Page 21

138 2 0
                                        

📗📚BURINA 📗 written by Khadija Mustapha

Page 21

    Haka na shiga kitchen na hau yin aiki , Ina kammalawa na zuba a cikin food flask na Kai saman dining na ajiye , Yana chat a wayarsa na sameshi na ce masa nagama , Kai ya gyada sanan ya tashi , zuba masa nayi nasaka masa spoon , kallona yayi sanan ya cire spoon din yasa hanunasa da ko wankewa bai yi ba yau hau cin abincin Yana wani irin tauna mai Kara , sanan yasa yasta ya kwakulo Wanda ya ke cikin bakin sa ya hada ya cinye , Yana gama wa ya shiga lashe hannu , naman ya kirga tsaf sanan ya kalleni Allah ya soki Baki taba mun ba da yau sai kinyi mamakin wanene yussuf , kallonsa nayi at this point na gama tsorata da lamarin yussuf , haka ya saka naman nan a gaba ya cinye abinsa idan wani ya makale masa a hakora ysa toothpick Yana cirewa Yana cinye abunsa ko a jikansa , tashin zuciya kallonsa yasaka mun haka na tashi da gudu na shige bandaki na shiga amai sosai , kamar zan amayar da hanjin jikina haka nayita amai Ina hawayen bakin ciki .

A bangaren usman kuwa soyaya suke da rahma mai tsafta abunsu gwanin sha awa ,tare suke aikin gida sanan suyi breakfast , sanan shi ya tafi wajen aikin sa itakuma ta zauna a gida, abunsu gwanin sha awa , a kullum Tana tunanin yar uwarta zaitun ko yaya take ciki  oho, Aman Tana missing dinta dukda ba sani shiri suke ba .

Ni kuwa a bangare na wasa wasa na kasa gane kan yussuf , ga wani Abu da ya tsiro dashi , baya fita sai yamma likis zaiyi wanka sanan ya fita bazan Kara ganin sa ba sai karfe 11 watarana har 12 , tsakanina dashi sai masifa da hantara, kazanta kuwa ba a magana haka zai shiga bandaki yayi abinda zaiyi yaki flushing, ya dauki dan kwali na ya face majina abunsa, in takaice muku magana ko wankan tsarki yussuf bayayi sai ya ga dama , ballantana yayi wani sallah ,haka idan zai fita zai rufe kitchen Wai karna kwashe masa Kayan abinci nakai gidanmu.

A wata biyu na rame na lalace banida aiki sai kuka da Dana sani .

Yau gidansu usman sun tashi cikin Farin ciki , gurinda usman yayi interview ne suka kirashi sanan suka bashi md a company din , murna gurin rahama ba a ma magana , daman duk wani jinkiri alkhairi ne sai yanzu ya tabbatar da haka

A bangaren su zaitun kuwa yau muka tashi cikin tashin hankali dalilin samun cikin danayi , haka yussuf ya rufe idon sa yaci mun  mutunci Wai shi bai shirya haihuwa ba , tashin hankali mai sunan tashin hankali na shige shi , haka yayi tamun tijara daga baya ma da yaga hakan baiyi masa ba ya shiga zagina da iyayena, nan na tashi nace ya Daina hadawa da iyayena dan ba laifi sukayi ba shi ya nemi aurena kuma suka bashi dan haka su ba abun wulakantawa bane , tashin hankali wanan magnar danayi ya kuma hargista shi yace zaitun kenan har kin manta da irin rashin kunyar da kikayi ma iyayenki akaina ko kin dauka zaki ci bulus ne , hmm kin yaudari Wanda yake sonki dan Allah kin bi mu masu abun arziki hmm zaituna kenan har yanzu Bakisn ko ni waye ba , Aman very soon zaki sani sanan mamaki yanzu ma na fara Baki bakiga komai bama gold digger kawai , sakin Baki nayi Ina kallonsa , nama rasa bakin magana , haka na lalaba na shige daki Ina kuka mai cin rai , wayata na laluba nakira rahma, rahama na shiga uku wlh Ina cikin damuwa , ban rufe bakin a ba naji a banko kofar dakin da nakeyi, wata mata ce ta shigo da wasu maza a bayanta yussuf ya biyosu Yana magana haba hajiya jamila dan Allah kuyi hkuri iyalina ce da ciki , mene haka , kallonsu nayi na kalli yussuf daya karasa shigowa dakin , matar danaji an Kira da Hajiya Jamila ce ta fara magana ke yarinya ki hada naki da naki kizo ki bar gidan nan , kallonta nayi sanan nace kin isa tayaya zaki shigo mun gida har bedroom kice na bar gida , wacece ke , dariyar takaici tayi sanan ta nuna kanta ni Kike tambaya wace ni , sanan ta kalli yussuf Kai kuma zaka fadamata wace ni ko ni na fada mata , kallonta yayi sanan ya kalleni kinga zaitun zo mu bar gidan , kallonsa nayi sanan na kalli hajiyar nace wlh ni bzan bar gidan nan ba , ke wace ke ki fdamun , kallona tayi sanan tace kinga yarinya ni matar mijinki ce , duk dukiyar da kike takama dashi nawa ne na baku minti 20 ku hada komai naku ku bar mun gida kaikuma ta nuna yussuf idan na Kara ganin mai kama dakai wlh saina saka a kashe mun Kai kuma na kashe banza sanan aure Dani dakai ya kare , ka tataro mun komai nawa kabani, ta kalleni sama da kasa ta fice wanan mazan suka bita a baya .

BURINA(HAUSA NOVEL)Where stories live. Discover now