Page 2

216 5 0
                                        

Maryam makociyar mu ce kuma amarya da aka kawo Layin , tun Ana Zuwa jere naga alamun amaryar da za a kawo masu kudine daga irin Kayan gado da aka dinga kawowa, na kudiri Niyan saina yi kawance da ita saboda nasamu ko a cikin abokin angon ne yace Yana sona tun da daga ganin irin ginin gidan nasan yanada mugun kudi .

Ae kuwa Ana kawowa amarya washe gari da rana na cewa mama zan je gidansu kawata hafsa wace itace kawata da muka taso tun muna kanana, mama ta bini da a dawo Lafiya na gaida mamansu hafsan na amsa da Toh

Na jima ina kwankwasa gate din amarya Maryam kafin daga baya naji muryar mai gadin gidan Yana tambaya na waye , na amsa da nice, Yana budewa ko jiransa banyi ba na cusa Kai na fada gidan , ah ah daga jna mai gadin y fada Yana karemun kallo , nace ni makociyarta ce , jinjina Kai yayi sanan yacemun Toh bismillah ga hanyar shiga cikin gidan ya nuna mun wani Dan corridor, Kai na kawia na gyada sanan nafara bi ta Inda y nuna mun ina karewa gidan kallo kmar yar kauye ko dake ae banida maraba da su saboda kaf dangin mu babu mai irin wanan gidan , Kai wasu ma basuda arzikin siyan gidan a haya suke, naja tsaki wlh na tsani talauci (wa'iyazubillah) , banyi wani tafiya sosai ba na ga kofa ina da tabbacin shine ko far shiga parlon , Saida na tsaya na gyara sanan na kwankwasa.

Maryam ce ta bude da murmushin ta , ina kwana amarya na fada ina murmushi, fuska a sake ta amsa ah Lfy lau shigo mana, na shigo Ina karema parlon kallo a hankula, maganar Maryam ne ya kaste mun kallon danake, ah saidai baiwar Allah bangane ki ba tace Tana murmushi, na kalleta itadai ba kyau ne da ita ba , tanada haske ba laifi , tsayima ba wani sosai ba , siririya ce kamar zaka hure ta , na rasa yadda ta samu miji mai kudi haka ta aura, maganar Maryam ne y kaste mun tunanin dana tafi yi , nace bangane ki ba ta kuma maimaitawa, la ae mu makota ne gidan da yke gefe gidan nan shine gidanmu sunana zaitun, la zaitun ni sunana Maryam kinga daman bansan kowa ba nasamu kawa bara na dauko miki Abun sha ta yi wani sashe a bangaren parlour din Wanda nake tunanin kitchen ne, ae Tana fita na kara karewa  falon kaloo inata admiring , Kai gaskiya kudi suna Inda suke ga sanyin ac da yake rasta ko ina a jikina, jna ma ace nice a gidan nan na fada ina dora kafa kan daya, shigowar maryam ne ya kaste mun maganar tawa nayi saurin gyara zamana ina murmushi, Yauwa ga lemo da Dan Abun taunawa ta fada gamida ajiye mun tray a kan table din da yake gabana, drinks ne da su snacks da rabona da shan su ni har na manta, nayi murmushi la amarya ngd na fada Ina murmushi, mun Dan taba hira sanan nace mata ni zan wuce gidan mu, tace na jirata Tana Zuwa nace Toh , stairs din parlour din ta hau nikuma na fara addu ar Allah yasa abun arziki zata bani

Takai Kunsan minti  5 sai gata da wata leda mai kyau ta miko mun gashi ba yawa zaitun nagode sosai saikin kara shigowa Dan Allah kina zuwa kina tayani hira, na gyada Kai a raina nace tab basai kin fada ba ae ni naga waje, a filli kuwa nace Toh amarya Insha Allah sai anjima

Har gate ta rako ni sanan ta koma , nikuma na shiga gidanmu cike da farin ciki da zumudin samun abun duniya sanan uwa uba nacika tumbi na da abincin yan gayu.

Da sallama ta na shiga gidanmu, mama na gani suna tankadan garin tuwo da rahama , mama ce ta amsa sallamar tare da bin ledar hanuna da kallo , a Ina kika samo wanan kuma , murmushi nayi ae da nadawo daga gidansu hafsa shine na shiga gidan wacan amaryar shine fa ta bani wanan Kayan ni banma bude ba , na fada Ina zama a tabarmar da su mama suke zaune, na bude ledan, doguwar riga ce Dubai abaya sai dan kune da agogo sai turare da yan kayan kwaliya, rahma ce ta tabe Baki sanan tace Kai aunty zaituna wanan ae maula ne tayaya zaki karbi duk wanan abun daga Zuwa gidan mata Zuwa na farko ke ba saninta kikayi ba , mama ce tace gskiya ne zaitun akan me zaki shiga mata gida kuma ta Baki wanan uban Kayan ki karba , ae daga ganin ginin gidan kinsan keba ajin matar gidan bace baxa ki iya talaucin ki ba ko zaituna, na hade Rai Kai mama kawai dan na shiga a San Juna shikenan sanan wanan kayan wlh ni ban roke ta ba , raham zata sake magana na mata tsawa yimun shiru idan kika Kara cewa wani abu wlh saina buge mki Baki munafuka kawai, mamace tace aa fa wanan magana babu munafurci ae gskia ya fadi mki Kayan nan sunyi yawa bai kamata ki karba ba , Toh mama nayi kuskure bazan Kara ba na fada Ina maida Kayan cikin Leda , ni zan shige Daki nace Ina mikewa, mama ce ta bini da kallo tana girgiza Kai ba tareda da tace komai ba

Tundaga wanan ranar Maryam amarya ta zama kawata , kusan kullum Ina gidanta sabida mijinta matafiyi ne Yana aiki as chief technology officer kuma ba zaman gari yke ba , haka y bani daman Zuwa gidan, mun shaku sosai da Maryam Wanda ni saboda halinta na kyauta yasaka nake kawance da ita kuma nasan zan amfana da ita , sau da dama idan akayi abinci da na tsana especially mai da yaji gidanta nke Zuwa na cika tumbi na ko gudin gori bana yi, mama tayi fadan harta gaji Aman banaji, rahma kuwa saidai ta bini da ido , babanmu kuwa bai masan wainar da ake toyawa ba saboda tun da safe idan ya fita sai dare tun da sana ar siyarda  Kayan marmari yakeyi kuma kasuwar har dare Tana ci dukda ba wani jarin kirki ne dashi ba

BURINA(HAUSA NOVEL)Where stories live. Discover now