Episode 55&56

164 18 7
                                    

*TAUFEEƘ*
NA
_Hafsat A Garkuwa_

*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
  _(Domin Marubuta Mata)_
           ✨W.W.A✍🏻
https://www.facebook.com/Women-Writers-Asso-106752595253176/

*Episode 55&56*
… "Amatullahi! Amatullah!! dan Allah ki tashi kada ki tafi ki barmu wlh muna jinki har cikin zuciyar mu innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Alhaji bata motsi fa dan Allah ƙara zuba mata ruwan".
Abba da gaba ɗaya a kiɗime yake ya sake buɗe wani goran ya tiltila mata shi duka a jikinta.
"hhhhhhhhh! hummmmmmmm!!!
Wani irin dogon numfashi taja tare da sauƙeshi a hankali ta fara buɗe idanunta ta buɗesu tar akan Ammy da idanunta suka kumbura tsabar kuka ga kuma hawayen da ke bin kan fuskarta.
Ammy ganin ta tashi ne ta rungumeta tsam a jikinta tana sauƙe ajiyar zuciya.
"Alhamdulillah.!
"Alhamdulillah.!
Alhamdulillah.!!
Shine abun da suke faɗa musamman Abba da yake ganin kamar shine silar faruwan haka wani irin kuka ne wa ƙwacewa Amatullah bayan ta tuno duk abun da ke faruwa kuka tayi sosai a jikin Ammy ba tare da sun tsayar da ita ko sun hanata ba sai dai kuma ganin bata da niyar tsagaita kukan nata ne yasa Abba ya ɗauko mata goron ruwa me sanyi ya buɗe ya miƙa mata.
"Karɓi ki sha."
Ba musu kuwa ta karɓa ta kafa kanta sai da ta shanye tas sannan ta ajiye goron ji tayi zuciyarta ta fara sanyi a hankali ta fara sauƙe ajiyar zuciya sai dai tuni zazzaɓi ya rufeta dan jikintan nan kau kamar garwashin wuta jin hakan da Ammy tayi ne ta ɗago rinanun idanunta ta kalli Abba da sai yanzu ya nemi waje ya zauna yana maida ajiyar zuciya.
"Abbansu jikinta yayi tsanani fa a ƙira likita yazo nan gida dan ƙila dai a ɗaura mata ruwa dan jikin yayi zafi ainun.
Jinjina kai yayi alamar "to"
Sannan yace
"Fatima ki ɗauketa ki kaita ɗakin da kika san babu wata hayaniya yanxu Dr. Zaizo ya dubata ta.
Miƙar da Amatullah tayi amma sai taga Amatun ta koma tq zauna gyara zama tayi tana kallon Abba tace
"Abba na amince da zaɓin da kamin haƙiƙa kai ɗin mutumin kirki ne ka cika adali tabbas bazan taɓa mance wannan halaccin da ka min ba Abba ace baka sanni ba baka kuma san suwa yi ahali na ba baka ma damu da ka sanin ba amma ka ɗauki ɗan ka guda zaka haɗani aure da shi babu abun da zance da kai sai dai na yi muku fatan gamawa da duniya lafiya dan kun gama min komai tun bayan Mutuwar mahaifana kaine mutum na farko da ka fara nunamin soyayya da tausayi da kuma jinƙai na gode Abba.
Ta ƙarisa maganar wasu hawaye masu zafi suka fara sintiri akan fuskarta.
Cike da farin ciki Abba yace
"Na gode Amatullah in sha Allahu kuma baza kiyi ɗan dakin sani ba tashi maza kije ki cire waɗan nan kiƙaƙƙun kayan likita yazo ya baki magani.
Ammy ne ta taimaka mata suka fitoa direct ɗakinta ta nufa da ita dan tasan nane kawai ba tulun jama'a suna shiga kuwa hakan ta tarar ba kowa a ciki sai ƙanwarta Hajiya Mariya ajiya Amatullah ɗin tayi ta fita ba jimawa ta dawo ɗauke da kayanta sabbi na biki da Abba ya musu miƙa mata tayi tana faɗi
"Maza sauya ki haye gado ki kwanta yanzu likinta zai zo".
"Tom".
Ta faɗa a sanyaye dan gaba ɗaya wani irin layi take ji sam ba komai take ganewa ba musamman in ta tuna Lamir.
Fita Ammy tayi ita da Hajiya Mariya da take yiwa Amatullah sannu.
