Page 24

136 3 0
                                        

📘📗BURINA 📗 PAGE 24
Written by Khadija Mustapha
 
Da Asuba natashi nayi alwala nayi sallah , na dade akan sallaya Ina addu a Allah ya fitar Dani daga cikin wanan halin da nake ciki

Karfe 7 naji hayaniyar yan gidan da ga alamu sun tashi , da sauri na fito na tarar da maman na kiciniyar hura wuta , gaishe ta nayi ta amsa ba yabo ba falasa sanan tace Yauwa zo nan zaitun kike ko man zaitun zo ki huramun iccen nan , haka na karasa jikina duk ya mutu na hau hura Icce , sosai nasha wahala sanan nasamu ya Kama ga makogaro na ya bushe rabona da ruwa tun jiya kafin mu bar gida, gahshi Inason tanbayn ruwa Ina tsoran rashin mutuncin da akayi mun jiya, daga jiya Zuwa yau nayi Dana sanin aikata abubuwa dayawa a rayuwata, na farko cin mutuncin da su karima suka mun haka nake ma raham kuma bata taba danuwa ba , Ashe haka ake ji idan mutum ya ci mutuncin ka , sanan hura iccen nan aikine da tun tasowa ta mama ce kuyi kuma bana tayata komai saina ga Dama  gashi yanzu nice nakema wata wace bata ganin ma mutunci na ,

Dumamaen Tuwon jiya aka Kara bamu da kunu haka na tura badan Raina naso ba , Ina gamawa aka loda mun uban wanke wanke , shikuwa yussuf tun jiya ban kuma saka shi a ido ba

Wasa wasa a hka nayi sati 3 ba yussuf ba alamar sa , mama kuwa sai masifa take Wai tagaji da cigar Dani dan haka na fara bin su Karima siyarda wake da shinkafa a cikin kasuwar garin , sosai abun y bani mamaki Toh su waenan basu San hakkin aure bane ba Ko me , a yau da yamma sai ga yussuf ya dawo bayan ya huta nace bara na fada masa abunda mahaifiyarsa ta fada duk da nasan bayana zai bi a wanan karon baxai yarda ba , Saidai sabanin hakan ne ya faru nan yussuf yace tabbas sai na bi kanensa Zuwa kasuwa siyar da abinci daman shi baxai iya ciyar Dani ba hakama bazan dorawa mahaifiyarsa nauyi ba , a ranar nayi kuka da Dana sani ba adadi,

Washe gari kuwa bayan nayi aikin da na sabayi da yaxama aikina dole sainayi ko inajin dadi ko banaji, ciki Kuwa banyi sati 2 ba ya bare tsabar wahala da aikin da nake yi ,

Da rana bayan na daga uban shinkafa da wake haka muka Kama hanyar kasuwar dan siyarda abinci, tausayin kiana naji Wai ni zaitun nice na koma yar tuwo tuwo , kwalla ce ta zubo mun cikin dabara na share , haka muka siyarda shinkafa da wake dai tas , yau naga mutane Kala Kala , da waenda zasu Yaba maka magana sai wanda zai maka tsawa da Wanda zai nemi ya fada maka mganar banza Nikam yau zaituna naga rayuwa su kuwa su Karima b kamun Kai kowa ma wasa suke dashi na fuskanta nidai bance musu komai ba kawai kallonsu nakeyi Ina mamakin irin rayuwar da suke , ga shigar banza da sukeyi Wanda ko da wasa maman bata taba yimusu magana akai ba , a iya xanman danayi a gidan na fuskanci kowa kawai abinda yakeso shi yakeyi a gidan .

