PAGE 19

122 3 0
                                        

📚📗BURINA📘📗
Written by Khadija Mustapha
              PAGE 19

Mutane da basu fi 10 bane ba suka Kai rahama gidanta , wasu dayawa sun je gidan zaitun domin su kashe kwarkawtar idon sa ,wasu kuma don ganin motoci masu tsada ne , wasu kuma dan kar ayi babu sune , haka dai aka Kai rahma aka waste aka barta ita kadai daman ita batada kawa ko daya , tashi tayi Tana kallon gidan ba laifi gidan zaman mutum daya ne palo ne da bedroom sai kitchen da bandaki a tsakar gidan , ita komai ya mata na gidan usman yayi kokari sosai ta fada Tana murmushi da kallon gidan

Zaitun kuwa tunda aka daukota ba a ajiye ta ko Ina ba sai tankamemen gida na alfarma, ni kaina saida nayi mamakin tsaruwar gidan , nan kuwa yan kawo amarya suka shiga santin gidan Ana ta magana Akan tsaruwar gidan , har bedroom Dina aka ajiyeni sanan suka tafi , ya rage daga ni dai Zee dasu yesmeen , hirar mu muka cigaba da yi ta manyan yara as always , yesmeen ce take complain mijinta yanzu baya xanan kasar ma so take mu gama school ta koma abroad gaba daya , tafa wa mukayi muna mata dariya , horn mukaji Wanda yake tabbatar mana da ango ne , ta window din dakin Zee ta leka sai ta ango shi kadai , ah ah Wai zaitun wanan mijin naki shin bashida aboki ne kinga shi kadai still yau , Anya , kallonta nayi cikin rashin fahimta kmar ya Anya kuma abokai maybe sun koma garin su tunda duk ba yan garin nan bane ba , yesmeen ce tayi magana Aa zaitun haka yau da safe yazo shi daya akwai daman ango dake Zuwa gidan su amarya shi daya bayan daurin aure , ihsan ce ta kaste yesmen Aa ku kuma mene haka so what Dan ango yazo shi daya , it's normal dan Allah a bar wanan maganar it's not making any sense , shiru kowa yayi sakamakon kwankwsa kofar bedroom din da akayi , ka shigo ihsan ta fada nikuma na rufe fuskata da mayafi na ,

Shigowa yayi Yana washe Baki suka gaisa da su yesmeen sanan suka yi mana salama , suna fita shima ya fita dan rufe kofar gidan sanan ya dawo gun amaryar sa zaitun .

A bangaren usman kuwa yau ta kasance rana da ce mai mahimaci a gurin sa , ya dauki alkawarin zai kula da rahma tunda itace ta share masa ha waye a sanda yake bukata, itama haka rahma tayi alkawarin saita mantar dashi bakin cikin da xaitun ta saka shi Insha Allah

Yau sati daya da auren mu , kuma zance bantaba samun Farin ciki ba kamar wanan lokacin , abunda nakeso nake ci kuma nasha Wanda nakeso, wani abun ma ni ban sanshi ba , yussuf kuwa sai bani kulawa yake yi wanda ya kuma sakawa na yarda dashi kuma nake Kara Jin sa cikin Raina .

Wasa wasa tunda mukayi aure yussuf baitaba ce mun zaije aiki ba , yau kusan wata daya kenan , tun bana damuwa har nafara damuwa hakan yasa nayi masa magana, ae kuwa naga baccin rai nan ya shiga yi mun masifa dalilin dayasa nake masa wanan tambayar kmar yarona, sosai yake masifa ta Inda yake shiga ba Tanan yake fita ba , nan take jikina ya hau rawa don tunda nake da yussuf bai taba daga mun murya ba Aman yau shine yake mun bala i kmar yasamu yarsa, haka ya gama sanan ya fice daga gidan bayan ya mun warning na tabbata nayi  masa abinci dan tunda nazo gidan take away mukeyi, sosai nasha kuka na Ina tunanin ko dai asiri akayi ma yussuf ne , da naga tunanin bazai amfane ni da komai ba na tashi Ina share hawayen dake zubo mun na nufi kitchen Dina don Dora abincin.

BURINA(HAUSA NOVEL)Where stories live. Discover now