Sauya kayan tayi ta haye gado ta kwanta wani irin zazzafan zazzaɓi na sake rufeta gaba ɗaya ɗakin ne taji yana juya mata ga wani irin sanyi da take ji duk da ta rufu da blanket mai kauri amma bata dai na jin sanyi ba.
Tana a haka Dr. Ma'aruf yazo ya gwadata tare da ɗaura mata drip ya zuba magani a ciki nan take kuwa baccin azaba ya ɗauketa, tana sauƙe wani irin ajiyar zuciya.
Abba kuwa suna fito bayan ya ƙila Dr. Saif ya ƙira yace ya samesa a falon sa ba jimawa kuwa ya shigo bakinsa ɗauke da sallama duk yayi wani iri da shi ya rame.
Ri sinawa yayi yana faɗin
"Abba ga ni nan Allah yasa dai lafiya?
"Lafiya ƙalau Saifudden sai alheri".
Gyaran murya yayi yaci gaba da cewa
"Ba sai na tsaya yi maka dogon jawabi ba dan kasan komai, kasan dai iyayen abokin ka Lamir sun fasa auren Amatullah ko?
Da sauri Saif ya ɗago cike da kaɗuwa, mamaki, farin ciki domin shi kwata-kwata bai san da wannan daddaɗan labarin ba yace
"Abba wlh bani da labari garin yaya mais yasa kuma suka fasa?
A lokaci guda ya jefowa Abba wannan tambayar wacce mana kallon fuskarsa za ka gane tsananin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa sai da ya fallasa sirrin zuciyarsa.
Murmushi Abba yayi ya sanar masa duk abun da ya faru ya ƙara da cewa
"Haka ne yasa na yanke wani hukunci wanda nasan za kafi kowa farin ciki, domin nasan kana sonta hakan yasa san haɗa ku aure da ita yadda kuma aka sa date baza a ɗaga shirye ba dan haka sai ka fara shiri.
"Wayyooo Allah na! Ihu zanyi ne ko kabbara zanyi? Allahu akbar Allah mai iko Allah mai yadda yaso kana naka Allah na nashi na Allah shine dai-dai Allah na gode maka".
Duk wannan maganar a fili yake yi ba tare da yasan hakan ba dan duk ya ɗauka cikin zuciyarsa yake sai da yaji Abba yana faɗi
"To sannu maras kunya".
Sannan ya dawo cikin hankali sa tare da sunkuyar da kai yana tsotsa ƙeya alamar kunya.
Abba ne yace
"Kaga ka riƙe min ɗiya da amana kar naji kar na gani kamar yadda kake riƙe da Nana hannu bibbiyu itama Amatullah ka riƙe min ita hannu biyu.
"Ai Abba hannu ɗari-ɗari ma zan riƙeta wlh".
A zuciyarsa ya faɗa yana jin wani irin yalwataccen farin ciki so yake kawai Abban nasa ya sallamesa yaje ya ganta so yake kawai ya ganta ko zai ƙara samun nutsuwa fiye da wanda yake ciki yanzu.
Nasiha Abba yayi ta masa mai rasa zuciya ya ƙara da cewa "sai ka sanar da abokanka na kusa tunda abun yazo ba shiri sannan fargabata Nana ce kawai ban san yadda za ɗauki lamarin ba…

Ji yayi gabansa ya faɗi domin sai yanzu ya tuna akwai aiki a gabansa dan yasan yadda Nana ta tsani ayi zancen kishiya ta dinga sababi kenan da ɗagawa kanta hankali balle kuma ace ita za ayiwa dakewa yayi yace

"In-sha-Allahu Abba zanyi mata gamshashshiyar bayani na tabbata baza a samu matsala ba.

"To Allah yasa ai hakan muke fata ayi komai cikin kwanciyar hankali za ka iya tafiya Allah ya maka albarka.

Cike da farin ciki ya miƙe yana faɗin "Amin ya rabbi Abbana na gode".

*My Fan's I love u ficika-ficika wlh yanzu rashin comment ɗinku yasa na adama hankali na waje ɗaya bazai yiwu ina faranta muku ku bakwa farantamin ba amma duk da haka ina muku son so domin Allah*😘✨🌹

#Vote
#Comment
#Share
#Taufeeƙ

*ONE LOVE💞🤞🏻*
08132761212

TAUFEEƘHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin