📗📚BURINA 📚📚written by khadija Mustapha
PAGE: 17Event 2 nayi organizing with the help of su yesmen da hafsa , duk da Hafsar bata so hakan ba kawai dai ta yi shiru ne abunta dan tasan ko ta fadama ba sauraronta zanyi ba ,
Ladies party mukayi shirya yi as event din farko sai dinner party dan mama tace ita ba bidi ar da zatayi , yini kawai zatayi , rahma ma Daurin aurene da yini , ai kuwa na yi mata ta tas harda kiranta matar shige, sosai ranta ya sosu da har kwalla Saida tayi ,
Saidai Ana wata ga wata ranar da aka nuna mun furnitures Dina Wai shi akayimun , na kalli mama ko kunya na ce ni banaso nafi karfin akai mun wanan sabida yussuf ya nuna mun gidan alfarma daya Gina bazan Kai masa wanan Kayan ba , sai ya Raina ni , sosai mama taji haushi , rahma ce ta dubeni bayan na gama bayani na , sanan tace Aman wlh zaitun bantaba tabbatar da cewa ke mahaukaciya bace dai yau marar tunani, yanzu mama ce kike fadama haka bayan Kinsan ita mahaifiyar kice , kyaleta inji mama ta fada Rai a bace nagode sosai zaitun , kuma Kaya sai an Kai su bawanda zai chanza miki idan kinga dama ki saka Petur da ashana ki Kona su Tana gama fadin hakan ta shige daki Tana kwalla da takaicin abunda zaitun din tayi . Maimakon naji tausayin ta aka sun haka ne ya faru saima juyowa danayi gun rahma nayi mata wankin babaan bargo sanan nayi shigewata daki Abuna Ina mitar Indai natafi wlh sai nayi shekara basu gani ba tunda dai ni aka tsana a gidan .
Yau saura wata daya bikin mu dan haka anata shirye shirye , yau takama za a kawo Lefen mu nida rahma, tun safe yan uwan mama da baba suka cika gidanmu dan ganin lefe , sai habaici nakeyi ma rahma Akan zanga tsuma yau Ina shewa abuna, friends Dina kuwa da suka zo gidan Maryam amarya na kaisu, ihsan da Zee ne kawai suka zo , yesmeen bata gari sun tafi abuja itada mijinta, snacks da nasaka ayimun dan tarbar da gin yussuf masu kawo lefe na kawo musu , muna ci muna hira , shiru shiru lefe har 4 na yamma kuma nakira numbers din yussuf duk basa shiga , sosai na shiga damuwa , da har 5 yayi shiru ba labari yasa su Zee yimun salama suka tafi Akan zasu dawo ganin lefen some other time , gyada Kai nayi kawai nayi jikina duk yayi sanyi
Bayan sun tafi na shiga gidanmu, lefan rahama kawia na gani yan uwa na budewa , yar yayar baba ce naji Tana mun mgana ah zaituna Wai haryanzu naki shiru ko dai baxa su zo ba , kizo kiga na yar uwarki tunda ke naki har yanzu shiru , yaron yayi kokari, sosai yayi bajinta, Allah ya sanya alkhairi
Kallonsu nayi sanan na kalli kayan , karasa sawa nayi har Inda Kayan suke na shiga kallon Kayan , usman yayi kokari ni kaina i was shocked Dana ga Kayan , akwati 8 duk Shake da Kaya , sainaji nadama , na sakar da murmushin takaici yayi kyau kawai na iya fur tawa sanan na tashi nayi hanyar waje Don Zuwa gidansu hafsa wace batada Lfy Tana fama da malaria
Ko da naje jikin nata da sauki , ta tambyeni ko an kawo lefen ,Kai na girgiza mata alamun Aa , meyasa ta tambaya cike da damuwa , wlh hafsa I don't know , kuma nkira yussuf din wayan sa baya shiga sam , am confused har an kawo na rahma , shiru tayi sanan ta shiga kwantar mun da hankali Akan zasu kawo maybe wani abun ne ya faru .
Sosai nasamu relief dan haka nayi mata salama na Koma gida , ko da na koma har kowa ya waste sai makotan mu dasu shigo ganin Kaya , ko ta kansu ban bi ba nayi shigewata daki

YOU ARE READING
BURINA(HAUSA NOVEL)
FantasíaThis novel is about a young lady zaituna who was came from a poor background and Tries her possible means to fit in just to be with her friends who happens to be rich Sit back and enjoy 🩷