Part 25

77 0 0
                                    

📗BURINA📗📚written by Khadija Mustapha

Page 25

Da dare sai ga su rahama , sunyi kyau kana ganin su kaga waenda suke cikin Jin dadi , take wani tunani yazo mun da tuni nice da usman , Aman na biyewa son zuciya . Da gudu rahma ta rungume ni Tana kuka zaitun kece kika dawo haka , hawaye ne ya fara zuba a idona tabbas na musgunawa usman da rahama yanzu duk kunyar su nake ji bare usman , cikin kuka na ke magana dan Allah usman ka yafe mun na San na cutar dakai Baka cancanci haka ba Aman na rufe idona nayi treating Dinka with so much disrespect , murmushi yayi yace ba komai ya wuce gashi Allah ya musanya mun da alkahiri ya nuna rahama, tabbas na cancanci usman ya fadamun magana kadan ma ya mun a gani na , haka dai aka cigaba  da jajanta maganar sanan daga bisani suyi mana salama su tafi .

Nan fa unguwar mu ya dauka na dawo na rame na yi baki , wasu suce dan yankan Kai na aura wasu suce ae siyarda ni yayi nikuma na gudo, labari dai kala kala, haka na zama abun kwatance yanzu iyaye da ni suke ma ya yan su mata kwatance .
Sosai na chanza na zama shiru shiru , ko magana na daina yi , na samu labarin hafsa itama tayi aure an kaita Abuja , na tausayawa kaina sosai da ban bi son zuciya ba da tuni Nima Ina nan gidan mijina .

A bangaren su usman kuwa tunda nace ma karima na tafi bandaki taji shiru hakan yasa ta bi bayana Aman ko me kama Dani bata gani ba , sosai tayi mamaki dan haka ta koma kan abuncin Tana masifa Tana zagina Wai wlh yau duka xasu mun , tun tana saka rain gani nan har ta fara fidda Rai haka suka tashi Aman shiru ban dawo ba , haka yasa suka nufi gida ko Ina can Aman mama tace nan dawo ba , har magrib yayi aman ba ni ba dalilina hka yasa suka yanke hukunci kawai na gudu , salllamar yussuf suka ji , ae kuwa sukayi shiru suna kaloon sa , kallonsu yayi sanan yace Ina wanan yarinyar har wuyan ta ya rika tamun sata , mama ce cikin Inda Inda tace yussufa ta gudu fa , ware ido yayi sanan yace me kike nufi da ta gudu , nan suka fada masa yadda abunda ya faru , nan fa gumi ya shigo tsatafo masa mama ce ta kalle sa yussufa ya naga ka shiga damuwa ba kace bka sonta ba Toh ae saikaji dadi ta gudu muma mun huta da ciyar da katuwar gardiya, mama na Riga na siyarda zaitun kallonsa sukayi cikin rashin fahimta me kake nufi daman kaine ka dauke ta ko me, Aa ba hka nake nufi ba ya ce kinga Kinsan nace mki sai zautun ta biyani kudin Dana kashe mata , Toh shine nake ta neman hanyar da hakan Zai faru akan yasa na hadu da wani Yana safarar yan mata nan mukayi ciniki ya siyi zaitun naira milion 10 , kuma ni na kashe kudi dan Ina ganin ma baifi 500 ne ya rage ba a cikin kudin yanzu kuma kunce ta bata ya anyi yanzu , mama ce ta saki salati sanan tace yanzu yussuf million 10 ka kashe kai kadai nan ta shiga kuka Wai ko million daya ne ae ya kawo mata ya barsu suna wahala, kallonta yayi sanan yace yanzu mana bki damu da tashin hankalin Dana shiga ba mutanen nan fa ba barina zasuyi ba wlh saina biya su kudinsu ko na kawo musu zaitun ,kuma wlh nasan zaitun ta gudu ta koma gun iayayenta ba abinda zan bata da zai saka ta dawo saboda tasan ko ni waye , wayo ni , mama ce tace Toh wanan kuma kai kasani tunda kacinye kudin nan Kai kadai Saidai ka nemo mafita kai kadai  Tana gama fadar hakan ta yi shigewar ta daki .

