Episode 25&26

195 9 2
                                    

*TAUFEEK*

NA

*Hafsat A Garkuwa*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*Episode 25&26*

*...* front seat ya buɗe mata kamar baza ta shiga ba sai da Zarah ta ɗan mintsine ta sannan ta shiga su kuma suka shiga back seat, cike da murna ya zagaya ya shiga driver seat yaja suka fice a makarantar
Raudah kunya duk ta rufeta ji tayi ina ma kasa zata tsaye da babu abun da zai hana ta shiga ta rufe da ita tsabar kunyan da take ji, Ruky ne ta yafa mata gyalen da ta cirewa Amatu sannan ta kama hannunta suka nufi inda motar gidan su take dan su Amatu suna fita shi kuma ya shigo murmushi kawai take zubawa dan ita kaɗai tasan abun da zata ƙulla musu, tuni Shamsiyya ta shiga suma shiga sukayi ganin drivern baya da niyar tafiya ne yasa cikin gadara Raudah tace
"Wai mai ya tsayar dakai haka ne ko mu bayin ka ne da zaka shanya mu?
Murmushi yayi dan ya jima sa sanin halinta juyowa yayi yana kallonta yace
"Kin san bazai yiwu na tafi na bar sauran ƴan uwanki a nan ba dole sai na jira sun fito.

  Dariya tayi sannan tace "ni bani da wasu ƴan uwa ga ƴar uwata nan My Ruky ta faɗa taba rungumar Ruky a jikinta tana dariya.
Girgiza kai kawai Shamsiyya yayi tace "kaga kawai mu tafi dan su sun tafi ƙila ma yanzu suna cikin gida.
Kallonta yayi yace "in muka tafi ba matsala ko?
"Eh ba matsalan komai ta bashi amsa.
Hakan yasa yaja motar suka wuce.

Wani katafaren eartry suka je wanda babu me zuwa sai ɗan wane da wane, zama sukayi su huɗu, sannan kowa aka kawo masa abun da yake so Amatullah samosa kawai tace a kawo mata sai drinks bata wani ci sosai ba saboda yadda Akunta ya zuba mata idanu suna kammalawa ya biya suka fice a wajen, mota suka shiga ya kalli Amatu dake gefen sa yace "ranki shi daɗi a wace anguwa suke, kamar baza tayi magana ba ta sanar dashi yaja motar suka tafi, suna tafiya yana zuba mata surutu but taƙi amsa masa sai Zarah ne da Kausar suka shiga cikin hirar, sun ɗan yi tafi sannan suka iso, mamaki ne ya kamasa ganin ƙofar gidan su abokinsa Saif suka iso, da mamaki ya jiyo yana faɗin "wai kuna nufin ku sister Saif ne.

Da mamaki Zarah take kallonsa tana faɗin "a ina kasan Yaya Saif?
Murmushi yayi yana faɗin ai aboki na nane tare mukayi karatu.

Da mamaki tace "to school din mu da kake zuwa fa, murmushi yayi sannan yace abun sirri ne tare da kanne mata ido ɗaya, horn yayi mai gadi ya wangale masa gate ya kutsa motarsa, yana gama parking Amatu kamar jira take ta fice fit! suma fitowa sukayi suna fadin mun gode Zarah tace
"Amma baka faɗa mana sunanka ba"
"Sunana Lamir ku gaida min da su Ammi wataran dai zan shigo a domin mu gaisa.
"Za taji suna shiga falo suka ga mutane cirko-cirko ana bazo musu ido

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Taufeeƙ yazo zai wuce ɗakinsa yaji abu ya faɗi dim! da sauri ya nufi ɗakin kwance ya ganta a ƙasa ganin ko motsi ba tayi yasan suma tayi dan shi kansa yasan wannan aikin ya mata yawa ganin ba sabawa tayi ba, ruwa me mugun sanyi yazo ya watsa mata tsabar mugunta, kamar an tsikareta ta miƙe, harara ya balla mata tare da faɗin
"Tsabar asaranci ɗan wannan aikin ne wai ya baki wahala har kika wani suma, tsabar sangarci,  mtsww yaja tsaki ya wuce a wajen.
Wani irin kuka ne yazo mata wanda bata tsammaci zuwansa ba, ji take zuciyarta kamar zata buga ji take baza ta juri wulaƙancinsa ba tun ba aje ko ina ba, ace amarya tun daren aurenta ta fara fuskantar wulaƙanci kuka taci sosai sannan ta miƙe a daddafe tayi bathroom ta haɗawa kanta ruwa me zafi tayi wanka hakan yasa ta ɗanji dama-dama, mai kawai ta shafa ta zira kayan bacci ta haura gado nan da nan baccin wahala ya ɗauketa.

  Tun daga wannan rana kullum cikin wannan aikin take na rana daban na dare daban, tuni ta ɗan sauya kana kallonta kasan tana aikin wahala,ga ta gefen sa da yake jifanta da muggan kalamai babu halin ramawa dan yanzu zai haɗa mata gajiya, dan akwai ranar da tayi hakan sai da ya fasa mata jiki da maruka, ta rasa wani irin tsana yake mata, ta kuma rasa me tayi masa yasa yake mata irin wannan tsanar, kuma san bata so ta sanarwa iyayensa halin da take ciki dan tasa za su iya samun matsala duba da yadda suke nuna mata ƙauna tamkar su suka haifeta, yau ma kamar kullum ta gama aiki ta gyara ko ina ta shige ɗaki tayi wanka ta sanya ƴar ƙaramar riga da ɗan wando dan sam bata son sa kayan da zai takura, sallama yayi ya shigo ɗakin a hankali ta amsa tana wasa da ƴan yatsunta, bai kalleta ba yace ki haɗa duk wani abu da kika san zaki buƙata sannan ki shirya ƙarfe bakwai ki fito kin jini dai ko?
"Eh naji Allah ya kai mu, ta faɗa muryarta a sanyaye fita yayi, a fili take faɗin
"To fa! ko ina zamuje oho gashi ba halin tambaya dan wannan fuskar nasa bazai bari ka tambaya ba, ko gida zai kai ni? Allah ma yasa gidan ne dan walle in na tafi bazan dawo kurkuku ba...

_Sanarwa! Sanarwa! Sanarwa!!_

*Ina sanar da masoya cewar zamu fara class na matsalolin ma'aurata tare da hanyar magance su, da kuma gyaran jiki da sirruka da dama sai dai fa gidan ba kunya za ayi bayani yadda kowa zai fahimta ina tabbatar miki ƴar uwa baza kiyi asarar kuɗin ki ba za mu fara ne da zaran mun shiga sabuwar shekara wato 1st January 2022… zaku iya fara biya tun daga wannan rana cikin farashi me sauƙin biya, domin ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan number* 08132761212

_Kaɗan daga ciki_👇🏻
'''Akwai mata da yawa da basu san dadin saduwa, idan aka raba matanmu na arewa kashi ɗari da ƙyar zaka samu kashi sha biyar da zasu ce maka suna jin daɗin saduwar aure, wannan babban lamari ne sannan idan mukayi duba da hadisi da yake cewa. "Babu kunya a cikin addini, dole mu warware wannan matsalar bakin gwargwadon iyawar mu,
Da akwai dalilai da dama da kan sanya mace taji ita sam bata jin daɗi duk lokacin da mijinta ya kusance ta gashi kamar haka...'''
Insha Allahu zaku samu dalilai da kuma hanyan da zaku magance ta da kan ku hajiyata kar ki bari ayi babu ke a wannan tafiya😁

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212

TAUFEEƘWhere stories live. Discover now