📗📘BURINA📗 written by Khadija Mustapha
PAGE: 23
A bangaren rahma kuwa tana zaune taji kiran wayarta tashi tayi ta dauko wayan tayi mamaki da ganin kiran zaitun , sosai tayi missing din yar uwarta abunda ya hana ta kiranta shine gudun zaitun ta wulanata ta ko ta fada mata bakar magana shiyasa har yau bata taba kiranta ba Aman ko Yaushe Tana ranta , Tana dauka taji muryar zaitun Tana kuka Tana cewa ta shiga uku ta na cikin damuwa can kuma taji hayaniya kuma tana Jin duk abunda ya faru tundaga zuwan Hajiya Jamila har labarin da yussuf ya sanar da ita na ko shi waye , saikuma taji wayar ta kaste shine lokacin da yussuf ya karbi wayan , sake Kira tayi Aman taji a kashe nan fa sosai hankalin rahma ya tashi , ta shiga cikin damuwa kar yussuf ya cutar da yar uwar ta , kuka ta shiga yi , da sauri ta Kira usman Akan yadawo gida ba lfy , Yana dawowa nace masa ni ya kaini gidan zaitun , ba yadda bai yi ba na fadamasa nace sai mun dawo zan fada masa , haka ya rabu dani muka tafi gidan , muna zuwa saidai mun taki rashin sa a motar su zaitun na tafiya da 10 minutes mukuma muka karasa gidan , a rufe da katon kwado muka tarar da gidan nan da na shiga rera kuka , shikenan usman ya siyarda zaitun shikenan wayoo Allah , cikin rashin fahimta usman yace waye ya siyar da ita , meyake faruwa rahama tell me , nan na fadamsa duk abunda nasani , sosai usman ya jinjina lamarin sanan ya rarasheni da mubar gidan Insha Allah za a ga zaitun din yanzu suje su fara fadama su mama a San abunda za a yi. Haka muka Kama hanyar gida dan sanar da baba da mama
Sosai sun shiga damuwa bayan mun sanar da su duk abunda ya faru , baba ne yace tabbas Inada laifi Nima da ban yi zurfin bincike akansa ba Nima Inada kamasho, mama ce tace Aa baban zaituna kayi iya kokarin ka dukada zaituna bataji kuma abun duniya ya rufe mata ido , gashi yanzu tasa ka mu da ita kanta a cikin mastala, Allah yasa mutuminan ba siyarda ita yayi ba , nan usman ya shiga kwantar wa dasu mama hankali da alkawarin zaiyi iya kokarin sa a ganta, saikuma zai fuskanci hukuma Insha Allah, sosai su baba sukayi masa godiya kuma sunji dadi da samun suruki kamar usman Yama manta da laifin da zaitun tayi masa .
Nikuwa tunda yussuf ya bar gidan Dani muka dau hanyar barin garin kano , can wani kauye kusa da Kano , a daidai wani karamun gida naga ya tsaya , ya kalleni saiki fito malama, na kalleshi da idanuwa na dasuka yi ja nasha kuka har na gode wa Allah , haka na fito kmar na Ruga da gudu Aman Ina baxan iya ba , dan mugun Tsoran yussuf ne y kamani a yau dinan ,
Da salama na shiga gidan Ina binsa a baya , wata mata mai Kama da yussuf din sak na gani Tana tankade garin masara, ga hayakin icce duk ya turnike gidan kamar gidan bokaye, ah Yusufa ne naji na matar ta fada , ko ba a fadamun ba nasan itace mahaifiyar sa , Ina wuni na gaishe ta Ina rabewa, Lfy lau ta amsa tana bina da kallo , yussuf ta kalla ita kuma wanan wacece ta fada Tana nuna ni , um mata ta ce , mata kuma ita hajiyar Tana Ina kuma meyasa haka fadamun ba zakayi aure ba , haba mama naji ya fada dan zanyi aure saina sanar Dake naga ae ni na yaro bane ba , hakane naji tace , hajiya kuma fa ta maimaita, hajiya na sake ta , gwalalo ido tayi sanan tace yanzu sabida wanan yarinyar mai Kama da mayu shine ka saki hajiya , Aman wanna yaro akwai dan iska mahaukaci, kallonta nayi Dana ji ta danganta ni da mayu, sosai Raina ya baci na hango zamana da wanan matar a mastayin uwar miji a gida daya , harna fara tausayin kaina , Aa mama naji yussuf yace zaitun ba mayya bace hajiyar kuma xan samu wace ta fita kudi karki damu , gwara dai ta fada Tana bina da wani mastiyacin kallo , shigo ga dakin ki nan naji muryar yussuf , binshi nayi kmar rakumi da akala har dakin da Kira a mastayin nawa , babu komai a dakin sai wata yagulaliyar katifa , ko ledar daki babu a dakin sai siminti, ga ba Fanka, shigowa nayi hawayen tab a idona , haka na zauna a katifar Inata kyankyanmin katifar, ae ban yi cikaken minti 1 ba abunka da mai ciki naji wani irin tashin zuciya , nan na fice daga dakin da gudu na taho tsakar gidan na fara amai kamar hanjin cikina xai fito , mexan gani haka naji muryar mamansa Tana fada Kai Aman yarinyar nan akwai yar iskar yarinya , kawai daga Zuwa sai kizo da kazanta, haka ta yita zagina , nikuwa ban ce mata komai ba har na ji saukin aman na gyara wajen na wanke bakin a na koma dakin Ina tunanin rayuwa ,
Da dare kuwa yussuf ne ya shigo mun da tuwon masarar da aka dafa , ajiyemun yayi a gefe na sanan yayi ficewar sa ko ka kaina baibi ba , yunwa ce ta saka ni a gaba haka na tashi na bude kwanon tuwon, badan dadi ba naci tuwon nan dan miyar ma daga jinta ta kwana biyu aka bani ita, da kyar naci loma 4 na tsame hannuna Ina hawaye , haka na rufe na fito dan wanke hanuna, wanan Karin su uku ne a tsakar gidan da alamu kanin nsa ne da ya fadamun , wanke hanuna nayi , Sanan na tuna yussuf bai kawo mun ruwa ba Dan haka na karasa Inda suke nace mata mama dan Allah pour water nakeso , kaninsa ne suka kalli juna sanan suka tuntsire da dariya , babar ce tace yanzu ke sabida rashin kunya zaki zo kice mu Baki pour water a Inda kika fito haka aka koya miki, dayar ce tace la ke Baki sani ba ae bata ganin mutuncin iyayenta tayaya zataga na wasu, Toh bara na fadamki yaya ya bamu tarihin ki dan haka kar muke kallon ki kwadayaya kawai , Karamar ce tace kuma yaya yace saboda ke hajiya tace sai ya sake ta yanzu gashi mun daina cin kaza a gidan nan banza mai Kama da mayu kawai , haka suka cimun mutunci uwar na kallo bata ce komai ba , a ranar na sha kuka wato Yusuf fadamsu yayi ko ni wace Kai kaico na ni zaitun , na biye ma kwadayi gashi yanzu na sauka a tashar wahala, a ranar bacci ya kauracewa idona sai can dab da asuba bacci yayi gaba Dani Yusuf kuwa ban Ganshi ba har nayi bacci

YOU ARE READING
BURINA(HAUSA NOVEL)
Viễn tưởngThis novel is about a young lady zaituna who was came from a poor background and Tries her possible means to fit in just to be with her friends who happens to be rich Sit back and enjoy 🩷