Page 16

134 3 0
                                        

📗📘BURINA📗📘 written by Khadija Mustapha   📗📗📗
Page 16

Ina shiga daki na kalli rahma da haryanzu kuka takeyi marar sauti, na saki tsaki sanan nace daman ke ce kika dace da usman ba ni ba , Ashe tun wuri Yana da ajinsa y Bari yake batamun lokaci kuma wlh tunda kece kika ce kinji kin gani sai abunci ya gagareki a gidan usman , banza kawai

Dago kanta rahma tayi Tana kallona da idonta da taci kuka har ya kumbura, murmushin takici tayi sanan tace naji kuma zan baki mamaki Insha Allah sai usman ya zama abun kwatance kuma Allah yaga zuciyarsa all he does is make you happy Aman ke you are selfish , bakya tsoran alhaki zaitun , Aman Allah baya bacci zai saka masa

Tabe Baki nayi sanan nace kece dai zaki sha mamaki da talaucin usman bani ba , tunda ke kin zabi mastiyaci sai kije kiyita fama na tashi na fita daga dakin ma gaba daya .

Baba da Kansa yasa aka kira masa usman yayi masa bayani sanan yace shi ya bashi rahma, sosai usman ya kadu da Jin wanan magana ta zaitun , Toh dan meyasa zata aiko masa wanan text din ko daman dan duk taci mutunci sa ne , zazabi yaji ya rufe shi a haka dai ya lalaba ya tafi gida

Yana Zuwa gida ya sanar da umma mahaifiyarsa, sosai taji hushi kuma taso Hana usman din ma tayin aura masa rahama da akayi , Aman saitaga gwanda rahamar dan tama fi yabawa da hankalin yarinyar ,nasiha mai kwantar da hankali tayi masa ta nuna masa daman zaitun din ba alkhairi bace a garrshi shiyasa hakan ta faru,

Yau sati 2 da faruwar wanan al amarin, a bangaren rahma da usman kullum cikin kunci suke , sabannin zaitun da yussuf Wanda su sai shan soyayar su suke abun su , yau ce ranar da yussuf  yace zaizo ganin baba kafin daga baya a zo ayi maganar aurensu, murna kuwa gurin zaitun ba ma magana

Bayan sallahar isha saiga yussuf , yaci manyan kaya abunsa , duk da ba wani kyau ne dashi ba Aman dan gayu ne na karshe , a Zaure akayi masa shimfida , bayan baba ya fito suka gaisa , yayi masa tambayoyi ya amsa , baba ne yace zaiyi bin cike dan haka ya basa lokaci zai neme shi Insha Allah , da Toh ya amsa y fito da kudi bandir 2 yan 500 ya ajiye gashi wanan baba ba yawa , girgiza Kai baba yayi sanan yace Aa yaro nagode Aman ka rike bana bukata Aman an gode sosai .

Yussuf ba yarda baiyi da baba ba Aman yaki karba haka ya hakura yayi masa salamaa ya tafi

Duk binciken da baba ya Dace yayi , yayi dan haka ya fadama zaitun data fada masa ya turo iyayensa a tsayar da ranar aure

Ranar da baba ya Sanar Dani nayi farin ciki sosai harda  rawa , na dinga yadawa rahma habaici itakuwa ko kallo ban ishe ta ba ,

Yau aka saka rana na da yussuf daidai da bikin su rahma, naira dubu 200 y kawo a mastayin kudin nagani inaso Dina , na n ma na dinga yada habaici Aman rahma ko ta dago Kai ta kalleni bata yi ba hka na karaci habaici na nayi shiru

Dana fadama hafsa sosai tayi takaicin rabuwa ta da usman , Aman hka ta hkura ta mun Allah y sanya alkhairi , muka fara shirye shiryen biki ,

A bangaren usman kuwa ya dan fara hada yar lefensa da taimakon umman sa , kaya yake siya daidai karfin sa , Saidai har yanzu ko number din rahma bayada shi, ya rasa wanan wani irin aure zaiyi da bayada maraba da na dole .

Farouk kuwa abokinsa ya taya shi murna , abokina wlh bakaji dadin Dana ji ba ya fada bayan sun hadu , hmm kawia usman yace , kaga mallam kawai mantawa zakayi da zaitun Kayi transfer din duka soyayar da kake ma yayar ya koma kan kanwar, ni Ina ji a jikina itace mai share maka ha waye , Dan haka cheer up yau ka shirya Kaje gidan ku fuskanci juna wlh zaka samu relief kadaina azabtar da kanka da zuciyar ka akan wada bata ma son kanayi ba .

Sosia ya dauki shawarar Farouk wanan karon dan hka anyin Isha e ya shirya tsaf ya Kama hanyar gidansu zaitun Saidai sanan lokacin bada niyyar ganin zaitun ba sai rahma

Rahma na zaune a salaya Tana karanta wani lit tafi taji slm yaro Wai Ana salama da ita inji usman , daram gabanta ya fadi , usman kuma taji zaitun ta fada Tana dariya , kice yau soyaya za a sha ,, Allah y raba mu da talauci , ko kallonta banyi ba na tashi na chanza hijab na fita , mama na sanarwa sanan na fita gabana na faduwa dan yau ne rana ta farko Dana fara zance kuma ba da kowa ba da saurayin da yayata tace bataso Nina karba dan farantama iyayena.

A kofar gidan na gansa ya hade hanayensa a kirjin sa , sai yau nayi masa kaloon tsaf , Masha Allah na fada a cikin zuciyata ga kyau ga hakuri na ayana a Raina , da sallama na isa na tsaya dan nesa dashi , na Dan risina kasa gamida gamida gaishe shi

Lafiya lau ya amsa shima Yana Yaba sanyin Hali irin na rahama Masha Allah ya firta a filli, kingani yau ko ya fada Yana kallona

Kasa nayi da kaina sanan na gyada kaina alamun eh , Kinsan dai duk abunda ya faru inaso ki saka a ranki Insha Allah bazakiyi nadamar zaba na ba a mastayin mijinki, zan kula Dake Insha Allah,

Nagode yaya na fada Ina murmushi , sai yaga na koma masa kmar zaitun da sauri ya chanza tunani dan yanzu zaitun ta haramta a gareshi ko bai auri rahma ba ya haramtawa Kansa ita kuma zuciyarsa ma bazata taba yafe mata ba

Mun dan taba hira Wanda yasaka komai ya chanza daga bisani mukayi sallama y tafi bayan ya karbi numbern wayana ,

Tun daga ranar soyaya mai karfi ta shiga tsakanina da usman , kowanen mu Burinsa ya kyautatawa dan uwansa sabanin da da son maso wani usman yakeyi Wanda Hausa wa suka ce koshin wahala,

Nikuwa sai lefe muke hadawa na gani na fada Nida yussuf , komai nace Inaso shi ake siya , a waya yake turo mun saina zaba , idan nace masa zanje na siyo ya bani kudin sai ya ce Aa baya son na sha wahala nayi. Zama na , ban kawo komai ba Dan haka duk abunda ya tura mun yace na zaba nake zaba sosiai ko kuma na tura masa Wanda nakeso  , planing biki kuwa saiyi mukeyi Dani da su yesmeen abun dai sai dadi yakemun banida damuwar komai abuna.

BURINA(HAUSA NOVEL)Where stories live. Discover now