📗📗📗BURINA📗📗written by Khadija Mustapha 📗📗📗
Page 15
Washe gari Da dare dukanmu muna tsakar gida ana Shan iska sabida zafin da yayi yawa kwana 2 , yaro ne ya shigo Yana cewa Ana salama da baba inji mallam Garba , baba ne yacema dan Aiken yace Yana zuwa , baba ne yace ma mama Yana Zuwa bara ya duba ko waye , da Toh mama ta bishi sanan baba y fita , mukuwa muka cigaba da hirar mu
Ko da baba ya fita su mallam garba suna tsaye su uku , hannu baba y mika musu sukayi musabaha, mallam garba ne ya gabatar da Kansa a mastayin kawun usman , baba ya saki murmsuhi Masha Allah usmanu yaro mai hankali, Toh shine yaro ya ce a zo a tambaya masa auren yar wajenka , murmushin baba ya karu ya ji mganar da mallam garba ya fada bara a dauko muku tabarma wanan mgana bata tsaye bace , baba y shigo cikin gidan da sallma, ah maman zaituna dauko tabarma manyan Baki ne suka zo , da to mama ta amsa ta tashi ta dauko ta bawa bashir suka nufi Zaure da baba bayan ya shaidawa mama zai yi mata bayyani idan yadawo.
Mukuwa shiru mukayi Kap cikinmu babu Wanda yasan abunda yake faruwa ,
Can wajen kuma bayan su mallam garba sun zauna aka sake gaisawa sanan suka Kara jadada su Neman aure ne yakawo su ,kuma su da kudin aure sukazo , Masha Allah baba yace sanan a lokacin mallam yunusa makocin mu kuma aminin baba y shigo zauren bayan baba y aiki bashir da ya kirashi, gaisawa sukayi sanan baba ya Shaida masa abunda yake tafe dasu , sosai mallam yunusa yaji dadi Dan ba Wanda bai san usman ba , tun sanda ya fara Zuwa gin zaitun Saida ya nemi izini sanan y fara Zuwa zance kuma baba ya saka akayi bincike Akan sa , kowa ya tambaya yabon kyawawan halayen sa akeyi , hakan ysa baba yima zaitun kwadayin auren usman
Kudi su mallam garba suka fito dashi naira dubu talatin a mastayin kudin nagani Ina so , a nan aka tsayar da lokaci nanda wata 6 masu Zuwa , cikin mutunci aka gama suka tafi baba kuma sukayi sallama da malln yunusa ya shigo gida, an kawo mepa dan haka nida rahama muka shige daki mama ce kawai ya tsakar gidan , bayan baba ya sanar wa da mama duk abinda ya faru sosai ta nuna farin cikinta, suka fara tautauna yarda za ayi Kayan daki, baba ne yace kinga yanzu saina je na daga wanan gonar na siyar a harhada ayi mata Kayan daki n , eh Nima Ina dan aji yar kudi na kaga yanzu sai naje kasuwa na fara siyan kayana kitchen mu harhada , eh karbi wanan kudin saiki hada Dana hanunki , godiya mama tayi sanan suka kwanta cike da farin ciki ,
Washe gari bayan mun gama karin safe baba yayi Gyaran muryar sanan ya kalleni , zaituna y kira suna na , na am baba na amsa , Kinsan usman dai koh , eh na amsa , Toh jiya da kijaga na fita iyayensa ne suka zo kuma sunzo kan magnar auren ku dashi, yanzu dai sun kawo kudin aure kuma na karba nanda wata 6 auren ku dashi , yanzu saiki fara shirye shirye , Allah yasa ayi damu ,
Bakin ciki, tashin hankali duk sune suka ziyarce ni a lokaci Guda , na rufe idona na ce Sam ni bana son usman Inada Wanda nakeso , baba ne cikin kwantar da murya yace zaituna naga yaron nan Saida yazo Neman izini kuma nakira ki kikace kina sonsa shiyasa har na yi karambani na ansa da na basu ba tareda naji daga bakin ki ba , kiyi hkuri ki aure shi Insha Allah shi alkhiri ne a gareki, ae kamar baba ya karani na Kara daga murya cikin karaji wlh ni baba banso wlh kuma kukmun dole saina gudu , na shiga duniya
Sosai ran baba ya baci , mama kuwa tashi tayi ta kwada mun Mari baba ya mata magana da ta. Kyaleni rahama kuwa jikinta har rawa yakeyi kamar tabtashi ta rufe ni da duka saina daina mosti sanan ta sakeni, na Bari soyaya ta rufemun ido na bata ran iyayena Wanda sune gata na duniya ,
Mama ce ta ce wlh saina aure shi ko zan mutu, da wani irin kuka na fa she dashi nace wlh ni ban sansa kuma wlh idan na gudu ba Wanda zai kuma gani na , rahma ce ta tashi cikin bacin rai tana huci ta kalleni sanan ta kalli baba , baba ni zan auri usman na amince , kekuna ta nuna ni wlh Allah baxai barki ba , ga alhakin bawan Allah gana rashin biya ya da kika ki ma iyayen ki sabida son zuciya da kwadayin abun duniya , Tana kaiwa daidai nan kuka yaci karfinta ta bar dakin Tana kuka mai cin rai
Baba ne ya kalleni idon sa y kada yayi ja , zaitun ya kira sunana kije ki fadama Wanda kike so din ya turo da iyayayensa nayi alkawarin zan Baki shi , fatana Allah yasa alkhairi ne kije dakin ku, murmushi nayi sanan na gyada Kai na fice ko a jikina .....

YOU ARE READING
BURINA(HAUSA NOVEL)
FantasyThis novel is about a young lady zaituna who was came from a poor background and Tries her possible means to fit in just to be with her friends who happens to be rich Sit back and enjoy 🩷