PAGE 18

82 1 0
                                    

📚📗📘BURINA 📗📘 written by Khadija Mustapha

PAGE 18

Sosia na shiga cikin damuwa rashin kawo lefe na da ba ayi ba kuma nakasa samun yussuf a waya , mama kuwa ranta ya baci sosai har ta fara fada baba ya bata baki yace ayi musu uzuri maybe wani abun ne ya faru haka dai aka bar maganar Aman na shiga damuwa matuka.

Kwana 2 da faruwar hakan yussuf ya kirani a waya , harda kuka na na ce masa banji dadin abunda yamun ba , hakuri y shiga bani sanan yace baban su ne uzuri ya taso masa so he has to accompany him , Insha Allah na fadama su baba gobe za a kawo lefen karna damu.

Sosai naji dadi sabanin da Dana fara tunanin ko dai fasawa yayi , washe gari kuwa kamar yadda ya fada Karfe 12 saiga mata da motoci ankawo Kaya , akwati 12 duk cike da kaya , zo kuga murna har kasa boyewa nayi , kayana ne na gani na fada , ae kuwa harda Wanda bansani ba a unguwar mu Saida suka zo ganin lefen , kowa yana ta furta albarkarcin bakin sa.

Komai aka saka wa rana tabbas zaizo , yau ne aka fara bikin mu Dani da yussuf , rahma da usman , dukda su rahama ba event ko daya sai daurin aure nice dai yau zamu fara da cocktail party

Da rana usman ya turo mota aka kaini gurin makeup , cikin hour 2 aka gama mun makeup na fito kamar na sace ni ka gudu ,

Hall ne mai kyaun gaske yussuf y bani kudi na Kama , aka fara event , tun Ana jiran ango har aka fara gajiya, na Kira wayarsa Aman not reachable hakan ba karanun bata mun rai yayi ba Aman saina yi masa uzuri maybe ba charge wayar sa na tabbata zaizo , su Zee kuwa har sun gaji da tambayata Wai ango bazaizo ba za a yanka cake , na basu amsa da zaizo

Har aka kusa tashi ba ango sanan nkira wayar sa still switch off , haka aka yanka cake ba ango , wasa wasa har aka tashi ba ango , sai su Zee ne suka sauke ni gida , hakan kuwa ba karamun bata mun Rai yayi ba .

Yussuf bai kirani ba sai bayan Karfe 10 na dare , sosai na nuna masa Raina ya baci , excuse yabani Wai Baki yayi waenda suka zo daurin aure so Yana Chan Yana saukar su , ban saki Raina ba Saida ya jadada mun dinner dinmu yadda ya tsara komai kuma ya kashe kudi don ya faranta mun , haka dai na saki Raina muka cigaba da hirar biki .

Washe gari shi da Kansa ya dauke ni yakaini gurin makeup , Saida aka kusa gama mun yadawo dan daukata mu wuce gurin dinner din , Karfe 9 daidai aka gama makeup din Dan haka bamu wuce ko Ina ba sai event center din , sosia waje yayi kyau ya hadu kamar yadda muka hadu muma, ba tareda da bata lokaci ba aka fara event , Wanda na Lura da friends din yussuf basu wuce 5 ba , sai gayar kawayena da yan uwana, Aman duk da haka na share dan ni ya gama cikamun BURINA tunda y zabe ni a mastayin mata kuma ya shirymun biki irin wanan na kece raini

Sai 12 na dare aka tashi daga wajen dinner , da Kansa ya ajiyeni gida , baba sosai ya yi fada da munyi dare , hakuri na bashi na shige daki Ina mita daga gobe na bar muku gidan ma ni gaba daya  , yan mata ne duk a dakin dangin mama da baba anata tautauna yadda  dinner ya tsaru ana Yaba kudin yussuf , nikuwa kaina ya Kara girma Ina ta washe Baki ni dole zan auri mai kudi , ko zancen rahma ma ba a yi, biki yaxama kamar nani kadai akeyi kowa hira ta data yussuf akeyi da irin dukiyar daya kashe .

Washe gari karfe 11 aka daura aurena da yussuf , sai rahama da usman , zo kuga murna a gurina yau na cika BURINA na auri mai kudi , Ashe dai Nima Allah ya na tune Dani na fada cike da Farin ciki

Sosai gida ya cika da yan uwa sai hoto akeyi , kowa kagani dauke yake da Farin ciki , angwaye sunzo, usman yazo da abokanasa sosai sabanin ni da ango yazo shi daya , nayi mamaki hkan aman bantamyeshi ba dalilin hakan ba

Da yamma mama da baba suka suka aiko  a kiramu nida rahma , bayan mun zauna baba ne ya fara bayani  kmar hka zaitun da rahma Allah yayi yau an daura muku aure alhamdulliah , kunsani na baku tarbiyya daidai gwargwado , Dan Allah kubi mazajen ku , ku zauna lafiya , kuyi hakuri , kuzamo masu hakuri Indai kuka yi hakan Toh zaku xauna Lfy Insha Allah, rahma ce ta fara kuka Aman nikam ko a jikina gani nake dan usman talaka ne yasa ta fara nadama tun yanzu , yarinya baki ga komai ba ma na fada a cikin zuciyata

Mama ma tayi mana nata nasihar sosai mai rasta jiki, haka mama da baba suka saka mana albarka sanan muka koma dakin mu

Karfe 6 daidai usman ya turo motar daukar amarya , mota guda daya ce ta daukar amarya sai adaidaita Sahu da bus an fito za a fara kaita motoci na alfarma sukayi parking , wasu mata su biyu suka fito daga cikin Dayan suka gabatar da kansu as sune suka zo daukar  amarya zaituna , ae yan kai amarya na ganin motoci aka fasa hawa adaidaitan da usman ya aiko a kai amarya rahma

Haka mutane suka dinga shigewa na zaitun , da kyar aka cika adaidaita biyu aka dau hanya dan Kai rahama dakin ta

An fito za a fita Dani sai a lokacin naji kwalla  ta cika idona , shikenan yau zan kwana cikin gidan Daba namu ba , Aman dana tuna irin daular Dake jirana nan take na saki Raina , haka aka fito Dani aka saka ni a daleliyar mota mai kyau da tsada aka nufi gidana Dani .

BURINA(HAUSA NOVEL)Where stories live. Discover now