Part 9

134 3 0
                                        

📘📘BURINA 📗📗by Khadijat Mustapha

PAGE 9📗📗

A gidansu Zee akayi fixing za ayi makeup sanan a shirya daga can za a kawo  motoci dan daukar Zuwa gun Inda za ayi kamun.

Da wuri na shirya nayi ma mama sallama na Kama hanyar gidansu zee, ko da naje bedroom dinta ta kaini , ni ce na far sa Zuwa dan hka muka hau hirar mu , Tana bani labarin irin kudin ango y kashe na yin organizing dinner , murmushi nayi sanan nace ae haka akeso Zee , kinga daman auren mai kudi is the goal zai fitar dake kunya sosai ko gun friend dinki ba raini , kwarai kuwa inji Zee ni bantab ji kinyi zancen saurayin ki ba , Dan murmushi nayi sanan nace Inada shi kawai busy man ne a kasar waje yake aikin sa , wow inji Zee kice big boy ne , hope dai ba ya yan daddy bane Kinsan an fi son guys masu kudin kansu bana iyayensu ba , Dan murmushin rashin gaskiya nayi sanan nace nooo kudin sa ne, ni  yadda yake kashe mun kudi har tsoro yake bani nafada jna dan basarwa kamar gaske , hannu ta mikomun muka tafa tace that's the goal girl , kisamu a dinga kashe mki , Kinsan big girls kamar mu dole ne aji damu, we are expensive , hakane nace nan muka cigaba da hirar biki kafin su yesmeen suka karaso saboda mai makeup din Tana hanya itama.

12 na rana aka fara yima Zee makeup , sosai ta fito tayi kyau , nice next saboda na Riga su Zuwa , zata fara mun nace Yauwa mai makeup nawa ne saboda ni duk a ganina ae zan samu na biya har na gobe duk a yau kar na kashe sauran dubu 9 din daya yayi saura a kudin da baba yabani , oh I thought munyi mganar da Zee each bridesmaid zaku biya 25k shine price din home service very cheap ko ta fada Tana dan murmushin ta , iyye nace muryata ta sarke, Allah y soni su yesmen sun sauka kasa danyin lunch kafin a gama mun , kinga nace mata bazai yiwu ayimun na 5k ba wlh bnida saikuma na yi shiru karna tonawa kaina asiri , 5k mai makeup ta maimaita, Aa , nace dan Allah ko jagira saiki mun a 5k din , mamaki sosai mai makeup tayi sboda tasan Zee and tunda Zee can afford to pay kusan makeup din 100 plus ae friends dinta ma can afford 25k , girgiza Kai mai makeup tayi sanan tace Noo bana haka , yanzu Ina zan ga wani 25k na bawa mai makeup , kawai na yanke hukunci na fasa , da dinner din na nemi kudi duk Inda yake nayi na gobe , muryar mai makeup naji Tana magana yanzu y muke ciki , Inda Inda nafara sanan nace ki bari kawai Dan Allah karki fadama Zee munyi wanan maganar nafasa yi sai gobe , Kalona tayi sanan ta ce okay fine , kiramun next person pls , nace Toh

Kasa na sauka sun gama lunch kowa na chat a waya , Yauwa yesmen mai makeup tace next person yaje, Aa y naga ba ayi mki ba , yesmen ta tamabya, hmm Wai ba colour Dina foundation din , kalon juna sukayi haba dai tayaya xa a ce makeup artist kmar wanan batada colour din skin dinki , taho muje suka ce , no kubarta dan Allah tace gobe xata siyo Wai tayi order ne bai karaso ba na fada , nama rasa Inda na Nemo karyar Dana zabga, Yemen tace Toh bara ni naje a faramun time Yana tafiya , Zee Tana can dakin stylist dinta ce tazo ana sa mata outfit din , Kai na gyada na bi bayan yesmeen , muna shiga dakin yesmen tace Yauwa mimi sunan ami makeup din , zaitun tace Wai bkida skin colour dinta why , kaloon yesmen tayi cikin rashin fahimata nikuma cikina y duri ruwa , kaloon mai makeup nayi itama naga ni take kallo nayi mata da alama da dan Allah ta rufamun asiri, bana Jin ta gane Aman adu a ta shine Allah yasa ta rufamun asiri, eh ta  fada a takaice gobe zan taho dashi yau dai kam babu , aji yar zuciya nayi da Jin abunda mimi tace nasamu guri na zauna duk a rikice Aman banso su gane ..

