Episode 21&22

203 21 0
                                    

*TAUFEEK*

NA

*Hafsat A Garkuwa*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*Episode 21&22*

*...*"Why? Papa taya zaka yanke min wannan hukuncin mai yasa zaka ɗaura alhakin kula da wacchar yarinyar a kaina mai yasa Papa? kasan bazan iya cikawa ba Papa bana son yarinyar nan na tsaneta Papa, wlh na tsaneta"
Ya faɗa tare da furzar da iska me zafi a bakinsa, da wannan ya ƙarasa ɗakin nata, buɗe ƙofar yayi ya shiga a hankali wuta ya kunna ya hangota chan tsakiyar gado sai mutstsikuku take hannunta riƙe da cikinta leɓen sa na ƙasa ya kamo yana cigaba da tsotsa kamar bazai yi magana ba sai da ya gama ƙare mata kallo chan cikin tsawa yace

"Are you okay?  ta jisa amma ko gezau batayi ba ta cigaba da juyinta tana riƙe da cikinta ransa ne ya ɓaci dan yasan sarai ta ji sa amma ta share shi ƙarasa shigowa ɗakin yayi cikin faɗa yake faɗin
"Dan ubanki ba magana nake miki ba wlh kika bari na hauro gadon nan na sameki na lahira sai ya fiki jin daɗi ban da amanarki da Papa ya damƙamin me zai dameni har inzo ina tambayarki, amma dan rainin hankali nayi magana kina jina amma kika min banza kega ƴar iska ko?

Nabeeha tunawa da tayi da halinsa yasa a hankali ta buɗe bakinta tace
"Yunwa nake ji Yaa Taufik sai kuma ta fashe da matsanancin kuka"

Iska ya kuma furzarwa tare da jan numfashi  domin ta sanya shi yayi magana bai ko kalli inda take ba ya juya yana faɗin mahaukaciyar banza, cikin harshen nasara.

Kitchen ɗin saman ya shiga ledar da ya ajiye wanda take shaƙe da kaji da kayan motsa baki ya ɗauka ya koma ɗakin yadda ya barta haka ya taddata ajiya mata ledar yayi ba ko kalli inda take ba bai kuma ce mata ƙala ba yasa kai ya fice abunsa, yana komawa ya kwanta yana maida numfashi tare da jin zuciyarsa wasai dan ya sauƙe nauyin da Papansa ya ɗaura masa.
Ta wani ɓangare na zuciyarsa kuma haushi da tsanarta yana ƙara addabar zuciyarsa, a haka bacci ya ɗaukesa
Yana fita daga ɗakin da sauri ta miƙe ta sauƙo ƙasa, ledar ta buɗe taci iya cinta tasha drinks taje ta wanke bakinta ta kwanta dan bata san ta inda zata mayar da abincin ba bata wani ɗau lokaci ba bacci ya ɗauketa
Asuba ta gari ango da amarya😹

Washegari ƙarfe goma ta tashi tun da tayi salla ta koma yanzu ma yunwa ce ya tada ta,  toilet ta shiga tayi wanka sannan ta fito ta shafa mai da powder da man baki, wani riga da wando mai laushi maroon wanda bai ɗameta sosai ba, ta yafa ɗan ƙaramin mayafi ta feshi jikinta sa turare ta fita, a hankali take bin ko ina na gidan da kallo, gidan ya mata kyau sai dai duk dube duban ta bata hango kitchen ga yunwa sai cinta yake, hakan yasa ta zauna a ɗaya kujerun dake falon ta zuba uban tagumi tare da lulawa duniyar tunani tana a haka taji ana faɗin
"Hajiya! Hajiya!! da sauri ta ɗago ganin wata wacce baza ta wuce sa'anninta ba rusine a gabanta in ka kalleta baza kace mai aiki bace dan cikin tsafta take sai dai I.D card ɗinta ne da zai bada shaidar hakan, gaisheta tayi sannan tace
"Hajiya sunana Larai nice me aikin gidan nan ni nake gyara falon nan, sannan kuma ni nake yiwa sauran ƴan aikin da jami'an tsaro girki.
"Masha Allah Larai nace ko zaki iya nuna min inda kitchen yake?

"Hajiya wani abun kike da buƙata naje na miki?

