📗BURINA 📗📘 written Khadija Mustapha
Page 26 (LAST PAGE)
Tsawa yayi mun dana fito daga motar , cikin rawar jiki na fito , muna fitowa daga motar daidai da iso war usman da yan sanda , na gudu na gudu bayan usman na fara magana cikin kuka usman siyarda nayi zaiyi na fada cikin kuka , yan sanda ne suka saka ma yussuf ankwa Yana tirjiya sanan suka shiga cikin gidan nan aka fito dasu oga Wanda ya siyar musu dani , nikuma usman yace na shiga mota muka Kama hanyar gida har yanzu Ina kuka , Allah sarki rayuwa usman din dana wulakanta shine yau ya cecci rayuwata , kaico na yau na gane dan Adam ba abun wulakaantawa bane ba , barinma usman da ba laifin daya mun sai ma soyaya da ya nuna mun tsakani da Allah Aman na ki sa kawai saboda bashida abun duniya, na manta da arziki da rashin sa duk Allah ne .
A gida kuwa kowa hankalin sa a tashe , suna ganina na dawo da usman nan aka tareni cikin Farin ciki , usman ne ya sanar dasu abinda ya faru, mama ce ta kalleni sanan tace kinga zaitun wanna sai yaxama ishara gareki da duk wani mai biyewa son zuciyar sa , hawaye ne y cikamin ido sanan nace Insha Allah mama na chanza halayata bzan Kara biyewa zuciyata ba , Allah ya kiyaye gaba inji mama kowa ya amsa da Amin , rnar dai kowa a sanyaye jikin sa yake
Shaida aka kirani a court dan haka mukaje dasu mama , nan alkali ya yanke wa Yusuf daurin shekera 15 a prison , sosai yayi nadama , a gabanmu aka tasa keyar sa aka saka shi a mota dan kaishi gidan maza dashi dasu oga , maman shi kuwa sai kuka take Tana birgima da tsine mun Wai duk nice na sa aka kama mata danta tillo daya mama kuwa ta yi mata ta tas nan taja Baki tayi shiru Tana mazurai, ranar na Kara dana sanin abunda na aikata
Bayan shekara 5
Abubuwa dayawa sun faru daga ciki harda gida da usman ya siya ma su baba , yanzu usman ya zama Alhaji usman kudi sun zauna masa suna nan d yaran su biyu asmau yar shekara 4 sai bilal dan wata 6 , rahma tayi kyau abunta usman ya bata jari Tana kasuwancinta, ni kuwa da kyar su baba suka shawo kaina na yi aure , na auri wani mai mata daya hashim Yana aiki a kamfanin zarafa takalma Yana da dan Ruffin asirin sa zaman mu Lfy , har yau idan na tuna da rayuwata ta baya sainayi kuka ...
Alhamdullilah Alhamdullilah munzo karshen wanan littafin na BURINA , Allah yasa sakon da nake son isarwa ya isa , Allah y shirye mu gaba daya Amin
Wait for my new novel soon Insha Allah
YOU ARE READING
BURINA(HAUSA NOVEL)
FantasiThis novel is about a young lady zaituna who was came from a poor background and Tries her possible means to fit in just to be with her friends who happens to be rich Sit back and enjoy 🩷