Haka ya yanke hukuncin Kawai ya shiga cikin gari har gidan su zaitun din yace a bashi matar sa duk abunda zai faru ya faru sanan a bashi matar sa ya ba mutanen nan dan wlh shi baisan ind zai Nemo musu  kudin su ba ,

Nikuwa yanzu jikina duk yayi sanyi ko fita bana yi sai ta Kama , su Zee sunzo gidan Maryam suka fara Zuwa da su ka ji shiru , Maryam ce ta sanar dasu nan ba gidan mu bane ta nuna musu gidan mu , sosia sunyi mamaki , ranar naji kunyar da bantaba ji ba , haka suka zo suka cimun mutunci Akan karyar danayi musu , Banda bakin magana har suka gama suka ficewarsu bayan sunmun warning da kar na Kara Neman su dan su ba ajina bane ba

Yau muna tsakar gida dukanmu Ana taba hira , Jefi jefi nake saka Baki dan yanzu ba wanan surutun na dawo so silent , sallama akayi da baba , baba ya tashi ya fita , can sai gashi ya dawo ransa a bace , ya kalli mama Wai wanan mahaukacin yaron nan ne yazo , mama cikin rashin fahimta tace wa fa , yussuf baba y fada , daram kirjina ya buga, Wai na bashi matar sa ya tafi da ita , sosai fargaba da tsoro suka dirar mun na kalli baba wlh baba bazan koma ba Dan Allah kuyi hakuri wlh nasha wahala a gurinsa, baba ne yace dakata zaitun kwantar da hankalin ki babu mai sa ki koma kuma saiya Baki takdar ki kinji, gyada Kai nayi nace Toh Yauwa shige cike zan San abun yi , da Toh na amsa na shige dakina, haka nayi ta tunani har bacci ya dauke ni .

Yussuf kuwa ya takura mana kullum sai yazo Yana tashin hankali a kofar gidanmu Wai shi sai na fito na bishi , tun baba na fitowa har ya daina , kullum gidanmu a tashin hankali yake , nan baba ya yanke hukuncin kiran yan sanda , aikuwa suka zo suka tafi da Yusuf , kwanan sa daya a cell aka kira mu dan haka mukaje, Allah sarki baba baitaba Zuwa gun yan sanda Aman sanadina yau shine a police station . A police station din baba ya nemi yussuf din daya sake ni da yaso taurin Kai Aman Dake yanaso ya fito hka ya yarda yamun saki har uku Wanda hakan ya saka ni cikin Farin ciki , sanan aka bamu hkuri kuma aka ce ko kofar gidanmu kar ya Kara bi bare yazo sanan suka salame mu muka koma gida ..

Yussuf kuwa daina Zuwa yayi aman Yana nan Yana shirin sai ya dauke zaitun , gashi wa enda ya siyarwa sun takura masa ko kudin su ko zaitun, sun bashi kwana 7 ya kawo ni ko ya kawo musu kudin su hakan  yasa yau ya ya ke hukuncin dauko ni kuwa ko a Kansa ne kuwa ,

Bayan la asar mama tace naje na karbo mata kankana wajen baba dan yau azumi takeyi gashi bashir baya nan kuma yaron baba dauda ya tafi garin su , na fito Kenan naji an fusgeni an jefani a mota , ihu na soma yi , dauka ta a mota yayi daidai da shigowar su rahama cikin layin namu, rahama ce ta shiga ihu sanan usman yace ta sauka shi zaibi bayan motar kar mu yi nisa , da taso rigima da Saidai ya tafi da ita Aman ta fasa , shiga gida tayi ta sanar da mama abunda ya faru cikin kuka , shikuwa usman yabi motar da gudu kmar zai tashi sama , yan sanda ya Kira sanan ya cugaba da bin motar , shikuwa yussuf bai San da Ana binsa ba , kawai tuki yake ya kalle ni , ke kika ganin zaki gudu Baki biyani kudina ba ko Toh tsaya kiji na dade da siyarda ke gobe warhaka kina kasar larabawa na siyarda ke naira million 10 kinga har riba na samu Akan abinda na kashe miki , dariya ya barke dashi irinta marasa imani, addua a nashiga yi dan Allah kadai ne zai ceceni daga hanun azzalalumin nan , munyi tafiya sosai sanan mukazo wani gida da shi kadaine gida a wajen duk wajen jeji ne, ya dauko wayarsa ya Kira wani Yana cemsa ga alkawarin su nan yakawo Yana kofar gida

BURINA(HAUSA NOVEL)Where stories live. Discover now