📗📗📗📗BURINA📗📗📗khadija
mustaphaPAGE 8
Washegari kuwa kamar yadda baba yamalkawari mama tabani 20k , murna kuwa kuzo kugani haka naje na mikama salihu Taila dubu 12 na ajiye sauran kudin don biyan kudin makeup .
A kwana a tashi yau saura kwana 2 a fara biki , muka shirya yesmen zata zo ta dauke mu muje saloon , kamar nace bana Zuwa Sbd a rayuwarta ni bantaba Zuwa ba , da karkashi nake wanke kaina a gida , aman saboda kar na nuna wani abu na yarda zan bisu, gidanmu yes me tace zata fara Zuwa ta dauko ni sai su dauki zee da ihsan at last , tunda tace Tana hanya na shige gidan Maryam , muna dan taba hira, yesmen na Zuwa ta kirani na fito muka tafi , muka biya gidansu amarya zee , ae gate din gidansu zeee ma abun kallo ne, haka ihsan , nan sai nasha jinin jikina , aman haka baisa naji Wai zan fada musu gskiyar ko ni wacece ba
Bamu tsaya a ko Ina ba sai wani katafaren saloon daga gani kasan na masu kudi ne, nayi shiru Ina kallon saloon din , let's go girls yesmeen tace bayan ta gyara parking , muka fito kowa das das ,
Tv saloon din y koma mun don kuwa ni bantaba ganin saloon mai kyaun wanan ba akwai salon a unguwar mu na mama blessing kuma a da Ina admiring dinsa Aman Ina ganin wanan sainaga kmar saloon din mama blessing y koma kmar ba komai ba ,
Watace ta zo ta tarye mu Tana mana sannu da Zuwa , zee ce tace I want to relax my hair and also do pedicure and manicure pls vip mukeso , da sauri yarinyar tace okay ma pls come with me , muka tashi muka bita vip section din , wow na fada Ashe regular din ba komai bane compare to vip section nan nakuma samun Kwatin gwiwar gani BURINA ya cika na auren mai kudi .
Kowa ta fadi ahinda za a yi mata , ni bana saka relaxer dan haka matar tamun suggesting seaming , I have never experienced it and na Basar dan karsu Raina ni , aka wanke sanan aka sakamun man steaming aka tura kaina a dryer , ae at first naji dadi Aman Kunsan steaming da zafi idan dryer ta dau zafi hka na dinga hada gumi kmar zanyi ihu Aman na dake duk dan kar na bada kaina ,
30 minutes dinana kmar hour 30 nayi hka naji Sbd a zaba kuma nakasa complain, an gama mun aka zo pedicure Anan dai ban nuna kauyanci ba .
Hour 2 aka gama da kowa daman yesmeen ce ta dauki nauyin kowa so kawai biya tayi muka tafi , da ace ance kowa saidai y biya ma Kansa Toh da kashi na nasan ya bushe .
Su zee aka fara ajiye wa a gida sanan aka ajiye ni . Yauwa zaitun gobe 10 pls no African time mu hadu a gidanmu idan yaso sai mu je gidansu zee din tare , amsawa nayi da to mukayi sallma, ina tsaye a kofar gidan Maryam har yesmen ta sha kwana sanan na shige gidanmu .
Gobe tun da safe nacema mama kunshi zanje gidansu amarya dake a can duk a za ayi mana kuma zee ce zata biya , mama ta kalleni meyasa bazaki je gun ummi mai lallen ku ba sai kinje wata uwa duniya, da ba gun ummi din kike ba sai yanzu kuma zaki dauki jiki ki tafi can wata unguwa , tsaya ma meyasa ban taba ganin kawayen naki sunzo gidan nan ba , eh ta tsare ni da ido alamar Tana bukatar amsa
Toh mama ba school bane yasa basa yawo ba , kuma ummi ae yanzu saidai tayima rahma Aman ni na wuce ajinta , kalleni fa mama , Kinsan nawa za a biya duk hannu fa 3k ita kuma ummi dari 500 takeyin hanu duka biyu fa haba mama na girmi kunshin 500
Kallona mama ta shiga yi ta rasa wanan Hali a Ina zaitun ta samo shi, Allah y kyauta kawai tace sanan ta ce Nidai ki San mastayin ki shine kullum nasiha ta dogon BURI ba abinda zai haifar mki sai nadama.
Cigaba da aikinta tayi nikuma na tashi dan na shirya , Ina gama shiryawa nayima mama salama na fita bakin titi Neman napep
Ba wahala nasamu na kwatanta masa Inda xai kaini dukda wanan ne rana ta farko da nafara Zuwa gidansu yesmeen , munyi tafiya mai niss sanan muka shigo unguwar su, wani esstate mai kyau , kaloon gidajen unguwar na hau yi ina yabon kyaunsu da tsaruwar su a zuciayata kuma ina dada tsinewa talauci
Muryar mai napep ne y kaste mun tunanin da na tafi yi hajiya ga number 12 din , oh na fada na Sauko nabashi kudin sa tare da kwankasa gate din gidan Wanda shi kadai ma abun kallo ne .
Maigadin su ne y fito na fada masa gun Wanda nazo y mun iso Sbd yesmeen ta fada masa before nazo , mai aikin gidan ce tayi mun iso parlon bakin su Wanda y gaji da tsaruwa Gskia dole yesmeen tace gidan Maryam yayi mata karami, a shigowana ma naga masu aiki sun Kai 4 gskia ba karamin gida bane
Nan da nan aka kawo mun kayan snacks Wai nafaraci kafin yesmeen din ta sauko nayi godiya , nafara ci wani abun ma ni ban taba ganin sa ba ,
Yesmen Saida ta kwashe 30 minutes sanan ta shigo, bamu bata lokaci ba muka nufi gidansu zee ,
Gidan a cike yake da yan biki , wani part na gidan zee ta shigar damu wanda har y gaji da haduwa a hakan ma ba shi bane main palo na gidan ,
Anyi mana kunshi wanda kana gani kasan na manya ne , kowa y fito yayi kyau Masha Allah
Sai yamma likis na koma gida duk a gajiye, rahma na gani na ta tabe Baki yanzu wanan ne kunshin da akace ummi mai lalle bata iya ba , harara na Galla mata eh din zata iya ne
Kwafa rahma tayi Allah Anty ummi zata yi mki kuma naga ae da itace Keyi mana har ke din , kamar zan daki rahama nayi na mata warning da karta Kara shiga sabga ta ..
![](https://img.wattpad.com/cover/368980426-288-k701212.jpg)
YOU ARE READING
BURINA(HAUSA NOVEL)
FantasyThis novel is about a young lady zaituna who was came from a poor background and Tries her possible means to fit in just to be with her friends who happens to be rich Sit back and enjoy 🩷