Yau wata na 2 tunda yussuf ya baro ni da gidanmu da yan uwana , duk na Chanza kamar ba zaituna ba mai surutu da son gayu duk na rame nakoma abun tausayi duk da tallan da nake musu hakan bai sa Ana bani ko sisi ba, ko yabo na ba a tabayi ba duk da yadda nake kokarin siyarda komai sabanin da da ake kwantai, wasu dayawa sun dawo siyan abincin mu sabida su samu fuska a gurina Aman hkan ya gagara duk da haryanzu bansan wani irin rayuwar aure muke da yussuf , ba ci ba sha ko ganinsa bana yi sai jifa jifa, duniya ta mun zafi ko nace zan gydu ba kudin mota a gurina , haka na hkura na zubawa sarautar Allah ido .

A gida kuwa sai nema na akeyi Aman har yanzu bawanda yasan Inda yussuf ya kaini, gidana kuwa ansha Zuwa Aman Saidai a tatar da hajiya jamila kuma tayi musu warning da karsu Kara Zuwa Nema na Dan bana gidan kuma idan suka dawo saita saka an kamasu, haka su baba suka dawo gida aka cigaba da addu a ,

Rahama tashi ga damuwa dan gani take yussuf ya siyarda yar uwarta shiyasa haryanzu ba a samu ko labarinta bane , duk da abun alkhirin daya same su na samun aikin usman da Bashi mota da katon gida da company din da yake aiki sukayi, Aman har yanzu Farin ciki y kaurace mata na rashin zaitun , kullum usman Yana cikin rarashi Aman taki hakura.

Yau yussuf ne yazo gidan bayan nayi wata kusan 1 ban saka shi a ido ba , ya cire Kayan sa yace Zai shiga wanka sanan yazo ya tafi kasancewa yau din Ana rana , kuma yau mama tace baxa a fita Tallah ba sboda Karima bata Jin dadi kuma bata yarda data bani dukiyar ta ba nikadai batareda Karima ba , dan haka yau ba tallah

Ina ganin ya shiga wanka na samu na laluba aljihun sa aikuwa na samu kudi yan dubu har 5 , na kuwa dauke duka na tura cikin Rigata na zauna kmar banyi komai ba , Yana dawowa rigar sa kawia ya zarga yace mun Nina wuce sai kuma kin Kara gani na ya saka Kai ya fice , Yana fita na saki ajiyar zuciya dan nayi zaton zai duba kudin nasa .

Washe gari kuwa na yanke hukuncin gudu wa daman kudin mota ne ya hanani aikata hakan , Aman tunda nasamu babu abinda zan zauna jira. Yau bayan mun fita tallah, muna cikin siyar da abinci nace ma Karima zanje gidan wanka domin nayi bayan gida , kalona tayi sanan tace Toh Aman wlh na tabbata karna dade , na Toh na bita sanan na wuce na tafi, hanyar fita daga kasuwar na nufa , Ina Zuwa bakin titi na tare adaidaita Sahu nace ya kaini Tasha , ko tsayawa ciniki banyi ba na shige muka dau hanyar tashan Kano

Muna zuwa na biya mai adaidaita Sahu kudin sa na shige tashan , Inda ake lodin Kano na tambaya aka nuna mun , nayi sa a kuwa Ina Zuwa mota saura mutum daya dan haka na biya na shige wa ta cike da Farin cikin samun yanci yau , Karfe 6 na yamma muka sauka a Kano , mai napep na tare na yi masa kwatancen Inda xai kaini , har kofar gidan mu ya ajiyeni na Bashi kudinsa na shige gida da gudu , mama na tsakar gida tana gyaran zogale suna hira da Bashir taji na shigo da gudu , da sauri na fada jikinta Ina kuka mama ki yafemun mama na tuba , zaitun daman zamu Kara ganin ki mama tace Tana hawaye , rungume ni tayi sosai gaba daya muka saka kuka ita kukan yadda taga nakoma nikuma kukan nadamar bijire musu nayi , Saida mukayi mai isar mu sanan mama tace bashir yaje ya Kira baba yace nadawo sanan ta Kira usman a waya ta sanar dashi , sosia ya taya su Farin ciki sanan ya yi ma mama alkwari Insha Allah bayan Magrib zasu zo da rahama .

BURINA(HAUSA NOVEL)Where stories live. Discover now