"A'a ki barshi kawai ki nuna min inda yake zanyi"
       Dan Allah Hajiya ki sanar min zan miki kar yallaɓo yazo yaga na bar matarsa tana aiki,
Dariya ma abun ya bawa Nabeeha dan ita tama mance da shi mekewa tayi tace to muje na tayaki, tare suka shiga kitchen ɗin indomie da chips da egg sukayi suna yi Larai na zuba mata zance dan macece mai surutun tsiya duk da Nabeeha ma ba baya ba amma yunwa ya hanata sakewa, basu ɗauki lokaci ba suka gama ta ɗibi nata ta zuwa Larai ma sannan  suka dawo falo duk da Larai taso ta tafi dan duk lokacin da ta gama aiki bata zama a falon
Saboda abunda Yallaɓon su ya sanar da ita kenan, sam Nabeeha taƙi barinta ta aikata hakan, suna kammalawa Larai ta tattare wajen sannan ta dawo hira taci gaba da mata sai dariya suke kamar zararru dan Larai ba dai labarin barkwanci ba, sai da aka ƙwalla ƙiran sallar azahar sannan ta tafi ita kuma ta haura sama toilet ta shiga tayi wanka ta ɗauro alwala,
mai ta shafa sannan ta zira rigar Sallarta ta gabatar da Sallah sannan ta shirya cikin atamfa doguwar riga ta yi simple makeup wayanta ta ɗauka da take ringing Samha ta gani cikin farin ciki ta ɗauka bayan sun gaisa ne take tambayarta Yaa Taufiq ɓata fuska tayi kamar Samhar tana ganinta tace
"Ina ruwana da wani Yaa Taufiq meye haɗina da shi?
Dariya Samha tayi sosai tace "gaskiya kam ba ruwan ki da shi, dan yanzu tasan tana faɗar wata magana yanzu zata iya fashe mata da kuka, hakan tasa tayi sauri ta miƙawa Huda tana gama gaisawa dasu Sweetie ta ƙirata sun jima suna wata a jere a jere tayi ya waya da ƴan gidan su tuni ta mance da a wani wuri take, dariya take ta zubawa me sauti saboda yadda Nazmar yake bata labari, sam Jawaad bai iya tsayawa sunyi doguwar hira ba, kamar daga sama taji yace

"Ke bana son hauka ba gidan mahaukata kike ba gidan masu halinki kike, kina magana cikin hankali"

A tsorace ta juya ta ganshi tsaye a bakin ƙofa fuskar nan tana nan yadda take kamar kullum
  Baki ta turo gaba tace "to ina ruwan ka da ni ai bani nace kazo min ɗaki ba bare kaji abun da nake, ta ƙarasa tare da murguɗa baki.
    A fusace yayi wo kanta bakinta ya kama ya murɗa wani ƙara ta sake saboda zafi da ya ziyarceta, a fusace yace

"Dan ubanki yaushe na fara wasa da ke?...
To bari kiji ni ba sa'anki bane wlh nafi ƙarfinki na miki fintin kau dan haka bani wayan naki, sai naga gobe da me zaki ƙira kina haukan, ya faɗa yana wacce wayar hannunta ya zira a aljihu ya wullata kan gado tare da zabga uban tsaki yabar ɗakin, ɗakinsa ya nufa dan dawowar sa kenan daga taron gaggawa da al ƙirasu yana shiga ya kashe wayar ya cillata cikin kwando wanka ya shiga ya ɗan jima sai da ya rage cikinsa sannan ya fito mai ya shafa ya sanya jallabiya ya feshe jikinsa da turare ya ɗauko kayan aikin sa ya fito falo, ba kowa a falon sai A.C da Tv da suke aikinsu zama yayi ya fara aikin dake gabansa wayasan sa ne ya fara ƙara kamar bazai ɗauka ba sai kuma chan yayi tsaki tare da ɗaukar wayan, sallama tayi daga ɗayan bangaren a hankali ya amsa yace "ya akayi?
  Cikin kissa tace
    "Haba Dear ya zaka ce haka bayan kai kace zaka ƙirani anjima ni kuma dama nasan ba ƙira za kayi ba shiyasa ni na ƙiraka, Dear me yasa kake min haka dan Allah? kasan dai ina sonka wlh bazan iya rayuwa babu kai  ba kuma…
 
"Dan Allah dakata Haseenah na dawo a gaji kuma hutawa nake son yi pls ki rabu dani na hutawa raina nace ki daina ƙirana ni zan ƙiraki duk lokacin da bukatar hakan ya taso kina dai jina ko?

Kamar za tayi kuka san ba haka taso ba tace
"Eh naji dear sorry bazan kuma ba, da kusa muke ai da na zo na maka tausa ina son…

Kit! ya kashe wayar batare da ya bari ta ƙarasa maganar ba...

_Ku taɓa ku lashe kayanku walle yadda bana samun comment a wajenku yadda nake so haka kuma baza ku samu yadda kuke so ba walle mu tafi a haka_🤷🏻‍♀️

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212

TAUFEEƘWhere stories live. Discover now