PAGE 7

140 3 0
                                        

📗📘📘📗BURINA 📗📗📗by Khadeeja Mustapha

PAGE 7

Gidan Maryam na nufa , a falo na sameta Tana Dana waya , ah zaitun kece kwana 2 Baki leko ba , nayi murmushi eh wlh amarya kinga dan Allah kawata ce zata zo Toh su mama basa nan Dan Allah shine nake tunanin na kawo ta nan wlh bazata dade ba ankona kawia zata bani ta tafi , shiru Maryam tayi sanan tace Toh zaitun ta zo babu komai , Ajiyar zuciya nayi daidai da sake shigowar kiran yesmen, na dauka gamida Nufar hanyar waje, hello zaitun haba tun dazu nke Kiranki kinki picking kinsa inata bulayi a titi , oh sorry yes Ina bacci ne kinzo ne na tambaya ta , eh Ina wani layi hka gurin mai fruit na tambyesu ko sunsan zaitun yace shi zaitun daya y sani wai yarsa, nace no zaitun din da nake nema babnta a abuja yake aiki ba ita nake nema ba danaga zai isheni kawia na siya fruts din sa na rabawa almajirai it's like the old man just needed money ba wani zaitun yarsa kudi ykeso kawai , ae take cikina y duri ruwa Aman danaji bata yarda da abinda baba yace mata ba sai hankalina y dan Kwanta Aman haryanzu da dan tsoro a Raina , aa ni bansan sa ba ni ba yarsa bace (what a life sabida abun duniya yara yanzu suke denying iyayen su , Allah y shirya mu gaba daya amin )na fada , nasani yesmeen tace nidai yanzu where is your house tiryen tiryen nayi mata kwatancen gidan Maryam , batafi 3 minutes ba ta kirani Tana gate , na ce ma Maryam zanje fito da bakuwar ta amsa da Toh saiki bata lemo da snacks ni zan hau sama kaina kedan ciwo yau janet ma bazata zo ba , so idan kungama just ki rufe falon bye

Dadi naji at least Maryam tabani waje bazata ji maganar da zamuyi da yesmin ba tagane fake life nakeyi a school

A gate tayi parking saboda tace ba dadewa zatayi ba , nayi mata iso har palon Maryam , na dauko mata drinks da snacks , na isketa Tana kaloon gidan hmm zaitun not bad gidanku nada kyau Aman kmar yayi karami, zaro ido nayi a zuciyata nace Toh katon gida kamar wanan ance masa karami Ina ga nakai yesmeen gidanmu saitace akurkin kaji ne Ina tunani, murmushin yake nayi , ta mika mun paper bag mai  kyau ga aso ebi dinki sai dinki , Dan Allah Karki kaima tailor ga fashion designers nan masu bala in wuta , mine will help nayi murmushi nawa ne, oh each outfit dai daga 100k Zuwa sama ne, ae bansan sanda na maimaita 100k ba da karfi, eh menene zaitun kmar wace nakira mki 100 million , aa na wayance na ji yayi arha ne yesmeen kibari kawai zan kaiwa nawa ita daga 200k takeyi gskia I don't like cheap things na fada Ina kara jadada dubu dari a Raina , Toh fine tace ni zan wuce saimun yi waya ko , har motarta na biyotaa mukayi salama na koma ciki , kayana na kwasa Ina mitar 100k Dina da aka ci wlh nasan da kasuwa  naje baxan kashe haka ba yanzu Gashi Tana mun maganar wani kudin dinki kmar wace nace zan biyama duk yan matan amarya kudin dinki, salihu mai dinki na zan kaima na biya dubu biyu na Zuwa uku lol 😆 nidai nace

Ina komawa gida mama ta hauni da fadan tun Yaushe ta aikeni aman saboda na rainata zan ki zuwa natafi yawo na , sai babanmu ne da Kansa yakawo cefanen dayaji shiru shiru banje ba , Hakuri kawai na bata na shige dakina Ina addu ar da Allah ya fitar Dani nidai yau .

Washegari na shirya don kaiwa salihu taila kayan, lissafi yamun kudin a y Kama 20k  Kala biyu daman Kamu ne sai dinner , da kyar salihu y rage mun mukayi zan bashi 12 , nayi masa sallama natafi , Ina tunanin yadda zan samu 12k nabashi Sbd bikin saura sati guda

Bayan sallahr Isha e na samu baba Yana lazimi a daki , Saida y gama yayi addu a sanan y kalleni zaituna y akayi , hmm daman baba a makaranta ne akace Wai mu siya littatafai kuma dole ne, gyada Kai baba yayi sanan y yace nawa ne kudin , na ce hmm daman dubu ashirin ne, ashirin baba ya maimai ta , eh na amsa , zaituna yanzu wlh banida kudi sai kudin ajiya dubu 10 sai kudin makarantar su bashir 15 aman zan baki yanzu 20 din saiki samu ki siya sai nasan yadda zanyi na samu na basu ko , to baba na furta kmar da gaske littafin zan siya. Gobe da safe zan saka mamanku ta Baki , godiya na masa gamida tashi nayi masa Saida safe na Koma daki na hau chat a group din bikin zee anata shirye shirye na bikin ya yan masu dashi , ni bnida idea saboda bantaba Zuwa bikin masu kudi ba haka , wanan ne karo na na farko kuma naci Alwashin na dinga Zuwa kenan har saina samu mai kudi na aura

BURINA(HAUSA NOVEL)Where stories live. Discover now