4 daidai aka gama wa su yesmen makeup , kowa y fito da outfit dinsa zai saka , na fito da nawa , sosai munyi kyau mussaman ma ni saboda Allah yamun kyau da skin mai kyau , Dan idan ka kalleni saika ranste ba cikin talauci na taso ba , yesmen ce ta kalleni tace wow zaituna kinganki kuwa , gskia stylist dinan naki ta iya dinki sosai , a zuciyata nace eh b stylist salihu taila ba 😂, a filli kuma ji nayi kaina y Kara girma nace yes babes she is the best , gskia ne inji Zee , danma mimi bata mki magic touches dinta ba da sai kin zama Kamar yar tsana saboda kyau , dariya nayi muka cigaba da da shirya wa

Jaka ta da takalmi na fito dasu , Wanda na aro gurin Maryam designers itama mijinta y kawo mata birthday gift dayayi tafiya London  , ji nayi yesmen da ihsan sun fada wow a tare , wanna ba latest channel bag dinan bane , cikin yanga nace shine saurayina y bani as birthday gift , wow gsjia he must be loaded inji yesmeen , eh he works in an oil company abroad , omg ta kuma fada muka tafa,  sosai wanan ba Karamin Kara mun mastayi yayi ba gun kawayena, hka muka gama shiri munata zancen rich Guys and stuffs .

5 daidai motoci na alfarma suka kuno Kai cikin gidan , wata latest G .wagon muka dane Dani da yesmen , itakuma ihsan tabi mortar amarya

Mun iso gurin events din Wanda ya gaji da haduwa , hall ne kato da yasha decor na ya yan manya , hata mai decor din daga abuja aka kawota, an kashe kudi sosai kamar ba a tausayinsa, nan naji na raina kaina , tunda uwata ta haifeni bantaba Zuwa biki irin wanan ba , na sha bin hafsa bikin yan uwansu masu kudi Aman ban taba ganin irin wanan ba , Ashe kudin ma suna suka tara, sai yau idona ya tabbatar mun da haka .

Biki yayi biki , anci ansha  anyi rawa , a Zuba kudi Aman haryanzu ba Wanda y tayani, haka har aka tashi daga kamun nan banyi saurayi ba abun kuwa yamun ciwo dan a wanan bikin nkeso na hadu saurayi mai kudi dan cika BURINA Aman gashi shiru , a gidan su Zee aka ajiye mu, yesmen ta dauki Motarta ta Sauke ni a gida

Ba kowa a tsakar gida lokacin Dana dawo dan hka na shige daki na cire kayan jikina , na fito na shiga bandaki , alwala na daura sanan na koma daki na tadda sallah, magrib nayi da Isha Sbd lokacin 8 :30 ta ma dan wuce , Ina idarwa na kwanta nayi dailing wayar usman ,

Ringing 2 y dauka , gaisa wa mukayi sanan kowa yayi shiru , zaitun y akayi hope kina lafiya , na amsa da eh Toh usman dan Allah dubu 20 zaka bani bikin kawata akeyi zan bata gudunmawa , nisawa yayi sanan yace hafsa ce zatayi aure bansani ba , Aa ba hafsa bace wata kawata ce muna mutunci sosai wlh coursemate Dina ce , Toh yanzu zaitun dai wlh banida kudin da kika tanbaya yanzu  Aman zan kawo miki dubu 5 gobe da safe Shika dai ne itama dani, kwafa nayi har zanyi masa masifa Akan ne zai bani 5 k saidai wata zuciyar ta gargade ni na karba nayi manage , Toh nagode na fada Aman har zuciyata ni banji dadi ba , mun dan taba hira sanan mukayi salama, wlh na Kagu nayi saurayi mai kudi na rabu da usman dinan .

Hafsa na Kira bayan mun gama wayar nace ta aramun dubu 15 zan bata daga baya , bata tambayeni mai zanyi dashi ba tace zatazo ta kawomun da safe tunda bnida account nayi mata godiya muka dan taba hira sanan mukayi salama na ajiye wayan. Lafiyar gado nabi don Nikam cikina a cike yake dan Saida naci na koshi a gurin kamun.

BURINA(HAUSA NOVEL)Where stories live. Discover now