📗📘❤️BURINA 📘📗📗written by Khadija Mustapha
PAGE 14
A kwana a tashi yau watan mu daya da yussuf abubuwa da yawa sun faru a ciki harda bikin
Yesmen da akayi , an kashe kudi sosai kuma yussuf ya bude mun bakin aljihun sa Ina ta sharholiya ta da kudi , duk ankon da aka fito dashi na bikin yesmen babu Wanda banyi ba , makeup kuwa nayi har fuskata ta gaji , yanzu nasan dadin saurayi mai kudi dasu yesmen suke fada , usman kuwa ban Kara bi ta Kansa ba tun bayan rabuwa ta dashiYau ta Kama Saturday kuma yau mukayi waya da yussuf Akan zai dawo gari dan baya nan yaje Abuja wani business a yarda ya fadamun yanada important issue da yakeso zamuyi discussing , sosai na kagu yazo naji wanna wani magana ce
Karfe 8 y kirani Akan Yana kofar gidan mu , na feshe jikina da turare na kalli kaina a mirror Ina murmushi ni kaina nayi ma kaina kyau .
Yana fitowa naga yayi parking yau ma da wata arniyar mota mai kyaun gaske , daman a sani na da yussuf baya dadewa da mota yau kagansa da wanna gobe da wata , ji nayi kaina ya Kara girma saboda nasan ko ba komai zanja magana gurin yan unguwa.
Shige wa nayi motar , Ina zama muka saukar wa juna murmushi, gaisawa mukayi sanan muka dan taba hirar mu, kasa hakuri nayi nace Yauwa honey mganar da kace zamuyi kuma kayi shiru , murmushi yayi sanan yace uhn guess what na yi dum just tell me please karka ce nayi guessing , dariya yayi sanan yace Toh Inaso na turo gidanku but don't say yes yanzu kije kiyi tunani and tell me , zanyi magana yace Aa just go and think about it , nafison idan mutum zai yanke hukunci ya yi tunani sosai akai it's very necessary, gyada Kai nayi sanan na ce honey Wai ka yi tafiya Aman ka kasa kawo mun tsaraba, yar dariya yayi sanan yace haba baby ke Kinsan bazan iya Zuwa har wani gari ba bankawo miki tsaraba ba , y juya y dauko wani paper bag a bayan mota ya mikomun gashi aje ayita ado , sosai naji dadi don abaya ne guda 3 a ciki masu matukar tsada da takalmi sai jaka , godiya nayi masa, Aa yace ba wanan godiyar nakeso ba ya kai hanunsa zai shafa fuska ta , da sauri na kauce cikin baccin rai na kalle shi menene haka Wai yussuf , sorry babe bansan meyake damu na ba , hade rai na sake yi karka karamun hka banso , shiru yayi sanan yace fine shima ya hada rai kamar shi nayi ma laifin , zan tafi yace Yana kallona fuskar sa a daure , Nima da Raina ya gama baci saboda abinda yayimun nace Toh sai anjima ban jira amsar sa ba na bude murfin motar na fice abuna, y dan jima Yana tunani da ni kaina mai rubutun bansan name ba yayi kwafa sanan yayi murmushi y tada motar ya bar unguwar.
Ina isa gida a katifa na kwanta Ina tunanin abunda yafaru, danme yussuf Zai nemi ya tabani abinda bai taba mun ba , ko dai ba da aure yake Sona , Toh idan hakane meyasa zaimun magnar aure inji wata zuciyar tayi saurin kawo mun nata hujjar, ajiyar zuciya na saukar sanan na rufe idona a haka bacci yayi gaba Dani
Yau 2 days da faruwar abun ,kuma daga ranar yussuf bai kuma kirana ba , Nima kuma ban Kira ba Aman na shiga damuwa mai yawan gaske , yau dai na yanke hukuncin Kiran yussuf ko hakuri ne na bashi .
Text na shirya masa na ban hkuri kmar hka
'' am so sorry Dan Allah idan na bata maka rai kayi hakuri and maganar auren mu duk sanda ka shirya send your parents na Amince once again I am so sorry please forgive and forget''
Nazo saka numbern na tura kasancewar da karamun waya ne naji muryar mama na kirana , typing number nashiga yi da sauri Ashe number din usman na rubuta ba tareda na lura ba nayi sending gamida ajiye wayan na bar dakin dan amsa Kiran mama .
Yana zaune Yana tunanin da ya saba na zaitun , text ya shigo , daukar wayan yayi sabida tunda yayi interview a wani company yake expecting kiransu, shiyasa baya ignoring text idan ya shigo xai duba , sunan zaitun yagani da kamar bazai duba ba Saidai kuma ya bude , sosia yayi mamaki da ganin abunda ke cikin text din , murmushi yayi ya furta Alhamdullilah a filli shi yasan watarn dole zaitun zata chanza ta amince dashi gashi lokacin yazo daman ance mai hakuri maiwadaci gashi Yana zaune zaitun ta dawo gareshi
Mama ya sanarwa da maganar aikawa gidansu zaitun din , tayi farin ciki Aman bataso usman ya auri wace take gara shi ba , Aman ba yarda ta iya tunda shine zaitun ce Farin cikin dan nata kuma yace yaji ya gani, Dan haka fatan alkhairi ta bisu dashi , kawaunsa aka fadama dan haka suka ce washe gari Insha Allahu zasu je gidansu zaitun din a tsayar da magana
Ranar usman kamar zai zuba ruwa a kasa ya sha , zaitun kuwa bama tasan wainar da ake toyawa ba , da taji shiru ba reply daga yussuf yasaka ta yanke hukuncin Kiran sa , Kira daya biyu bai dauka ba sai a na uku ya dauka , Baka ga text Dina ha I said am sorry honey, kmar bayason mgana ya amsa da ni banga wani text ba , hkuri na shiga bashi da yayi hkuri , Saida muka shirya sanan nace masa na amince da magnar ya turo iyayyensa, sosai ya nuna yaji dadi sanan mukayi salama ya sanan Dani da yanzu baya gari Aman idan yadawo iyayensa zasu zo , mukayi sallama.

YOU ARE READING
BURINA(HAUSA NOVEL)
FantasyThis novel is about a young lady zaituna who was came from a poor background and Tries her possible means to fit in just to be with her friends who happens to be rich Sit back and enjoy 🩷