PAGE 5

74 0 0
                                    

📗📗BURI 📗📗by Khadija Mustapha
PAGE 5

Yau mukayi da usman Zai kawo mun kudin da yamun alkawari, tun safe na tashi da farin ciki saboda yadda nake ganin ae kamar nasamu mai kudi na gama , saboda farin cikin da nake ciki ko jiran mama banyi ba na hau aikin gida , Saida na gyara ko Ina a gidan tsaf dashi sanan na koma daki . ,
Mama ce ta fito , yau ta Dan makara saboda Tasha maganin mura da dare jiya , mamakin gidan tayi sabida tasan rahama bata nan taje gidan kanwarta da kwana , Kiran zaitun ta shiga yi , na amsa Ina fitowa daga dakinla mama nice fa yau kawai nishadi nakeji shiyasa , gyada Kai mama tayi ba tare da tace komai ba daman ita ba mutum bace mai son magana .

Bangaren usman kuwa tunda zaitun ta fada masa maganar kudi y bi yashiga damuwa wata zuciyar ta fara blaming kansa da bai fito y fada mata wanan karon ma ba yadda 100k din dazai bata , wata zuciyar kuma tana cewa ae dole ya samu y bata , balance dinsa y duba a account dinsa , dubu 10 ne kawai a account din ko rabin kudin ma bayida shi gashi wata ko tsakiya baiyi ba ballantana yayi ma principal magana a bashi Albashin sa y hada .

Gumi ne y keto masa a gaskiya Yana son zaituna sanan bayason abunda zai saka y rasata, option dinsa jafar nr kuma shi kafin y basa aron kudi sai yayi masa fada saboda yasan zaitun ce kawai kesa usman Neman kudi rance

Ba don yaso ba haka ya yanke hukuncin mai taimakonsa wanan time din ma jafar ne kawai , abokansa biyu ne kawai shi mutum ne da magana bata dame shi ba , jafar da muktar ne kawai abokansa , jafar ne yake aiki a bank Shima as customer care , muktar kuwa ba aiki ne dashi ba a shagon babansu yake a rabe a kasuwar kwari

Waya y dauko y danna kiran jafar , hello abokina kana gida, eh jafar y amsa , Toh gani nan Zuwa yace Yana mikewa, dakinsa y rufo y fice daga gidan .

A kofar gida y samu jafar , suka fara zolayan juna sanan usman y dan bata rai alamun serious magana zasuyi, ya ne usman y naga mood Dinka ya chanza ? Hmm jafar dan Allah Aron 100k zaka bani wani Abu ne y taso mun urgently

Rausaya Kai jafar yayi hmm zaitun again y fada a dan hasale, no usman this time wlh abun school ne y taso mata , jafar y kalleshi kaloon bkada wayo haka ita zaitun din ta fadamka Wai tsaya ma sai Yaushe zaka gane wanan yarinyar ba sonka take dan Allah ba , ta maida Kai ATM dinta ne kawai , usman ne y kara kwantar da Kai , abokina I can't say no to zaitun wlh Ina sonta kana fadan hakane don haryanzu Baka samu Wanda kakeso bane 100% Aman da zaka gane abunda nake nufi , yanzu Nidai dan Allah kaine kawai hope Dina

Murmushin takaici jafar yayi sanan yace bazan Baka aro ba this time around usman , zan baka kudin kyauta na Dan samu bonus wanan lokacin a gurin aiki , zan mka sending yanzu Allah y Baka ikon ganewa zaitun is not the person you thought she is

Godiya usman yayi masa sanan sukayi sallama y wuce cike da farin ciki don samun aboki haka zaiyi wuya , wata zuciyar ta na son yarda zaitun yaudarar sa take wata zuciyar kuma taki aminta da haka .

Karfe 8 na dare usman y aiko aka Kirani, ko minti daya ban Kara ba na fita sabanin da dasaina tsayar da usman fin 30 minutes sanan na fito kuma ko arzikin gaisuwa bazai samu ba , haka zan ta hade rai Ina basarwa.

Kwarai yayi mamaki kuma maganar jafar ta Dan so tayi tasiri a kansa Aman dake so Hana ganin laifi sai ya share y Hana zuciyar sa yarda da abinda take shirya masa .

Sosai muka sha hira kamar ba nice zaituna mai sha masa kamshi ba, haka kuwa ba karamun farin ciki y saka shi ba , bayan mun gama hirar mu y mikamun kudina nikuwa na karbe nayi godiya for the first time haka kuwa y kara saka shi cikin Nishadi and he believe na chanza , nan kuwa y share zancen jafar na zaituna ba sonsa take ba using dinsa take . (Allah sarki usman )

BURINA(HAUSA NOVEL)Where stories live. Discover now