📗📗BURINA 📗📗Written by Khadija mustapha
PAGE 13
Yan mata naji muryarsa ta kuma maimaitawa, dogon tunanin da natafi ne ya saka ma na manta da mutum a gabana , uhm Ina Wuni na fada a daburce, bai amsa ba ya cigaba da magana Wanda take naji farin ciki da nakeji ya maye da bakin ciki , ba komai mutumun nan yayi ba illa tambayata ko nasan gidan wani Alhaji idris wai shida matarsa sun dade suna yawo sun kasa samu, dogon tsaki naja na sake kaloon sa sai lokacin na Lura da mace da take zaune kusa dashi Ashe kujerar ta kwantar Tana shayar da babyn hannunta, bansani ba na fada cikin masifa, ko nayi muku Kama da google aikin banza na fada Ina barin wajen. Kaloon juna sukayi suka saki Baki da mamakin wanan al amarin, ne take tunani da mutumin ya tambayi matar , ya za ayi na sani ta bashi amsa maybe ko tayi zaton you are trying to talk to toast her , dariya suka saki sanan y ja motarsa sukayi gaba , (Nima dai na tayasu dariyar)Nayi tafiya mai dan nisa Ina yi
Ina mitar wulakancin da akayi mun sanan na samu napep na hau , 20 minutes ne ya kawo ni gidan Zee , sosai gidan kato ne har y yafi gidansu , ae kuwa nasha kallo , Dan komai na gidan abun kallo ne, a nan yesmeen take fadamana ae ansaka ranar ta nanda 1 month haka mu fara shiri , sosai mun tayata murna .Karfe 6 daidai muka bar gidan amarya Zee , yesmen saurayinta yazo daukar ta haka itama ihsan, su ihsan ne suka rage mun hanya , na tsaya a bakin titi Ina Neman abun hawa , sosai Ina takaicin kullum tsayuwa Neman abun hawa duk sanda zani unguwa , motar da ta faka a gabana ne y saka na maida hankalina a kanta, tunawa nayi da guy din dazu hka yasaka na ja tsaki, sauke gilashin motar akayi , gamida slm, amsawa nayi sanan na hade Raina duk zato na abunda y faru dazu ne zai maimaita Kansa , you look so pretty Masha Allah naji na cikin motar ya fada , murmushi nayi Wanda ya yake karamun kyau , nace nagode for the compliment , Nvr mind yace Yana murmushi .
Daman cewa zanyi me mace so pretty takeyi a titi by this time , murmushi nayi sanan nace wlh gida zan karasa ne daga gidan kawata nake , idan ba damuwa hau na ajiye ki kinji , shiru nayi sanan nace Toh nagode , na bude kofar gaba na shige abina, ya sunanki ya tambaya Yana kalona, zaitun na bashi amsa , wow pretty name sunanki mai dadi by the way ni sunana Yussuf , hmm suna mai dadi na fada Ina kare masa kallo, ba laifi yanada nasa kyaun Aman Saidai ko kafar usman bai Kamo ba , sai naga kmar ma Bleacing yake yi aman ni wanan bai dameni ba naga alama yanada kudi ,
Munyi hira sosai y afadamun shi dan asalin dan Gombe ne a can ma iyayyensa suke , shine babba sanan shi yana aiki ne a wani company as md sanan Yana business yanada da kamfanin sarafa cement , cikin zuciyata kuwa dadi ne ya cikata yau na hadu da Wanda nake ta mafarkin aura .
Har kofar gidanmu ya ajiye ni bayan munyi exchanging number din Juna , na shige gida cike da murna
Bayan nayi sallah isha e na bi lafiyar katifa ta ina chat da Yussuf , yau na hadu dashi Aman jina nake kamar na dade da sanin sa , usman y kirani Aman ina kaloon ta har ta tsinke ban dauka ba
Wasa wasa yau watan mu daya da yussuf Aman kamar munyi shekara, mun shaku sosai kudi kuwa ko na tambya ko ban tambaya ba bani yakeyi, daga haduwata dashi ya siyamun latest iPhone , ya chanzamun wardrobe , ya zama na daina Aron na Maryam , duk lalurar kudi daga dubu 1 har 100k yaxamana zan iya kashe ma kaina , mama tasan da maganar yussuf Aman bata wani bashi mahimaci ba , a wata Dayan nan na Chanza nayi kyau kmar ba zaituna ba , rahma kuwa komai na bata bata karba , hassalima Saidai tamun wa azi Akan na ji tsoran Allah kar na yaudari bawan Allah usman , tun Ina zaginta idan ta ishe ni har takai saidai na bar mata dakin shikuwa usman duk ya rame ya fita hayavinsa , Farouk har ya gaji da fadan y dawo nasiha, idan yazo gurina sai naga dama nake fitowa idan kuwa yasamu na fito Toh saidai yayi hirar sa shi kadai ya tafi ni Ina chat da yussuf a waya , duk da wulakancin da nake masa Aman hakan bai saka yayi zuciya ba , sai ranar da yazo kmar kullum na fita ta fara chat Dina shi kuwa yayi shiru Yana kaloona
Mun Kai 15 minutes a haka , nikuma ko a jikina yau chat muke da yussuf Yana fadamun bayason loosing Dina and all , Aman Yana kishi saboda ya taba zuwa ya gani da usman, nace ya rabu dashi dan wahala ne, kawai ya cika maita ne Aman shi yussuf shine mijina , ban lura ba naji usman y fisge wayan , y hau duba chat din Kai tsaye y shiga chat Dina da yussuf da nayi masa save da my everything , y karanta komai da nake fada masa Akan usman , bani wayana tunda ba kai ka siyamun ba na fada Ina hararsa, ko saurarata baiyi ba ya shiga call log yayi dailing number dinsa "Dan wahala" shine yayi appearing a number dinaaa , zaitun ni ni ni ii n e e da -n wa-hala n-i y fada muryar da na rawa , eh din ko ba haka bane ba , idona sa ne ya kada yayi ja, Kansa Yana sara masa ya mikomun wayar tawa sanan y juya y bar kofar gidan ba tareda yace wani Abu ba nikuwa ko a jikina nace Allah y raka taki gona na shige gida abuna..

YOU ARE READING
BURINA(HAUSA NOVEL)
FantasyThis novel is about a young lady zaituna who was came from a poor background and Tries her possible means to fit in just to be with her friends who happens to be rich Sit back and enjoy 🩷