi tare da lakutan hancinta ya ɗagata yana faɗin

"Eh naji bakya kishina tashi muje muyi wanka mu huta gajiya.

Ba musu ta miƙe suka shiga ko ina fes dan a kullum sai Larai tazo ta gyara wanka sukayi a tare suka fito tare da ɗauro alwala suka rama sallan da ake binsu kwanciya sukayi rungume da juna duk da tana jin yunwa amma baza ta iya cin komai ba saboda ɓacin ran da take ji dan har yanzu zuciyarta batayi sanyi ba wani kishinsa ne yake ƙara nunkuwa a zuciyarta sai yanzu take nadamar barin su a wajen har ya fara bacci yaji tana faɗin

"Meye haɗin ka da wannan karuwar?

Yi yayi kamar bai jita ba sai kawai yaji ta fashe da kuka da sauri ya ɗagota yana faɗin

"Haba Baby me yasa za ki wahalar min da kanki wajen zubar da hawayenki ki da kika ce bakya kishina me zai dameki?

Turo baki tayi tace

"Ko ma dai miye ai ni matarka ce ya kamata nasan wace ita.

"To naji ki kwanta ki huta in muka tashi zan faɗami miki pls ya faɗa yana shafo cikinta yana jin sonta da kuma ƙaunar abun da zata haifa masa, in ya tuma ya kusa zama Baba ji yake kamar yafi kowa farin ciki a duniya dan yana matuƙar son Ƴaƴa balle kuma ace daga tsatsonsa ya fito, a haka ya samu tayi bacci. *Pls kuyi haƙuri da wannan kuyi manage soyayyar da kuke nunamin ne yasa na ɗan muku wannan ina ƙaunarku my fan's*

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212

TAUFEEƘOnde histórias criam vida. Descubra agora