PAGE 10📗

97 2 0
                                    

📗📗BURINA 📗📘by Khadija Mustapha

BURINA page 10

Da safe sai ga hafsa , bayan sun gaisa da mama ta shigo dakina , marar mutunci tace mun cikin wasa , dariya nayi Kai hafsa menayi miki , bansani ba ta harareni, ace Wai tun rnar da kikazo Baki kuma ko lekowa ba , ko dake naga post dinki  a status ae kinyi sababin kawaye yan gayu shine ni kika ajuyeni a gefe , ke bar wanan magabar na me zakiyi da 15k , Mts wlh kinga biki muke kuma bnida kudin kwaliyya shiyasa , yanzu kwaliyya ne har 15k Wai ba dubu 5 wanan yarinyar ta saloon din mama blessing takeyi ba shine ke zaki je kiyi harna 15k tab , kinga hafsa idan baziki Aran va kawai kice Aa mene zakice naje saloon din mama blessing ke kinga wani saloon da mukaje da kawayena hmm wlh kmar a film din turawa dinan , da kalo hafsa tabini sanan tace Allah y Baki hkuri Aman gani nayi kwaliyya kwaliyya ce ko , Aa hafsa kwaliya kashi kashi ne, akwai kwaliyya akwai kuma muna kwaliyya wanan da za a yimun shine kwaliyya itakuma Wanda yarinyar mama blessing takeyi shine muna kwaliyya, kaloona kawai hafsa take Tana mamakin yadda zaitun ta waye haka , a iya saninta ko saloon din unguwar su na mama blessing bata taba Zuwa ba bare har wani saloon mai kama Dana turai , gskia kawar tata ta chanza, hafsa bata kara cewa komai ba ta mikamun kudin Toh gashi Aman ba bashi ba , abbanmu ne ybani 50k na chanza kaya shine na Baki a ciki, Kai Aman abba ysan abunda ya kamata ba kmar baba ba wlh babanmu baxai taba Baki kudi hka kawai va har 50k , saurin kasteni tayi haba zaitun kina sanin abunda zaki fada mana, baban ne kike mganar sa haka , Toh ae gaskiya na fada , Nidai banson ji ka kudin ni zan wuce kasuwa nasan ko nace ki rakani ba bina zakiyi ba biki kuke, kwarai kuwa nafada Ina dariya banason nayi Baki skin Dina yaki daukar kwaliyya, duka takaimun na kauce jna dariya mukayi salama ta fita ko rakiya bata samu Va Nikam BURINA y cika na samu kudin kwaliyya yanzu kuma usman nake jira yazo y kawo mun dubu 5 din da yace zai bani .

Hafsa bata jima da fita ba usman ya kirani a waya Yana Kofar gida , gyale kawai na yafa Akan abayar dake jikina , na fito nayi hanyar waje bayan na shaidawa mama usman ke Kira na

Yana Kofar gida na isa gamida slm , ya amsa Yana murmushi da saida dimple dinsa ya loba, gaisawa mukayi sanan yace shi zai wuce kasuwa ne saboda yana jiran Shagon wani mokocinsu a kwari idan y taso daga makaranta saikuma weekends da safe har yamma, mikamun kudin yayi tare da bani hkurin rashin bani duka kudin , ba komai nace nayi godiya na shige gida abuna

Jaka da takalmin da Maryam tabani na dauko zan maida mata saita bani wani , this time around wani hadaden purse tabani da takalmi suma designers , nayi godiya sosai sanan ta hadani da jewelries masu kyau

Karfe 3 na dauki hanyar gidansu Zee , yau duka a can na same su , muka hau hirar duniya da baya wuce na samarika su yesmen masu kudi , Nikam saidai na shirga karya saboda bani dashi , wani faruk kawai na taba dan gidan masu kudi shima da dan kudin sa ba laifi Aman tun ranar da na nuna masa gidanmu y daina kirana, Dana dame shi da waya ma ba kunya y fito ya fadamun shi fa bazai iya soyaya Dani ba at first daya gani ya dauka yar gidan masu dashi ne Aman tunda ya gane ba muda kudi gaskiya shi bazai iya ba karna cinye masa abinda ya tara Dani da iyayena, sosai naji zafin mganar sa Aman hka nayi shiru Ina bashi hkuri karahe ma dai blocking dina yayi

4 daidai aka fara yi wa amarya makeup saboda yau dinner ne kuma sai dare , nayima mama karya gidan kanwarta Anty saratu zanje nayi kwana biyu na dawo Monday da safe tunda Tuesday Inada lectures , nikuwa karya nake saboda mun shirya kwana gidan su Zee yau sai an Kai amarya kowa zata wuce gidansu , nasan da cewa mama bazata taba barina ba yasaka nayi mata karyar gidan Anty saratu zan je kwana .

An Kai kusan 2 hours Ana yi ma Zee kwaliya tayi kyau sosai sanan ta sauka kasa gurin stylist dinta wace ta karaso yanzu don saka Kayan dinner din , yesmen akayi wa sanan ni , ihsan ce karshe , suka mata transfer din nasu kudin nikuma na bata cash , murmushi kawai tayi Dana Mika mata kudin har yau inajin kunyar karyar da nayi mata jiya .

Kusan 7:30 muka gama shiri kowa tafito das ta ita barin ma ni , nayi kyau harna gaji , na kalli kaina a mirror yafi sau a kitga nsan tabbas yau nayi saurayi BURINA yau zai cika

Motoci ne na alfarma harsunfi na jiya kyau suka kaimu hall din daya gaji da haduwa , amarya da ango sun yi kyau Masha Allah , waje da aka ware mana mu manyan kawayen amarya , sai abokanan ango suma wajensu a ware yake , kana ganin kaga manyan mutane da kudi suka zauna musu , sosai bikin yayi kyau yayi dadi

Karfe 11 aka tashi muka fito daga hall din Ina kaloon yesmeen da ihsan suna zance da wasu Abokanan ango nikuma ba Wanda y kulani , na tsaya a gefen wata mota Ina chat cike da nada mar kashe kudin danayi gashi kwaliyya bata biya kudin sabulu ba

Suna gamawa muka dauki hanyar gidansu zee, Ana sauke mu na haura bedroom cike da Jin hau shin rashin cikar BURINA ,

Ina shiga na shige bathroom din dakin na goge dubu 25 Dina Ina hawayen bakin ciki, wanka nayi sanan na dauro alwala na fito , haryanzu basu hayo ba don hka na chanza kayan jikina na hau rama sallah

Ina tashi bayan na idar da sallah su Zee suka shigo , Wai zaitun dama kina nan , eh kawai na bisu dashi , Wai Kinsan waye yace Yana son yesmen kuwa inji ihsan , kaina na gyada alamun Aa , da gidan senator , kuma yes tace ta samu miji cuz irin wanan ba a barinsu su kubce, yesmen ce tace yess ta tashi Tana juyi kuna kaloon latest amarya ku fara shiri , murmushin takaici nayi yayin da su kuma suka hau shewa.

Kaina ke ciwo zan kwanta nace gamida da juyawa na rufe idon kada ma su Kara saka ni cikin zancen su a haka bacci yayi gaba Dani cikin bakin cikin rashin cikar BURINA

BURINA(HAUSA NOVEL)Where stories live. Discover now