Page 3
WACCE CE ZAITUN?
Zaituna Muhammad shine cikaken sunana , mahaifina Wanda aka fi sani da mallam muhammadu ba mai kudi bane , Dan asalin garin Kano , tunda y taso ma shi maraya ne ba uwa ba uba a gurin yayarsa yake, yayi iya primary daga nan kuma y cigaba da Zuwa islamiyya Yana yar sana ar sa ta siyarda lemon bawo, Wanda shine yke taimkawa yayar tasa bayan mijinta ya rasu, a hka har yakai munzalin aure , ya auri matarsa saudatu suna zaman su Lfy , y kama musu gida suna zaman su , haihuwar ta farko aka samu mace aka ranar suna ya taci suna zaituna, tundaga lokacin basu Kara samun haihuwa ba sai bayan shekara 5 , Allah y basu wata macen aka saka mata rahma daga nan kuma sai bayan shekara 10 , suka samu wani haihuwar wanna karon namiji aka saka masa bashir , daga nan kuma shikenan haihuwar ta tsaya .
Mun Taso cikin tarbiya da kulawar iyayen mu saidai mu ba masu kudi bane , mallam muhamadu mutum ne mai Neman nakansa, da tausayi watarana idan abincin da aka dafa ba yawa hka zai hkura shi y kwana da yunwa , hka rayuwa ta cigaba da tafiya lokacin dana taso kawata hafsa ita kadai ce muke kawance don cewa nake duk yan yaran layin nafi karfin su saboda kyaun da Allah y bani , fara ce ni sosai ga gashi sau dayawa ma idan Ina kallon kaina a madubi saina ta cewa Anya su mama ba sato ni sukayi ba Dan ni ba kalar gidan wahala bace ba
Ko a makaranta bana kawance da ya yan talakawa, idan naga kina zuwa da su dankalin turawa da Kwai ko indomie da lemo to nasan ke yar gidan masu kudi ce Toh zan yi kawance dake , idan kuma naga abinci ki gashi ga yada yake Toh nasan ku talakawa ne babu abinda zanyi dake ,
Mama Tana mun fada da nasiha haka ma hafsa aman hkan baisa Wai na chanza halina ba , Ina ss 3 , Allah y hadani da usman yazo service makarantar mu,
Tun ranar da ya dora idon sa akaina y rikice, da Yana boyemun Aman yaga ba mafita dole saiya fdamun, Dan hka bai yi sanya ba y fadama hafsa, ranar da hafsa ta fdamun nayi murna sosai saboda duk wata mace ta school din crushing yake Aman baya kulasu, don hka ba wani Inda inda na amince duk kuma a zato na Dan masu kudi ne saboda kyan jikin sa gashi ya iya daukar wanka ,
Mun fara soyaya da usman a haka har muka yi SSCE exams , da Kansa y biyamun jamb nayi sabida an sansa a gida kuma iyayaena sun Amin ta dashi , fafutukar Neman admission duk usman ne yamun ni kawai Ina kwance, abu na farko da ya fara saka usman y fita a raina shine dayace naje na gaida mamansa, na fadamwa mama Dan hka aka hadani da rahma mukaje,
Ganin irin gidan da suke, madaidaici hkan ysa na gane shi din ba Dan wani bane ba , mahaifinsa baya raye , Yana tare da mahaifiyarsa wace itama take teaching a wani primary school a unguwar , haka suke lalaba rayuwarsu, su 3 mamansu ta Haifa shida kanwarsa fatimah sai yayar sa Aisha wace take aure a kaduna
Mahaifiyar usman ta karbe mun sosai cikin girmamawa Aman maimakon naji dadi , haushi ta dinga bani , da zamu tafi kuwa tabani Atamfa mai dan karamun kudi sai sabulu, Dana kawo gida mama sai shi mata albarka takeyi nikuwa na hade rai , Wai tsabar ma talauci y musu yawa mama a hadani da Atamfa roba roba da wani sabulu giv Kai aman talauci baiyi ba , rike Baki cike da mamaki mama tayi Tana kallo na , sanan tace yanzu zaituna duk wanan abun arzikin da ta Baki godeba kike fadin magana marasa dadi Anya zaitun kina da hankali kuwa ,
Na zumburo Baki na ce nikam banaso ki rike ko ki bama rahama wlh banso kuma usman din yajecan ya nemi daidai shi , mama zata kaimun Duka nayi Saurin mikewa na shige daki da Gudu , kwafa mama tayi gamida fatan shiriya a gareni nikuma Ina daki Ina gunguni abuna
Tun daga ranar na dauki karen tsana na dorawa usman , na bude shafin rashin mutunci sai naga dama idan yazo zan fito , Ana hka y kawo mun waya smart phone , dukda ba sabuwa bace Aman naji dadi saboda ko banza zanyi chat ca kawayena masu kudi yan makarantar mu. Wanna wayar da usman ya bani y saka na Dan rage masa rashin mutunci dukda ba Wai dainawa nayi ba .
A haka nasamu admission a northwest , ranar da usman y tura mun admission letter Dina tsale da murna harda rawa nayi gani nake ae nazam a big girl , yanzu zan hadu da kawayen da nakeso, ba Wai karatun ne a gabana ba Aa life din dazan yi, da BURIN haduwa da miji mai kudi shine BURINA kuma nayi alkawari saina cika shi sanan .. mujee Zuwa
![](https://img.wattpad.com/cover/368980426-288-k701212.jpg)
YOU ARE READING
BURINA(HAUSA NOVEL)
FantasyThis novel is about a young lady zaituna who was came from a poor background and Tries her possible means to fit in just to be with her friends who happens to be rich Sit back and enjoy 🩷